Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 2

Chapter 2

1,226 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

girmamawa, Mai Martaba ya sunkuya tare da dafa kansa. Fadawa suka ɗauki roƙon kirarinsu, "Nan Sarki ya amsa." Mai martaba ya ɗago shi, madadin ya sake shi, sai kawai na ga ya rungume shi. Fada ta ɗauki ihun murna har da tafi. Ni kuwa wani irin daɗi ya saukar mini a lokaci ɗaya, saboda Yarima na ɗagowa sai ya nunawa Sarki ni. Ganin haka yasa na isa na yi saurin tsugunnawa a gabansa. Ya dafa kaina nima. Gaba ɗaya fadawa suka ɗauki maganarsu. "Sarki na amsawa, Gimbiyar mata wacce ta isa, gaba sarauta baya mulki,so da ƙauna dole a yi miki shi." Ina tsugunne Sarki ya koma ya zauna, sannan duk faɗar aka zauna har da shi Yarima, ya tsugunna kusa da ni. A nutsuwa Sarki ya fara magana, wanda ƴan jarida da ƴan ɗaukar hoto da na talabijin sun zagaye fadar. "Na godewa Allah da ya kawo ni wannan ranar ta farin ciki, shi ne ranar da Yarima mai ci gaba da mulkin mutanena ya dawo lafiya tare da iyalansa. Allah yasa masu albarka ga auren su. Ya yi tafiya ta hutu tare da iyalansa ta tsayin watanni uku. Allah ya dawo mana da shi lafiya, Allah ya bashi ikon riƙe iyalinsa lafiya da kuma al'ummar garina. Na gode da irin karancin ƙaunar da ku ka nuna mana,ni da iyalina gaba ɗaya, Allah ya saka, ya kuma kawo mana canjin rayuwar jin daɗi a nan gaba. Kuma buƙatar da iyalinshi suka buƙata a takardar da ta iso min daga hannun jakadiyarsu,an gama ta tun wata biyu da suka shige, daga yau kuma iyalinsa na da iko da ƴancin zartar da hukunci a kan kowa,ko da kuwa hukunci a kan abin da suke son yiwa mutanena ne. Yanda suke son tsarin bayin gidansu, da masu kulawa da su ya koma a hannunsu. Na gode ƙwarai da ba ni haɗin kai da ake a game da hukuncin da na yanke,ko na gindaya. Yanzu za su shiga ciki domin ganawa da jami'ar da suka daɗe ba su gani ba." Daga haka Mai Martaba ya yi shiru,ko motsi ban ƙara ganin ya yi ba. Duk da kaina a sunkuye yake, ganin Yarima ya matsa kusa da kujerar mulkin Sarki, ya dafa kansa ya miƙe tsaye,ni ma shi yasa na matsa aka dafa nawa kan, na miƙe na bi mijina da yake tsaye dama yana jirana. Cikin gida kuwa, kamar ranar walimar amare bakwai, saboda mata da suka yi yawa a gidan. Maroƙa mata kuwa, sai yi suke, amma Yarima ɗaga kai kawai ya yi ya kallesu, sai na ga duk sun zube ƙasa suna ƙwasar gaisuwa. Gaskiya al'amarin sarauta da akwai sha'awa, sai kuma yanzu na tabbatarwa kaina cewa ba su ne da kansu suke nuna ƘASAITA ba, musamman Allah ne ya saka musu ita a cikin jininsu. Falon Hajiya Kilishi muka fara shiga,a inda na ga hakan ba ƙaramin daɗi ya yi mata ba. Har ƙasa muka sunkuya muka gaishe ta, cikin daɗi ta amsa, har da kamo ni da tayi ta rungume,wai ga ɗiyarta ta dawo. Cikin zolaya irin ta manya ta fara magana. "Amma dai nan za ta ƙwana, saboda gajiya,ai dole ne ta ɗan samu hutu." Shi dai Yarima sai dai kawai ya yi murmushi, "Baka ce komai ba?" "Hajiya ai yarki ce,ga ta nan." Amma fa ya kasa ɗago kansa. Hakan yasa ni kuma na ƙara zolayarsa. "Dama kuwa Hajiya duk na gaji, ga zaman jirgi,Gara na huta yanzu,ko sati biyu na ɗan yi." Ya ɗago ta gefen ido ya harare Ni, Hajiya tasa dariya. "Daina hararar ta,ku tashi ku je tunda ka yi mini rowar ta." Ya miƙe yana kiran, "Hajiya ba da ke nake ba, da ita nake,. Manya na magana tana saka musu baki." Aka saka ƴar dariya, muka fito. Manyan mata kenan, iyayen gidan Mai Martaba,su Mama. Zaune take kamar yanda muka samu Hajiya Kilishi, cikin sakan ɗaya suka yi gaisuwa duk suka fice ɗaya bayan ɗaya, suna fita ta taso ta rungume ni jikinta. "Your are welcome my daughter." "Nifa mama?" Ya faɗa cikin ƴar shagwaɓar da yake yi mini. Kamar dai yanda na ga ya yi mata farkon zuwana gidan. "Ina ruwana da kai ni kuma, sai ka koma can wajen Hajiya." "Kai shi kenan,kun haɗe mini kai. Ita ma Hajiya cewa ta yi ta samu ƴa." "Sai ka koma wajen Mai Martaba,ƙila shi yana so." "Kai Mama." Muka ɗan yi dariya, sannan na ga ya zauna ƙasa yana gaishe ta. Hakan yasa ita ma ta zauna tare da ni a kusa da ita. Ƴan nasihohi ta yi mana na mu zauna lafiya, kada ta kuskura ta ji wata matsala ta taso a tsakaninmu. Nan ta ce mini idan har na ga tana shirin tasowa na bugawa Hajiya Kilishi waya ko na nemi shawarar jakadiya. Nan take ta ba mu labarin cewa, bayan tafiyarmu an ƴanta bayin gidanmu, amma da sunan za su cigaba da aiki, amma a dinga biyansu albashi. Na gidana kuwa,an ce su nemo miji a yi masu aure, wacce mijinta ya bar ta ta cigaba da zuwa, wacce ya hana ta ta yi zaman auranta,ko yanzu haka ake ciki. Ƴan gidan yari kuwa, Mai Martaba cewa ya yi sai kin dawo za'a sallame su, shi ne zasu bi layi a karanta miki laifin kowa, wanda ki ka ga ya dace ki sallame shi,ki sallame shi, wanda bai dace ba ki san ya zakiyi da shi. Na ji daɗi kuwa ƙwarai da gaske,a inda murnata ta ɗan fito fili. A lokacin dai har Mai Martaba sai da muka ƙara keɓewa da shi na musamman, muka gaishe shi a fadar cikin gida. A lokacin ne ma na samu na yi godiyar abubuwan da ya yi mini, waɗanda na buƙata. A nan shi ma ya yi mana nasihohi irin nasu na manya. Sannan ya ce Yarima ya yi taka tsantsan da rayuwa, saboda Abdulrahman ya zo da baya nan, har ya dinga rabon kuɗi a can gidan namu, ya ce a ɓangaren gidan Ahmad ya zauna. Sai da na ɗan nisa sosai, sannan na tunano wanda Sarki ke nufi, wanda Mama ta bani labari cewa ɗan Sarki ne, amma baya sonsa, baya son ma a ce ƴaƴansa ne, kenan ɗan Hajiya Asabe. Sai bayan da aka idar da sallar la'asar, sannan muka yi sallama da su. Ban tashi gane ina mota ta tsaya ba sai da aka buɗe mana ƙofa,kawai sai na ganni gidanmu. Na yi saurin kallon Yarima, sai na ga ya sha kunu, alamar babu wasa,ya ma yi gaba abinsa. Kafin ya kai ga ƴar matattakalar da ke ƙofar shiga gidanmu sai ga su Mamee sun fito, ita da Dad suna fara'ar murna. Kunya ta yi saurin dirar mini,tare da murnar ganin iyayena da na yi, wata uku har da ƙwanaki da dama ban gansu ba, balle ma Dad ɗin da ba na iya ƙwana uku a da ban ganshi ba,ko tafiya ya yi saboda ni baya daɗewa, ya san har kuka nake yi masa a waya. Yarima na isa na ga ya tsugunna ƙasa yana gaishe su. Shi kuwa Daddy sai naga ya ɗaga shi ya rungume, irin dai gaisuwar nan ta larabawa. Dad cewa yake, "Oh! My Son, welcome back,I am happy to see you." Ni kuwa

Table of Contents

Chapters

23 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});