Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 6

Chapter 6

1,222 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

proud of you." Ma'ana "ina alfahari da ke." Sannan na ji ya miƙe tsaye, ina kallonsa ta tsakankanin ƙofar yatsuna ya fita daga ɗakin. Tsayin mintuna biyu ya yi, sai ga shi ɗauke da ɗan faranti a hannunsa, ya zauna bakin gado tare da ajiye farantin da tree top ya ɗago ni, sai da ya matsa mini na sha, sannan ya ba ni magani ƙwaya ɗaya na sha, na koma na ƙwanta. Ƙwanciyata ta yi daidai da wata ƙara mai ƙarfin gaske kamar ƙarar bindiga. Ban da ihu da muka ji mutane na yi. Ba Yarima da ke zaune ba,ko ni dake ƙwance ina fama da zazzaɓi, sai da na miƙe cikin sauri. Gaba ɗayanmu sai ga mu tsaye jikin taga, ban da ƙura da ta turnuƙe wajen. Bayan kamar mintuna uku, sai muka ga ƙura na washewa a hankali. Ganin wani mutum muka yi a tsaye zagaye da shi, ana ta watsa kuɗi, jama'a na ta tsinta. Yarima ya juyo ya kamani. "Zo ki ƙwanta, bari na sauka ƙasa na dawo." "Ka turo mini jakadiya." Ya amsa da to. Ya yi waje. Cikin mintuna sha biyar sai ga jakadiya a nan nake tambayar ta me ke faruwa? Bayan gaisuwar da ta yi mini,a nan take ba ni labari wai wani ɗan Sarki ne ya zo, tun ba mu daɗe da tafiya ba. Ba yaudarar da ba ya yi a gidan nan, shi ne rabon kuɗi, abinci da sauran kayayyaki, duk wanda aka kaiwa ya ƙi karɓa, to zai faɗa ne. Take gaya mini ko ita an bata magani ta zubawa Yarima a abinci da sauran wurare. "Kin karɓa?" "Eh, saboda in ka ƙi karɓa sai dai a wayi gari ba kai." "Ɗan Sarkin wane gari ne?" "An ce babban Yayan su Yarima ne,wai shi Abdulrahman." Na yi shiru. A nan take na tunano labarin da Mama ta ba ni, ina cikin wannan tunani sai ga Yarima ya shigo da saurin shi. "An kashe mutum uku a wajen can." "Me ye dalilin kashe su?" "Wai saboda sun ƙi ɗibar kuɗin da yake sa wa ana watsawa." "Wa ye shi?" Wai Yayan mu ne." "Meye dalilinsa na yin haka?" "Sarauta yake so." Na yi shiru tare da faɗuwar gaba mai tsanani saboda tunanin kada a kashe mini mijina. Canja alkyabbar jikinsa ya yi, ya ƙara sa turare a jikinsa. "Ina za ka?" "Wa je." Na miƙe da sauri. "A'a kada ka fita ya harbe ka." Ya yi murmushi. "Ai mu ba'a kashe mu ta nan ɓangaren." Ya nuna jakadiya da ɗan yatsa. "Kin ga wacce za ki danƙawa amanar mijinki nan. Sai kuwa masu dafa mini abinci, ta sanadiyyar su ake yi mini komai." Ya iso inda nake tsaye, ya tallafi kumatuna, cikin nutsuwa ya fara magana. Kada ki tayar da hankalinki,ki yi tunanin cewa kina da yaron ciki, zai iya zuɓewa ta kowanne hali,ki ƙwantar da hankalinki." Hawaye suka ƙarasa gangarowa. "Ni dai ban yarda ba." Ya yi murmushi, "Yasmin kada ki karaya mana. Ki tuna gidan sarauta fa ki ke. Haba Honey." Na ƙwantar da kaina a ƙirjinsa, sai kuka sosai. Ya ɗago ni ya ƙura mini ido ba tare da ya yi magana ba. Ɗan tsayin minti ɗaya, sai kawai na ga ya mayar da ni ya rungume ni sosai. Ya ɗago ni da saurinsa ya sumbaci goshina, ya dawo ya tsotsi bakina,bai ce komai ba ya ɗauke ni cak ya ɗora a gado. Ya ja bargo ya lulluɓe ni, ya sunkuyo yana gyara gashin kaina, wanda ya zubo a fuskata,ko in ce wanda ya hautsine saboda ƙwanciya. ####### [2/20, 13:07] Ummi Tandama😇: *ƘASAITA BOOK 3* *NA* *MARYAM KABIR MASHI* Page 4 Ya ƙara sumbatar goshina, kawai ya juya ya tafi. Bin shi na yi da kallo, shi yasa idanuwana suka gane mini ba jakadiya a ɗakin nawa. Yana fita tana shigowa na mayar da kaina na ƙwantar,sai na ji hawaye sun ƙi tsayawa. Jakadiya ta iso ta tsugunna gaban gadona. Allah ya ja da rai,ai ke ce ya kamata a ce kin ƙara ƙarfafa masa gwiwa tare da shawarwari, ke ce mace,kin fi shi tausayi, ke ya kamata a ce kin tsaya kin lura da tambayar me yakamata a yi wa talakawa,shin hukuncin da bai cancanta ba a yi shi?" Na tashi zaune. "To yanzu jakadiya,kina jin ya ce an kashe mutum uku, wacce kuma daraja gare shi,ai kin ga bai dace ba ya fita, sai ya tsaya ya ga ya zata kasance." Ta yi murmushi, "Yana shugaba? Ai shugaba bai ga ta zama ba, ke dai kiyi ƙoƙari ki koyi dabarun taimakawa mijinki da shawarwarin da zai sa jama'arsa ta bi shi, ta kuma ƙara ƙaunarsa." "Kin san su ne ke? Saboda ni kin ga ba ƴar sarauta ba ce ba,haye min tayi da rana tsakiya. Kin ga kuwa ba zan san komai ba game da ita." Jakadiya ta yi murmushi, ta ƙara gyara zama. Tun da ta fara magana nake tallaɓe da kumatuna, saboda al'ajabin abubuwan da take faɗa. Wannan ne yasa a take na ɗauki waya na daddana, domin neman Yarima, saboda fara gudanar da dabarar ta farko cikin dabarun da jakadiya ta koyar da ni. Amma ina! Hayaniya ta yi yawa,ko ƙarar ta ma ba ya ji. Wannan yasa na yi haƙuri sai ya dawo gida, na umarci jakadiya da ta je tasa a sa fanka a kori duk warin turaren da suka saka a gidana. Na bata room Freshner gidan Yarima na ce a sa mini ita. Yariman bai samu shigowa ba sai ƙarfe tara da rabi na dare. Cikin nutsuwa ya zo ya zauna gefen gadon da nake ƙwance, ya sunkuyo ya sumbaci laɓɓana. "Sannu da dawowa." "Ke zan yi wa sannu, ke da na barki ba lafiya, na so shigowa in ga jikinki,amma ina, na so in gaishe ki ko da a waya ne, amma duk hakan ba ta samu ba, sai yanzu ma na ga kiran ki a wayata, missed call,ki yi haƙuri ban ji ba." "Ba komai. Yaya komai dai ya tafi lafiya?" "Eh, to hakan nake tsammani." "Wai me ye ya faru?" "Wani mutum ne ke neman tayar mana da fitina, shi ne na sa aka kama shi har da yaransa, wajen goma, bayan an kama su ne na turawa Mai Martaba Sarki da aiken cewa ga masu son tayar da zaune tsaye an kama. Kafin Mai Martaba ya iso shi ne nasa aka tara jama'a na basu haƙuri da dai bayanan da zai kwantar masu da hankali." Ya koma ya ƙwanta rigingine,saman jikina. "Kin san ko waye mai son haɗa mana rigimar nan?" Na ce "A'a." Cikin sanyin murya. "Wanda na gaya miki ne wai shi Abdulrahman,wai ɗa ne ga Mai Martaba, amma baya son ma a na faɗa, saboda ko a yanzu ma bai bayyana ba,ba kowane ya ji ba. Ni ma waziri ne ke gaya mini." Ya yi ɗan shiru. "Dama ni Mama ta taɓa ba ni labari cewa akwai su,su biyu ne ma har da Yayarsa. Yanzu dai Mai Martaba ya ja masa kunnansa cewa idan ya ƙara jin labarin ya zo garin nan sai yasa an kashe shi." Na shafa gashin kansa, "Ka ƙwantar da hankalinka, ba ka tambaye shi cewa me yake so ba.?" "Sarauta." Na ɗan yi saurin alamun tashi

Table of Contents

Chapters

23 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});