Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 3

Chapter 3

1,216 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

ina isowa na faɗa jikin Mamee wacce kai tsaye tana dariyar murna. Ta ɗan riƙe ni tana dariya, daga baya kuma sai da ta taɓa ɗan wasan da ta saba. ###### [2/18, 09:13] Ummi Tandama😇: *ƘASAITA BOOK 3* *NA* *MARYAM KABIR MASHI* Page 2 "Ke tashi daga jikina,ko ƴata ba ta zo ta haye mini jiki ba sai ke." "Kai!" Na faɗa cikin yanayin jin kunya da shagwaɓa." "Ke zo nan ƙyale ta dama ita haka take." Cikin jin kunya, na isa wajen Daddy, Amma sai ga ni na tsugunne a ƙasa, saboda kunya da ta kama ni. Ya sunkuyo ya ɗago ni ya rungume a jikinsa. Ƙamshin turaren sa na ji ya dakar mini hanci. A take na ji kaina ya sara. Cikin sakan ɗaya na ji ina juyawa tamkar wacce ta yi hajijiya ta gaji (Katantanwa), wani amai na ji mai zafin gaske yana taho mini. Tun ina ɗaurewa har na ji gashi nan ya gangaro a bakina. Na zame jikina daga rungumar da Dad ya yi mini,na ruga a guje ga famfon da ake bawa fulawowi ruwa, na tsugunna. Wani irin mugun amai na dinga ƙwaranyawa. Ni dai na ji an riƙe ni, amma ban iya ɗaga kai ba ballantana in ga waye mariƙin nawa. Tun ina yi daga tsugunne,sai ga ni na durƙushe sosai, shi kuwa aman nan ya ƙi tsayawa ko shan iska ma in yi. Na ƙwashe tsayin minti goma ina ƙwaranya amai. Sai ya yi kamar zai tsaya, sai kuma in ji wani sabo ya taso. Muryoyin sannu kuwa,ta ko'ina a kunnuwana, mai dafani kuwa, sai na ji ya tsugunna ya rungume ni a jikinsa. Jin aman ya tsaya, yasa na samu na miƙe na isa na buɗe famfon na kuskure bakina, tare da wanke fuskata, saboda hawayen aman da suka tsattsafo ga idanuwan nawa. Sai da na juyo na ga mutane tsaye a kaina kusan mutum goma sha,ƴan aiki, masu gadi. Mamee ce rungume da ni. Dad kuwa yana tsaye yana kallon ikon Allah, dukkansu suka yi mini sannu. Daga nan Mamee na ɗan riƙe da ni har cikin falon Dad ɗina. Na ɗan kishingiɗa kaɗan a kujera,Dad ke tambayata me ya ke yi mini ciwo? Na ce ba komai, sai dai kaina kawai. Cikin rawar jiki Daddy ya ɗauko magani ya miƙa mini. Mamee ta karɓa. "A'a ba a shan magani ko sai an ga likita. Ka bari in sun tafi can su ga likita, sai ya rubuta musu magani." Nan take na ji Dad ya fara faɗa, "Ya ma za'ayi a ce sai ta ga wani Likita,ai kowa ya san maganin ciwon kai." "Ka zo ciki Alhaji." Ta yi ciki. Na san ɗakin Daddy suka nufa. Nan fa Yarima da ke zaune gefe ɗaya ya yi ɗan ƙaramin zaman makokin cutata, ya samu damar saurin isowa gare ni, ya kama ni ya rungume ni da rawar jikinsa. "Ya ya me ke miki ciwo? Ki gaya mini kin ji Yasmin, talk to me please." "Bana jin komai, sai dai kaina da ya yi mini nauyi kamar yana ciwo." Ya sake ni ya durƙusa a gabana, ya rike hannayena duk biyun, "Please Yasmin, tell me the truth." "Ba komai,ni bana jin komai." "Yasmin look at me." Na ɗago na kalleshi. "Kada ki ɓoye mini Yasmin,ki kalleni ki ga yanda na koma a yanzu kawai. Kina tunanin in ki ka ɓoye mini ya zan koma a nan gaba?" Ya sumbaci hannuwana. Na zame hannu ɗaya na shafi gefen fuskarsa, tare da sunkuyowa na sumbaci laɓɓansa cikin kunya. "Ba zan taɓa yi wa mijina ƙarya ba saboda ina son shi ba zan so in ga hankalinshi ya tashi ba. Ka amince da abin..." Motsin da muka ji yasa ya yi saurin tashi ya koma inda yake zaune. Shi ne kujerar da ke nesa da ni. Dad ne ya shigo, amma sai na ga damuwar fuskarsa ta gushe, wanda take kaɗan ya yin da Mamee ta biyo bayansa. A nan Mamee ta ce mu shiga ciki mu bar su nan. Na miƙe tare da satar kallon Yarima, saboda in karanto me ke fuskarsa. Cikin maganar raɗa ya ce, "Take care." Na lumshe ido alamar na amsa masa na wuce cikin gida. Mamee ta zaunar da ni ta dinga yi mini ƴan tambayoyi kamar su, "Ba komai dai zaman ki da mijinki? Ya ya yanzu kun daidaita ko? Ya gida? Sarautar ba dai matsala?" Duk na amsa mata da eh kawai. Saboda na san ni yanzu ba ni da wata matsala dama matsalata ɗaya ita ce Yarima, yanzu kuwa ni kaina na san ina son Yarima. To ballantana shi wanda na lura da zai iya rasa rayuwarsa idan har ya rasa ni. Sai ƙarfe uku muka bar gidan, amma kafin in tafi tamkar ban taɓa yin komai ba, saboda sai da ma na ci abincin Mamee na ƙoshi. Lafiyata ƙalau muka yi sallama da su. Duk da sai da na nunawa Yarima ya bar ni gida tsayin ƙwana baƙwai,a lokacin muna falon Mamee. Wannan ne ma ya baiwa Yarima damar cije mini laɓɓana da harshensa kada ma na sake faɗar irin wannan mummunar maganar. Na ɗan narke masa tare da cewa. "Gidan mu ne fa! Yanzu shi ne mummunar maganar?" Bai ma ba ni amsa ba, sai dai ya ɗan kama hancina ya ja ya tafi falon Daddy,wato manufarsa baya son maganar ma. Muna shiga mota na ƙwanta daidai lokon motar. "I am tied." Har da ɗan canja yanayin fuskata. Bai fi minti ɗaya ba na ji Yarima na kiran sunana. Na juya na kalleshi, sai na ga ya ware hannuwansa, alamar in isa gare shi. Na ɗan kaɗa idanuwana na gyara ƙwanciyata sosai, alamar dai ba na zuwa. "Honey please come on. Ina son jin ɗumin jikinki a kusa da ni." Na matso na faɗa ƙirjinsa na ƙwanta tamkar ba ni ba, ina jin shi ya sumbaci goshina. "I love You Yasmin,I can't explain how much I love you. Amma ke kina ɓoye mini me ke cikin zuciyarki. Yasmin kin san ba zan iya yin komai ba sai kina kusa da ni. Me yasa za ki takura mini in bar ki gida? Wallahi ba zan iya ba,in ba so ki ke inyi ƙwanan ƙofar gidanku ba, amma na lura ranki ya ɓaci don na hana ki. Yasmin ki yi tunani, ba ki da lafiya fa, ya zan iya ƙwatanta ƙwanan da zan yi a yau in na tuna haka?" Jin maganganun za su yi yawa na san halin Yarima, yanzu zai iya shiga matsananciyar damuwa idan na yi masa shiru. Na ɗago nasa tsinin hancina a daidai bakinsa. "Ka yi haƙuri ba zan ƙara ba. Wallahi nafi son ganin farin cikin ka fiye da nawa. Na fi kowa baƙin ciki idan na ga kana cikin shi. Ka yi mini afuwa,ɓata maka ran da na yi ba zan ƙara maimaitawa ba...." Ya ɗago ni, "kin ci abinci?" Na ɗaga masa kai. "Are You sure?" Na ɗaga kaina. "Ai na yi wa likita waya, har ma na gayawa Mama na ce ta shaidawa Mai Martaba cewa ba ki lafiya za mu koma gobe." "What? Haba Yarima, daga ɗan amai kuma sai ka damu haka." Na sassauta murya, "Ka yi ƙoƙarin ɓoye sona a zuciyarka,fitowa da shi fili

Table of Contents

Chapters

23 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});