Chapter 11
Chapter 11
ne ta aiko da takarda tana son Yarima, shekarunta ba su wuce ashirin da huɗu ba, sai dai ƴar wahala ce ta mayar da ita baya kaɗan. Gaba ɗaya mazan na sallame su,ban da taran nan, kowanne daga cikinsu na bashi jarin dubu ashirin da kekunan hawa. Su kuwa matan keken ɗinki da dubu goma-goma. Mubaraka ce kawai na ce a kai mini ita gidana da sauran tambayoyin da zan yi mata. Mazan nan tara kuma na ce a tsare mini su, sai na yi bincike a kansu. Wata ɗaya na baiwa Mabaraka akan ta fito da miji a yi mata aure,in kuwa ba haka ba duk abin da ya biyo bayan haka, ita ta janyowa kanta. Na kawo dubu biyar na bata ta sayi sabulu kafin ta fito da miji. An yi bukukuwa lafiya, taro kuma ya tashi lafiya, amma inda Allah ya ba ni sa'a har yau ina tare da yarana na gidana, duk mazansu sun bar su, sai dai wasu biyu da aka kawo mini saboda ƙwana. Ammar kuwa ya zama abin ƙauna ga kowa. Yarima kuwa,ni da shi tamkar amarya da sabon angonta. **** **** **** Ƙwanciyar hankali tana neman gagarar mu ni da mijina, da duk wani masoyinmu, sakamakon juya bayan da Sarki ya yi mana,a cikin wata biyu kenan. Dabara, hanyoyin daidaitawa duk mun bi su amma abin ya faskara. Wannan tashin hankali ya hana mini Yarima iya zama gida, kullum yana gidansu neman ko a shirya, amma al'amari sai ma gaba yake yi. Babu wanda idanuwana ke son gani sai Yarima, saboda tun asuba da ya fita bai dawo ba, sai dai ya yo waya cewa Sarki na son ganinshi, gashi har ƙarfe goma na dare ta kusa. Tun ina hira da mutane har na kai ga komawa falon sama ina zaman jigum ɗin isowar Yarima, amma babu tunanin da nake sai na maganganun da jakadiya ta gaya mini. Anya kuwa jakadiya ba nema take ta zura ni hanyar wahala ba? Na tunano yanda ta ce mini,wai in dage da abi...... Shigowar Sa'a ita ta katse mini tunanina,tare da jin kukan Ammar. Tana isowa ta durƙusa ta miƙo min shi. Ban tsaya jiran wani ba'asi ba na raɓa shi a cinyata, domin ba shi abincinsa da ke jikina. Ita kuwa ta yi mini sai da safe ta juya ta koma maƙwancinta. Wasa irin na ɗa da mahaifi, shi Ammar yake son mu yi, shi ne riƙe bakina da yi mini waƙar yarensu ta yara, amma yau na kasa kula da shi. Yaron da Babansa ya sangarta shi da wasanni kala-kala, ballantana da ya fara girma. Hankalina kam ya tashi matuƙa, ganin agogon falon ya nuna sha ɗaya har da minti ashirin, amma ban ga Yarima ya dawo ba, wannan ne ya ba ni damar tashi na nufi sashensa, tallabe da Ammar a saman kafaɗata, yaran da ya yi bacci wajen awa ɗaya kenan. Gabana na ji ya yi wata irin mummunar faɗuwa,jin ƙofar barandar bayan ɗakin Yarima a kulle, na saka nawa mukullin, amma da ɗan makullinsa a jiki. Me Yarima yake nufi? Ba ya son ganina ko kuwa? Har na ji raina ya yi mugun ɓaci hakan yasa na dawo ɗakina na shinfiɗar da Ammar na zauna na rafka tagumi. Zuciyata babu abin da bata saƙa mini ba,amma daga ƙarshe duk na ajiye zugar shaiɗan ɗin da ta yi mini,na miƙe na ɗauki alkyabbata na saka, tare da tallabar Ammar. Shiru gidan namu sakamakon kowa ya yi bacci, sai masu gadi da suke yawo. Ƙofar gidan Yarima a kulle take, amma saboda ina da makullin ƙofar a cikin makullaina yasa na sa na buɗe ta,yau ko ƴar fitilar nan da ake bari ta falo ma babu ita, security light. Cikin ɗan lalubar hanya na iso falon shi na sama, shi ma fitilar wajen a kashe take, na murɗa ƙofar ɗakinsa na shiga. Nan ma fitilar ɗakin a kashe suke, na sa hannu na dinga laluba inda makunnin wutar yake da ƙyar na samu na gano shi. Haske ya gauraye ɗakin, wanda ya yi daidai da haɗa ido da Yarima, mutumin da na gani a ƙwanciyar rigingine, amma gaba ɗaya ƙafafunsa a ƙasa suke,gangar jikinsa ce kawai ke saman gado. Ya dinga kallona,ni kuwa na yi tsaye ina neman iso. Bai yi mini magana ba, amma ya yi mini magana da kansa, alamar in zo in zauna kusa da shi. Wata zuciyar ta ce in juya inyi tafiyata, amma sai na yi tunanin hakan ba mafita ba ce. Na isa na zauna kusa da shi, kamar yadda ya umarce ni. Na juya na kalleshi tare da dafa hannunsa ɗaya. Wannan na lura ba ƙaramin daɗi ya yi masa ba, sakamakon tashin da ya yi zaune, tare da ɗauke Ammar daga cinyata,yaro ɗan wata baƙwai da haihuwa. Ya miƙe tsaye ya kai shi,saman gadonsa ya shinfiɗe shi, sannan ya dawo ya tsugunna gabana, tare da kama hannayena duk biyun. Ganin ya kasa yi mini magana yasa na kama shi ya miƙe tsaye. Cikin nutsuwa na mayar da shi na ƙwantar a saman gado. Abubuwan da na san za su karkato da hankalinsa zuwa gare ni shi na dinga yi masa cikin salo-salo, hankali ƙwance. Yarima cikin sauri jikinsa ya ɗauki rawa, wacce take ba ni tsoro a duk lokacin da ta zo masa, amma yau zuciyata na ji ta yi mini daɗi, saboda na samu hanyar da zan tambaye shi me ke faruwa. Tabbas Yarima ya nuna mini farin cikinsa a fili har na tsayin wajen minti arba'in. Fitilar gefen gado ya kunna, sakamakon duhun da ya gauraye ɗakin a ɗan tsayin mintunan da suka wuce. Ina kallo ya miƙe yasa alkyabbarsa,nima ya ɗago ni ya miƙo mini tawa. ###### [2/22, 15:44] Ummi Tandama😇: *ƘASAITA BOOK 3* *NA* *MARYAM KABIR MASHI* Page 7 Yanda ki ka san kurame muka koma saboda kamo ni ya yi ya durƙusar da ni gabansa, sannan shi ma ya durƙusa, ma'ana dai mun haɗa gwiwoyin ƙafafun mu waje ɗaya,muna fuskantar juna. Ya kama hannuna duk biyun, sannan na gaya sunkuyar da kansa. Ganin ya ɗan ɗauki lokaci bai yi magana ba,yasa na zame hannuna ɗaya na matsa sosai, na tallabi kumatunsa ɗaya, sannan na ce, "Yarima." Cikin sanyi murya. Wannan ya ba shi damar yin magana, "Yasmin." Ya yi shiru. "Yasmin,zaki iya zama da ni ko bani da sarauta? Ko ba ni da komai,ko kowa zaya ƙi ni,ko bani da masu yi miki hidima? Ko ba ni......" Hannu na sa na rufe bakinsa, "Yarima ka daina shakku a kaina,ni kai nake so,ba wani abin ka ba, ba kuma wani naka ba, zan zauna da kai Yarima a duk halin da ka shiga, ballantana na sanar har abada ba zaka taɓa taɓewa ba,tun da tun farko Allah ya nuna maka ƙauna a kan harkokin rayuwarka. Shin wai taƙamaimai me ya janyo wannan rashin jituwar tsakaninka da Mai Martaba ne? Anya ba ƙulli? Mai Martaba na sonka,son da kowa yake son ya ga iyayensa na yi masa." "Yasmin,idan na ce miki ga abin da ya haɗa mu nayi ƙarya. Ni dai an wayi gari ranar wata juma'a mun je Masallacin juma'a na ga Mai Martaba bai damu da ni ba, kamar yadda yake yi mini da. Da aka tashi na je
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23