Chapter 30
Chapter 30
wa Abba kuka ,shi kuma se yazata ko dan saboda haihuwar ta da ta tsaya ne shiyasa ya tausaya mata ,tare da tambayar ta ta faɗi duk abinda take so shikuma ze mallaka mata. Haka rayuwar gidan ta ci gaba ,wanda a lokacin Mu'aisam har ya kammala bautar kasar sa ,sedai be fara aiki ba ,tukuna Indai Mu'aisam yana gida to zaka sameshi tare da twins kamar ma yafison su a duk yaran gidan ,ga biyayya da soyyaya da yake nunawa Ammi bazaka taɓa cewa ba ita ce ta haife sa ba ,haka yaran suna matukar girma mashi , twins na da wata 5 Allah yayiwa mijin Umma rasuwa ,wannan matuwar kam ta girgizasu matuka ,bayan anyi sakan 7 Abba yanemi Umma ta dawo gidan sa da zama amma se ta ki amin cewa ,daga lokacin ya ɗauki nauyin ta da yaranta shine ci da shansu da karatun su lokacin da za'ayi wa kannen Mu'aisam aure ma duk abinda uba keyiwa yaransa shi yayi musu ,daga waje yayi musu ordern kaya , kasancewar dangin Babansu bawani ƙarfi ne dasu ba. sam Khadija bata jin daɗin halin da mahaifiyar ta keyiwa Ammi ,gashi ita sam ba zama take tare dasu ba ,dan haka ko yaushe indai tana gida to tana sashen Ammi ,shiyasa su Rumaisa suka shaƙu da ita sosai dan tana son su ita kam ,ba kamar Rufaidah da tun tana karama halin uwarta ya bayyana a gareta ba sam bata da kunya ga shegen tsiwar tsiya Mu'aisam ne kawai take shakka a gidan ,shima saboda baya sake mata da ne ,ganin yadda yakeyiwa Rumaisa ,se itama tafara natsuwa idan ta ganshi da sauri zata gaida shi ,tun yana zaginta da me baƙin hali har ya dena bayan Ammi tayi masa faɗa tare da nuna masa ,yadena nuna mata wariya ,dan ko yaki ko yaso dai shiɗin yayanta ne ,daƙƴar yayi yaki da zuciyar sa ,har ya fara shiri da ita se daga baya ya fahimci tana da sauƙin kai kawai matsalar girma kai ne da aka tusa mata shi tun batasan wace ce ita ba Comments and share Real Bazamfaria ce ❤️ *INTELLIGENT* *WRITER'S* *ASSOCIATION* ( *On* *word* *together* ) *MABARACIYA* *Story* *and* *writing* *By* *FIDDAUSI* *SANI* (damsel feedorh) 🅿️:2️⃣3️⃣ "Ammi tunanin me kikeyi haka ,kardai saboda wannan haɗin ne kika shiga damuwa?". Dogon Nunfashi ta ja tana sauke ajiyar zuciya" ko ɗaya Mu'aisam , meyasa zan damu dan Alh yanuna ikon sa akan ka ,karka manta Rufaidah itama yatace ,dan kuwa jinin Alh ce , sedai fin karfin da yanuna ne ya taɓa zuciyata kuma na ta bbata saboda yasan bani ce na haife ka ba shi yasa yayi haka" haba Ammi dan Allah kidena faɗar hakan haihuwa ta ce kawai bakiyi ba ,amma wahalar da kikayi dani na tabbata ko kece kika haifeni iyaka kenan ,akaina menene ba'ayi miki ba a gidan nan kuma duk kika danne ,bantaɓa jin cewar bakece Mahaifiyata ba ,dan kin nuna min soyayyar da baki nunawa waƴanda kika haifa Ammi a lokacin da kika samu Rumaisa nayi tunanin zaki sassauta daga kaunar da kikeyimin amma se ma karuwa yayi ,Ammi kinsan ina sane da lokacin da Hajia saudah tayi makircin ta har ta hana Abba biyamin kudin school ,da kikayi magana lefin ya shafeki har yayi iƙirarin saki akan ki ,ke ce wacce kikaci gaba da ɗaukar dawainiyata da kuɗin ki da kuma ƙarfin ki ,a lokacin na sake tabbatar da kaunarki gareni ,naso nabar gidan nan tun a wancen lokacin dan kuwa har gida natafi amma se Umma tayi min tunin abinda namanta itace ta faɗa min cewar idan har nabar gidan nan to ke nayiwa butulci ba kowa ba ,kuma maƙiyanki zasuji daɗi ,nima na tabbatar da hakan shiyasa na dawo gareki ,Ammi ina zaune a gidan ne saboda ke da ke nayi sabon da banyi shi da wacce ta haifeni ba ,inayi miki so irin na ɗa da uwa ,taya zanjuya wa wacce ta sadaukar da komai nata saboda ni ,Ammi karki manta kece nan kika sakani fara kula Rufaidah ,har nafarajin ta kamar yadda nake jin yayarta Khadijah, wlh ban taɓa jin inayi mata wani so da ban ba kuma bana tunanin zan iya zama da ita a natsayin mata , musamman yanzu da na fahimci cewar ba ita bace zaɓin ki ,shirun da kikaji nayiwa Abba ,kece kika dorani akan hakan kin haneni dayin musu ga manya tun bansan amfanin hakan ba ,yanzu ma naji tsoron namusa masa ne ranki ya ɓaci shiyasa nayi shiru ,dan Allah Ammi karki saka damuwa a ranki ,dan kuwa koda ina son Rufaidah kikace batayi miki ba wlh zan canja ,bare ma bana son ta ,kinsani Ammi ni mutum ne me son ya auri macen da zata darajaki da kuma ni kaina ,kuma matuƙar na aureta hakan baze samu ba ,sam tarbiyyarta beyi min ba Ammi ,naga amfanin auren mace ta gari tun akanki irin yadda kikeyiwa Abba biyaya ,dan haka nima kiyi min addu'a Insha'Allah zaɓin Alkhairi ze zo ,dan Rufaidah ba Alkhairi bace a gareni". Shafa kansa Ammi tayi cikeda alfahari tace " Mu'aisam ko kaɗan banga lefinka ba kuma hakan da kayi ka kyauta ,kuma bawai ina kin ka aureta bane ko ɗaya ,sedai inason nunawa Alh ikona ne akan ka ,kayi haƙuri ka amshi kyautar da yayi maka ,ko mutuwa tana kunyar idon mahaifi Mu'aisam ,taya zakacewa Alh baka son yarshi hakan ma sam be dace ba ,kuma bakasani ba ko akwai alkhairi a tsakanin ku sedai abu ɗaya da zan faɗa maka kar ka tauye kanka ,idan har kasan akwai wacce kake so to kasanar dani nayi maka alƙawarin mallakar ta ,koda rayuka zasu ɓaci ,tashi katafi Allah yayi maka albarka ya tabbatar da alkhairi a tsakanin ku." Amenn Ameen, Ammi nagode sosai amma dan Allah kicire damuwar nan banason kusamu matsala da Abba saboda wannan abun, Mu'aisam naki ne har abada kece me iko dashi ,Abba ma zanyi masa karane saboda ke ,zan ɗan fita wurin Alƙasim amma bazan daɗe ba zan dawo " adawo lafiya ,Allah ya kiyaye min kai" Amin " ya amsa fuskar shi dauke da murmushi. Hajiya Sauda# Suna isa party ɗinsu tayi yarfi da hannun Rufaidah tana aika mata wani mugun kallo , akausashe tace" se kin faɗa min gaskiya ubanki ,kece kika je kika faɗa wa Alh cewar kinason lalataccen yaron ce ko kuwa? jin Muryar da tayi anfani da ita yasaka Rufee fashe wa da kuka dan zata iya cewa tunda take a rayuwar ta Hajia Sauda bata taɓa yi mata tsawa ba bare zagi " ko bakiji me nace ba? tasake katse mata tunani ,cikin rawar murya tace " kiyarda dani Mama ban san komai ba wlh ,tunda kika ce bakison sa na haƙura ban san meyasa Abba ya yanke wannan hukun cin ba" ajiyar zuciya ta sauke se kuma ta sassauta murya tace " Rufaidah a duk duniyar nan babu wacce take sonki fiye dani, nice nasha wahalar haihuwar ki da renon cikin ki ,tunda kika tashi baki taɓa cewa kina son abu banyi miki ba meyasa yanzu ni bazakiyi min wannan Alfarmar ba , Rufaidah da ace auren ki ze yiyu da yaron nan da bari amma taya kike tunanin zan bari ki auri jinin
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34