Chapter 23
Chapter 23
ƴar dabarar dariya ni kuma irin ta mu ta manya. "Jakadiya, nunawa ya yi ni yanzu an gama da ni. Ni kuwa na nuna masa ni kuma yanzu nake yayin kaina, shi ne ya ji haushi.” Ya ɗago hannu zai ɗan kai mini duka, na goce. Aka sa dariya, shi ma sai na ga ya yi dariya. "Jakadiya haɗe mini kai ku ka yi da Gimbiyar taki. Zan rama, sai na yi maku bazata.” Muka yi dariya, sannan ya juya. "Sai da safen ku, ga angon ki nan na kawo muku har da ribar ɗa." "Wallahi." Ya faɗa. Ni kuwa na juya. Bai shigo ba sai da har na ƙwanta. Yana shigowa ya wuce gadon Nasir ya ƙwantar da shi, sannan ya zo ya zauna gefen gado. "Yasmin." "Ina jin ka.” "Taso nan." Na mirgino na sauka na tsugunna gabansa. "Matso." Na matsa. "Ɗago." Na ɗago. Yanda yake tamkar an yi durƙushen raƙumi, kunnena ya kama har da, ƴar ƙara na yi masa. "Daga yau kada in ƙara jin kin ce ai ba ni ne na gan ki na ce ina son ki ba. Kina jina?" Na ɗaga kaina. "Kada kuma ki ƙara cewa wai kin daina sona,in na ƙara jin haka, duk hukuncin da na yi miki ke ki ka ja. Yanzu ma don ina tausaya miki sati biyu da suka wuce kin sha wahala da yawa, da sai na kai ki ƙara wajen Daddy ya yi mana Shari'a." "Na tuba,saboda Daddy na yanzu ya fi sonka da ni. Kada kasa ya zane ni da bulala." "Honey,an ruɗe an ga amarya." "Dole in ruɗe. Ka yi tunanin yanda ka ke nuna mini so,ƙauna a gaban kowa,yau in wayi gari in ga ana yiwa wata irin shi. Ka san yau da da gaske ne,ƙila in ƙarasa mutuwar da na kusan yi rana....." "Kada ki tayar mini da hankali. Yanzu a bar wannan maganar." Ya ɗago ni ya zaunar da ni a cinyarsa. "Ni yanzu tunanin da nake shi ne me zan yi wa Jakadiya da su Mansura?" Na yi ɗan shiru kaɗan. "Honey akan me?" "Na ɓangaren ƙyauta." "Eh, gaskiya, amma ni na san Jakadiya ba za ta bar gidan nan ba, da zata iya barin shi da sai a bata ƙyautar gida cikin gari ta koma ita da ƴaƴanta da jikokinta." "To tun da kin yi wannan tunanin,to ko mu samu gida mu saya mai ƙyau babba a baiwa ƴaƴanta su tashi daga gidan sarauta a basu jari. Ita kuma a ɗebi bayan gida a yi mata gidanta mai ƙyau a zuba mata komai." "Haka za'ayi Mai Martaba na biyu. Su Mansura kuwa na san har ka gama tunanin yanda za ka yi dasu. Abin da ya rage ni,ni kuma ina son zuwa gidan Yaya Ahmad a can Spain in ɗan huta,ka ga har na gaido kakannina,in gano iyalinshi ma." "Ki bar wa?" "In bar ka, ka san Sarki ba yawo,wa zaka barwa mulkin?" "Ki yi shiru ko in gama ki da Mama." "Gaskiya ni....” Sai kawai na ga ya ɗauki waya. Na yi saurin alamar ƙwacewa, ya haye gado. Na bi shi sai na ji yana cewa. "Barka da dare Mama.... lafiya ƙalau.... ga ta nan dama ita ce take...” "Barka da dare Mama." "Lafiyar shi lau, ga shi can yana bacci." "A'a dama cewa na yi bari in shigo mu gaisa." "To, to, insha Allah sai anjima.” "Mama,Mama.” na yi saurin rufe bakinsa. "Na tuba na haƙura." "Kin rufawa kanki asiri da yanzu kin sa na koma ƘASAITA ta in dinga ja miki rai.” "Me ka ce?" "Cewa na yi ƘASAITA,a waje ake yin ta ba a gida ba wajen iyali. A gida Honey ita ke da ƘASAITA. Ni kuwa sai in zama shalelenta." Yanzu kuma sai dai in yi miki godiya game da shawarwari da haɗin kai da ki ka ba ni har na zamo na samu ɗaukaka ga jama'a da mahaifina, ga talakawa, yanzu komai ya wadace su ba sai na tsaya jiran gwamna ko shugaban ƙasa ba. Na gode da shawarwarin ki.” "Tsaya ina da magana." Ina jin ki." "Amma na gama haihuwa haka nan?" "Ki ɗan ƙara ɗaya." "Ni dai a'a." Yana dariya wai ganin yanda na yi. Ya rungume ni. "My love,my life,my body,my soul. Na gode Allah da ya ba ni ke." Ya janyo ni muka ƙwanta tare da kashe fitilar ɗakinmu. Addu'ar ƙwanciyar bacci ita ta zamo murfin maganarmu, sai dai muka yi wa junanmu addu'a a zuciya, ta Allah ya taya mu riƙon junanmu. ALHAMDULILLAH! Na gode Mai ƙaunarku a kullum:- AUNTY MARYAM KABIR MASHI.
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23