Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 9

Chapter 9

1,218 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

fitowa kuwa bakuna suka dinga haɗuwa wajen yi mini sannu, ban da jakadiya wacce ta rangaɗa guɗa tamkar ta yi hauka don murna. Yarima ne ɗauke da yaron naɗe cikin jakar tawul ɗin jarirai, amma sai da jakadiya ta tsugunna ta karɓe shi daga hannunsa. Ni kuwa na sha gayuna tamkar ba ni ce na haihu ba. Tun daga ranar kuwa shagali ya tashi, amma kuma Yarima yana liƙe da ni,in ka ga ya fita daga ɗakina,dangin mahaifiyarshi ne ko nawa, shi ma yana yi yana zagayowa. Ana saura ƙwana biyu suna aka kai wa Mai Martaba jariri har gida, domin yi masa huɗuba, wanda taro suke yi na musamman idan za'a huɗubar nan, duk da dama ba ganin farko ba ne ba ga Mai Martaba, domin jakadiya ta kaiwa Sarki jaririn da Mama tun ranar da aka haife shi. Haka kuma Daddyna shi ma an kai masa shi gida. Wani abin mamaki kuma shi ne yaron kamar su ɗaya da Mai Martaba Sarki, ba ni da wani bakin magana sai dai kawai na yi wa Allah godiya, na yarda aka nuna mini ƙauna. Shi kuwa Yarima tamkar yau aka kai ni gidansa, saboda irin yadda yake liƙe mini. Maganar mai taya ni zama kuwa, Yarima sam ya hana mata sakewa, saboda sai ta yi barci, sai kawai na ji shi rungume a jikina,ko da kuwa zan kulle ƙofar barandar bayan ɗakina, sai yasa mukullin ya buɗe. Tun saura ƙwana biyu suna gida ya ɗauki cika, duk da Mai Martaba yasa a buɗewa jama'a gidan baƙi. Daren suna kuwa, abin har tsoro ya ba ni, irin yawan jama'ar da ke ƙwararowa gidanmu, ban da kaya da aka dinga shigowa da su,wai duk nawa ne ni da jaririna. Ba zan iya gane ko ƙarfe nawa na dare ba, amma tabbas na san dare ya soma yi sosai. Cikin ɗan sauri na tashi zaune, ina lalubar gabana inda jaririna ke ƙwance, amma ban ji kowa ba,gudun kada in kunna fitila mutanen da ke ƙwance ɗakina duk su farka, yasa na yi amfani da fitilar wayata, amma ban ga jaririna ba. Na haska gaban Aunty Salwa da take ƙwance kusa da ni, sai ƙaton goyon ɗanta a gabanta. A hankali na miƙe na dinga haska gabanta ina haska gaban baƙin da ke ƙwance a manyan katifu a tsakar ɗakina, duk da ƴaƴan ƙannai da matan yayye da ƴan uwan Mamee, amma duk ba jariri a tare da su. Na bi a hankali na buɗe ƙofar shiga sama, saboda duba su jakadiya da mata biyun da suke taya ni ƙwana da ƴan hidimomi ni da jariri. Duk na haska gabansu babu alamar ƙaramin yaro a tare da su. Sam ni ban ruɗe ba saboda na san da wuya a sace yaron nan, sai dai abin da na yi tunani ko dai suna wata al'adar ne wacce sukeyi da tsakiyar dare. Har na koma na ƙwanta sai na ji na kasa bacci ni kaina, ban san ina son jaririna ba sai yanzu. Na miƙe cikin sanɗa a hankali na buɗe durowar da alkyabbobina ke rataye na sanya ɗaya saman rigar barcin jikina. Ban yi wani motsi da ƙarfi ba har na samu na buɗe barandar ta wacce zata kaini dakin Yarima, domin in sanar masa abin da ke faruwa. Ina buɗe ƙofarshi da makulli ba abin da na ci karo da shi sai ɗan sayon sayon safar jaririna ɗaya. Na sunkuya na ɗauka, sannan na ƙarasa cikin ɗakin. Fitilar wayata dai na yi amfani da ita ina duddubawa, na yi murmushin da ya ratsa har zuciyata, saboda jin daɗi. Na lallaba na isa inda suke ƙwance. Ƙwance yake a rigingine ya ɗora yaron a ƙirjinsa, fararen kayan sanyi ne ya sakawa yaron,zaman da na yi a gefensu wannan yasa na kunna fitilar gefen gadon da suke ƙwance. Ƙyau Yarima ya ƙara yi mini. Na sunkuya na sumbaci goshinsa, tare da shafa gashin kansa. Gani na yi ya buɗe idanuwansa a hankali, "Ka firgita ni fa." Ya yi ƴar miƙar nan ta masu bacci, sannan ya tallabe yaron, ya miƙe zaune tare da sa ɗaya yana murtsikar idanuwansa alamar tashi daga bacci, har da ƴar guntuwar hammarsa. Zolaya ta sa nayi alamar tashi in tafi, sai a lokacin ne ma ya yi magana. "Ina za ki kuma?" "Ɗakina." "Da me ya kawo ki?" "Neman yarona." "Shi kaɗai ya dame ki,ni fa? Ko yanzu ba'a yi da ni?" "Na isa." "Zo nan." Ya nuna kusa da shi da hannu ɗaya. Na iso na zauna. "Dama na ɗauko shi ne saboda ina son yin magana da ke,kin ga da wuya gobe mu samu ganin junanmu da zamu iya tsayawa mu yi magana, saboda jama'a. Dama game da sunan yaron nan ne. Mai martaba ya mayar masa da sunansa, shi ne na ce bari na tambaye ki in ya yi miki,kin san shawara tana da daɗi." "Yarima ba ka gajiya,in ba ya ga zolaya irin wacce ka saba yi mini,ya ma zaayi in buɗe baki in ce bana son sunan da Sarki ya sa. Kai dai ka faɗi maganar da ke damun ka, ba dai wannan ba." "Ita ce mana, sai kuwa maganar zuwa gida wanka, gidan mu fa ake kaiwa, ma'ana wajen Mama za'a kai ki, gidan Sarki, amma za'a tambaye ki ra'ayin ki." Ya kama hannuna ɗaya, "Don Allah ki ce nan za ki zauna,a kawo miki masu kulawa da ke kawai,kin san Allah ko jakadiya kawai sai ta kula da ke, ballantana daga gobe kin gama wankan ganyen, magunguna zaki cigaba da sha." Na yi shiru, tunanin ya za'ayi in ce bana zuwa. Na girgiza kaina. "Ba zan iya ba, kunya nake ji." "Kunyar me, ba gidan mijinki ba ne ba." "Saboda me kai kuma ka ke son in Zauna nan gidan." "Saboda ni." "Ba ka da lafiya ne?" "A'a,in dinga ganin ku." "Ai can ma zaka dinga ganin mu ko?" "Yasmin, Please understand me." Na miƙe tsaye, "bari in tafi kada wani cikinsu ya farka bai gan ni ba, kaga kunya zan ji." Bai ce mini komai ba, ya koma ya ƙwanta. Ni kuwa na juya na nufi ɗakina, amma sai na ji duk jikina ya yi mini nauyi. Da na ƙwanta kuwa har gari ya waye ban yi bacci ba, saboda tunanin maganar Yarima ina son in ga jakadiya in gaya mata, saboda ko tana da dabarar yi, amma jama'a sun yi yawa. "Subhanallahi!" Na faɗa a zuciyata, saboda ganin yanda jama'a suka yi yawa, har sun fi duk taron da aka yi. Cikin gidan kuwa jama'a mata da maza,cin abinci akeyi ban da kayan sha,kai abin ya yi mini yawa, har na zamo ba na iya gane komai. Daɗina ma ɗaya ba yawo ake yi ba, zaune nake a saman kujerar mulkina a falon ƙasa, sai dai kowa ya zo ya kawo tashi gaisuwar,in kuwa na miƙe tsaye, to kaya zan je sakewa. Jariri Jafar Bn Jafar,yana hannun yayar Mamee Ruƙayya a riƙe, sai dai a leƙa a gansa, wanda kuwa yake da buƙatar ganinsa sosai sai dai ya kalli ƙaton hotonsa da ke manne a falona, wanda Mai Martaba ne ya aiko da shi. Ƙarfe huɗu na yamma kuwa duk jama'ar da ke gidan mu ta dawo waje, ana gama sallah kowa

Table of Contents

Chapters

23 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});