Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 15

Chapter 15

1,219 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

na ce mu biya asibiti in ga Likita, saboda zazzaɓin da ya rufe ni cikin ƙanƙanin lokaci, wanda ni na san hayaniya ce kawai ta yi mini yawa. Ina zaune a mota da yara da mai rainonsu a baya. Ni kuwa ina mazaunin kusa da direba, ina jiran in ga inda Yarima zai fito, saboda ba zan iya zirga-zirgar cikin asibitin Arewa Clinic ba. Ganin shi ya taho yana washe baki kamar na yi masa albishir ɗin daɗi, duk da na san yau farin ciki yake. Sai da ya iso ya buɗe mota sannan na ga ya ɗaure fuskarshi. Ni dai ban ce komai ba, amma ina mamakin ganinsa hannu biyu da wata ƴar farar takarda a hannunsa. Abin da ya sa ban yi magana ba, tunanin ko biyawa za mu yi ƙyamus a siyi magani, amma har muka wuce duk inda za'a samu magani ban ga ya tsaya ba. Ɗaki na nufa kaina tsaye, saboda yanda nake rawar sanyin zazzaɓi. Ina ƙwance Yarima ya shigo ya zauna kusa da ni. "Tashi ki karɓi takardunki." Gabana kam ya faɗi, amma na yi saurin tashi na karɓa saboda ganewa idanuwana abin da ke ciki. Positive (Pregnancy test) . Na ga an rubuta a jikin takardar. Na yi saurin dafe cikina. "Ciki! Haba." Ya harare ni. "To me kike nufi?" "Haba Yarima ciki fa?" "Kina ko ƙwanto ne?" "Haba gani na yi duka yaushe na haihu?" "Ko kina nufin ciki ɗaya ya yi kaɗan? Da gaskiyar ki,ƙato kamar ni a ce ciki ɗaya na yi. Tsaya ki gani in dage in yi na biyu yanzu." Ya taho da sauri zai hayeni, na yi ɗan hanzarin sauka. ###### [2/25, 21:47] Ummi Tandama😇: *ƘASAITA BOOK 3* *NA* *MARYAM KABIR MASHI* Page 9 "Na tuba wallahi,ɗayan ma ya isa." "A'a da sauran Waziri da yake gadin ƙofa, tsaya dai ki ga,ke kin ɗauka abin da wasa ne." Saboda rashin lafiyar da ke jikina yasa na kasa gudu sosai, har sai da ya kamo ni ya ɗauko ni cak, ya ɗora saman gado. "Yau Celebration (murna) ɗin shiryawa da Mai Martaba zan yi." Yana magana yana tuɓe rigar yana cillarwa. Ga shi saman cinyoyina zaune,ni kuwa sai dariyar kukan shagwaɓa nake yi, ina haɗa shi da Allah. Ya yi saurin sumbatar bakina, ya tsotsa, sannan ya ɗago ni ya tattara gashina da ya baje saman gado, ya riƙe da hannu ɗaya. "Yasmin na gode miki da ki ka taimaka mini da rayuwa mai ƙyau, ingantacciya. Ga shi kina haifa mini ingantattun yara. Na gode Allah da....." Muryar Ammar ce ta nufo ɗakin mu. Da ji da gudu yake yana kiran. "Dady ka yi baƙi masu kayan soja, ga su can a get a tsaye." Cikin gaggawa ya miƙe tsaye yana kokawar mayar da rigarshi jikinsa. Ni kuwa dariyar ƙeta kawai nake daga ƙwance, har Ammar ya shigo, amma riga ta ƙi sanyuwa,dan ma Allah ya taimaka da wandonsa a jikinshi. Ammar na shigowa sai na ji yana cewa. "Tsaya Daddy kada ka sa rigar." Yarima ya yi tsaye da riga a hannu. "Daddy tsugunna ka gani." Yarima ya tsugunna, Ammar ya taɓa damtsan cinyar hannun Yarima. "Wai Daddy ka ajiye chuka,ka fita haka,kai ma sojojin su ji tsoron ka,ka bibbige mana su,nima in na girma zan chuka haka." "Za kayi amma daga yau tsoka ake cewa." Ya dafa wajen ƙirjinsa,in tuɓe riga in ga ina da wannan." "Amma ba yanzu za kayi wannan ba, sai kana cin abinci ka girma,ka zama babba kamar ni." "Mama wai haka?" "Kai fita ka barwa mutane waje. Ba na hana ka shigowa ɗaki ba sallama ba da irin wannan surutun naka. Fita mana." Ya juya tare da cewa, "Ki yi haƙuri Mama." Yana fita na taso na ja kunnan Yarima. "Kai ma ba na hana ka biyewa surutun Ammar ba? Wata rana sai ya baka kunya a gaban jama'a." "Sorry Mamo." Na ƙara shan kunu na juya. Ya yi saurin fizgo ni jikinsa. "Sorry Mamo, ina son in na dawo inga an yi mani fara'a." "To je ka an yi haƙurin, kada a daɗe a zo a bani magani insha." "Pracetamol ne kawai za ki sha. Bari in ɗauko miki." "Ni dai gaskiya mai ƙarfi wanda zai hana komai zama cikina." "Kada ki damu, ba mantawa na yi ba. Kin ga ko Ammar ya ce zan iya faɗa da sojoji,kin ga kuwa ƙyau na ace ciki bibbiyu nake yi." Na ture shi. "Ni dai je ka." Ya yi dariya ya saka riga ya fice. Sai da sha ɗaya na dare ta wuce, sannan ya dawo. Da ganinsa kuwa a gajiye yake. Ya zauna kusa da ni cikin cewa. "Wash!" "Sannu." "Ke dai bari wallahi, na gaji sosai, ta so muje ɗaki,dama dai ni ake jira, bari in ɗan watsa ruwa in ji sanyi." "Abincin fa?" "Zan ci, bari dai in samu kaina tukunna." Bayan ya fito ne yake ba ni labarin cewa wajen su Sarkin ƙarya Abdulrahman ya je, saboda yasa a tuhume shi inda ya kai su Waziri. Da ƙyar ya faɗa, shi ma gani ya yi za'a kashe shi a banza. Kin san inda ya kai su?" Na girgiza kai, tare da matsowa irin na mai ɗokin a gaya masa. "Suna babban gidan yarin Legos,ƙiri-ƙiri Prison." "To ya za'ayi yanzu?" "Sai gobe zamu je mu taho da su. Kai Allah dai ya kusan raba mu da ƙajaga." Haka dai muka dinga tattaunawa har muka ƙwanta. N.T.A Kaduna, gidan talabijin na ƙasa, shi muke kallo. Inda muka ga su Yarima na saukowa daga jirgi da su Waziri a bayanshi, sun kai su talatin, dukkansu kamar za su kife ƙasa saboda rama, ga tsufa,ko kuwa in ce yunwa. Amma kaya ne masu ƙyau a jikinsu, ga shi sun sha aski. Jakadiya kuwa, sai kuka take yi,wai tunanin wahalar da ta sha take yi. **** **** **** ** Wata ɗaya kenan da sati uku da dawowar su Waziri wanda ya yi daidai da yau aka yankewa su Abdulrahman da Yayarsa Hadiza da uwarsu Asabe da sauran muƙarrabansu hukunci a babbar kotu ta jaha, wacce ta yanke masu hukuncin ɗaurin rai da rai, saboda bincike ya nuna Abdulrahman da mabiyansa an kama su da laifin fyaɗe, aikata aikin alfasha da maza, shaye-shaye,kisan kai. Ga shi dama wai sana'ar shi fashi da makami. Hajiya Asabe uwarsu kuwa an kamata da laifin yin zina kafin ta yi aure, da ta yi kuma tana shigo da wani namiji a cikin gida. Tuhumar ƙarshe kuma ta tabbatar cewa su Abdulrahman ba ƴaƴan Sarki ba ne, sakamakon faɗi da tayi da bakinta cewa ƴaƴan faranta ne. Hadiza kuwa zaman kanta take yi yanzu haka, ban da gidanta ne matattarar ƴan duniya, ban da bin bokaye da take yi, wanda ya bayar da tabbacin har maƙabarta an taɓa kama ta tana tono wani sashi na jikin matacce. Wa'iyazubillah. Allah ka cikamu da imanin mu,masu yi Allah ya shirye su. Na faɗa a zuciyata. An yi an gama, sai rigima ta dawo kan Yarima, wanda aka zaɓa a matsayin shi zai hau kujerar sarauta, amma ya ƙiya, ya ce shi da Jos har abada. Wannan al'amari ba ƙaramin tayar da hankalin jama'a ya yi ba. Har ya zama garin Kaduna ƴan garin sun zo, tunda kullum ma samu baƙi

Table of Contents

Chapters

23 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});