Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 10

Chapter 10

1,213 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

ya nemi wajen zamansa, tamkar dai yanda suke yin kayansu, amma yanzu ya sha bamban da na baya, tunda na baya za ka ga jama'a bayan mu, yanzu kuwa daga ni sai Yarima, sai kuwa dogarawa guda bakwai da ke zagaye da mu. ##### [2/21, 08:11] Ummi Tandama😇: *ƘASAITA BOOK 3* *NA* *MARYAM KABIR MASHI* Page 6 Yaro Jafar Bin Jafar na hannun jakadiyar Sarki, tsaye wajensu Mama da Mamee da Hajiya Kilishi, ban da ragowar mutanen da ke bayan su. Dad ɗina kuwa ga kujerarsa ga ta Sarki. Wasan ƙwallon dawaki aka fara yi (Polo), sai kuwa ɗan hawan Daba, sai wani wasa da shanu ke yi (Hawan Ƙaho), ban da wasanni da raye-raye da yare kala-kala suka yi. Saboda Yarima dai shi ne baya magana, amma ta hannu da ta ƙafa yake yi mini magana, shi ne yatsun hannuna ɗaya na riƙe da nashi yana ta wasa da su, ban da idan na gaji na ƙwace ya koma tsokanar ƙafa. Duk bayan an gama wannan hidimomin ne wanda za mu iya cewa ƙarfe biyar da rabi ta yi, sai na ga wasu irin ƙartin mutane guda biyar sun shigo filin, kowanne ɗaure da bantai a jikinsa, ma'ana ba riga sai wata fata mai ruwan jinin kare ɗaure a ƙugunsu, ga shi iyakacinta cinyarsu.Waziri ne ya miƙe ya fara magana. "Yau ne ranar da Allah ya kawo muka ga jikan Mai Martaba Sarki, rana ce ta farin cikin kowa. Duk wani wanda yake gidan nan ya san sunan yaron shi ne Jafar Bin Jafar, wanda ya gaji sunan Sarki kenan. Yanzu za mu ƙara tabbatar da cewa yaro namu ne, jinin mai girma Yarima ne, duk kuwa wanda ya tashi a gidan nan ya san ƙa'idarmu ce hakan, saboda haka jakadiya Bismillah." Ni dai na sa ido in ga ikon Allah, na san kuwa ba ni kaɗai ba, har danginmu gaba ɗaya, shi ne ƴan uwan Mamee da Daddyna. Jakadiyar Sarki ta sauko daga sama riƙe da jariri a hannunta sanye da kayansa masu ƙyan gaske. Tana shigowa tsakiyar filin nan sai na ga ta miƙawa ɗaya daga cikin ƙartin nan ɗana. Na ɗan yi alamar zan miƙe, Yarima ya riƙe min hannu. Ban ko kalleshi ba, amma na san dai na koma na zauna. Ina kallo aka tuɓe (cirewa) yarona kayansa gaba ɗaya, ya zamo tamkar yanda aka haife shi. Ganin ƙaton nan ya cilla jaririna sama yasa na yi saurin cakume cinyar Yarima da hannuna ɗaya. Sai a lokacin na ji Yarima ya yi magana, sai da ya jefa shi sama sau uku yana cafewa, sannan na ga ya miƙawa tsohon cikinsu. Me zan gani? Gani na yi ya saka mini yarona a cikin ruwan nan da ke cike da uban bahon ƙasar nan,ai ban san lokacin da na miƙe tsaye ba na ce "Yarima kalli ka gani, za'a kashe shi." Da sauri na ga Yarima ya fizgo hannuna ya zaunar da ni. "Yasmin ki ƙwantar da hankalinki, kada ki ba ni kunya. Ni nayi imanin Jafar ɗana ne,ni ne mutumin da ya fara sanin Mamansa,ni na san...." Ai kuwa wannan tsohon mutumin yasa yarona cikin ruwan nan ya barshi ciki bai ɗauko shi ba. Yarima ya matsa hannuna sosai, "Kalle ni." Na juyo na kalleshi. "Me ki ka gani?" "Ba komai." Na juya na kalli inda aka jefa mini yarona. "Ka gani ko,ka gani ko." Jin ya yi shiru ya ƙyale ni yasa na yi saurin kallonsa. Fuskarshi ba wata walwala da ya juyo ya kalleni. Ni kuwa har firgita na yi don tsoro, wannan yasa na yi shiru na zauna sosai, sai kuma hawaye da na ci gaba da zubarwa. Ba wani mai ƙwaƙƙwaran motsi a cikin mutanen da ke wajen nan, wajen ya yi shiru kowa yana kallon ikon Allah, tamkar a ce wani shugaban ƙasa ya iso wajen taron,an tashi za'a yi taken ƙasar su. Abin ka ga uwa, sai na ji na kasa haƙuri, sai da na ƙara kamo hannun Yarima,ko kallona ma bai yi ba, na juya na kalli Dad ɗina,amma ban ga alamar hankalinsa ya tashi ba, kowa na kalla sai in ga hankalinsu ƙwance yake, sai dai alamun su da ya nuna suna jiran ganin abin al'ajabi. Sai da aka ɗauki tsayin mintuna wajen sha biyar, sannan na ga yasa hannu ya ɗauko shi. Yanda aka yi masa da farko, haka ya yi masa yanzu, shi ne cilla shi sama sau uku. Inda na ga kamar hankalin Yarima ya tashi, shi ne a inda aka cilla shi na farko, sai na ga Yariman ya ɗan yi alamar miƙewa tsaye, na biyu sai na ji yasa kuka irin nasu na jarirai, sai na ga Mai Martaba ya miƙe tsaye. Gaba ɗaya mutane suka miƙe tsaye aka dinga ihu da tafi,sai a lokacin na ga Yarima yana dariya, ya juyo ya kalleni, kallon da ni da shi kawai muka san fassarar shi. Hankici ya miƙo mini, ma'anar shi na goge hawayen fuskata, tare da cewa. "Na gode." Cikin sanyin murya. "Wata al'ada sai mu masu ita." A nan na ga jakadiyar mu ta gangara tsakiyar filin nan, jakadiyar Sarki na karɓar yaron sai na ga ta baiwa tamu jakadiyar. Murna kuwa da jakadiyar mu ke yi kamar zata kifa don sauri. Daga nan dai jakadiya ta ɓace mana, sai kuwa Sarki da ya tashi ya yi wa jama'arsa godiya tare da ni kaina da iyayena. Ana haka aka miƙo mini jariri Jafar,wai zan kai wa Sarki shi. Kamar na yi ihu don kunya. Ganin na kasa tafiya yasa Yarima ya karɓa, ina kallo ya miƙawa Mai Martaba, shi kuwa ya ɗan tsaya yana nunawa jama'a shi, sannan na ga ya miƙawa wazirinsa. Jafar ya yi lamo cikin baƙaƙen kayan sanyi, waɗanda aka ɗorawa ƙaramar alkyabba a sama. Waziri ya miƙawa Hajiya Kilishi wacce suke rukunin mata Iyaye. Ina kallo ta baiwa Mamee. Mamee da ƙyar ta karɓa,ni dai na san kunya hana ta karɓa tun farko. Bai fi na mintuna biyu ba ta miƙawa Mama. Mama ce ta kaiwa Daddyna, inda na ga Daddyna ya karɓa yana dariyar farin ciki, irin wannan dai aka ci gaba da yi har lokacin sallar Magriba ya ƙarato, aka rufe taro da addu'a aka tashi. **** **** **** ** Gama arba'in ɗina da ƙwana uku, ya yi daidai da hidimar bukukuwan barorin gidanmu,ƴan mata da samari, wanda su Mansura tun da biki ya matso take kukan rabuwa da ni, duk da an ce wa mazajen su mai so zai iya barin matarsa ta yi aiki, ana biyanta kuɗin aikinta. Bayan ba kuɗin mota za su dinga biya ba, gidaje ne aka gina musu a cikin dajin gidanmu, sai dai na san muna da ɗan nisa da su. Ana gobe kai amarya ne na taka gidan yari tare da ɗana Ammar, wanda yake ɗauke ga kafaɗar Mansura amaryar Isma'il. Gaba ɗaya na sa aka jera su layi, na dinga tambayarsu. Yawanci laifi ɗaya gare su, shi ne rashin kunya, wasu kuma sun tarewa Yarima hanyar fita,babu dai wani taƙamaiman mai laifi, sai mutum tara,su ne aka haɗa baki da su za'a sawa Yarima guba a abinci, Allah ya toni asirinsu. Macen da na samu lokacin da Yarima ya kawo ni gidan yarin, ita kuma laifinta shi

Table of Contents

Chapters

23 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});