Chapter 7
Chapter 7
haɗe da tambayar. "Sarauta ta me?" "Ta Mai Martaba." "To kai fa?" Ya yi murmushi, "kina son sarauta ne? Aƙwai wahala fa." Na ɓata fuska sosai. Ya ƙara yin murmushi, "Yasmin kenan,ki ƙwantar da hankalinki,komai ya wuce, ina nan a matsayina na Yarima mai jiran gado, har da Babyna." Ya faɗa yana lakatar mini hanci. Kunya ta kama ni. Na yi saurin tura kaina filo, shi kuwa ya kama ƴar dariya irin tasu ta sarakuna. Ya turo kansa cikin filon. "Yauwa." Na yi saurin fito da kaina daga ƙarƙashin filon na yi alamar tashi da saurina. Ya yi saurin mayar da ni ya zaunar, tare da riƙe min kunne. "Kin manta ne ki ke tashi da sauri haka?" Ya ɗaga rigata ya sunkuya ya sumbaci fatar cikina, ya ɗago ya tallabi kumatuna tare da ƙura mini ido. "Yasmin! Yasmin!!" Ya girgiza kansa. "Ba zan taɓa iya ƙwatanta yanda nake jin ki ba a raina,son da nake miki yafi ƙarfin duk wani ƙaramin misali." Na rausayar da idanuwana, waɗanda na ji sun aiko da hawaye. Mayar da su ɗin da na yi na runtse ya yi daidai da gangarowar su saman kumatuna,ni kaina ban san dalilin zubowar su ba, sai dai na ji zuciyata ta yi mini sakayau, ba nauyi. Na san ba abin da take so sai Yarima, mutumin da nake jin ya gauraye jinin jikina gaba ɗaya. Hawayena kuwa sun tsiyayo ne ta dalilin wani abu da na ji yana yi mini yawo a tsakiyar kaina. Cikin sakan ɗaya na ga ya ruɗe,ruɗewar da take tayar mini da hankali. Gudun kada ya yi saurin fassara hawayena yasa na koma a hankali na ƙwanta a ƙirjinsa, zuciyata na son gaya masa cewa son da na ke masa yanzu ba zai taɓa misaltuwa ba, amma kunyarsa da nauyinsa sun hana ni sai dai na kurɗa kaina a wuyansa, na ce. "I love You." Cikin sigar raɗa. Ina jin shi ya ƙara matse ni a jikinsa,sam ban yi zaton ya ji ni ba, sai na ji ya ce "I love You too." Kunya ta sa na mayar da idanuwana na lumshe. Bai fi mintuna biyu ba na yi ƴar dabara na ƙwace jikina, saboda na san halin Yarima, sai mu ƙwana a haka. Na yi ɗan hanzari. "Jira ina zuwa, na yi mantuwa." Na sauko daga gadona. Har na yi taku uku ya kira sunana, juyowar da zan yi sai na ji ya ce "I Fancy you." Na yi murmushi na yi gaba. Faranti ne na shigo da shi ɗauke da abinci, har na ajiye farantin ban ga Yarima ya motsa ba, na yi sanɗa na iso inda yake, ya yi kwanciyar nan tasa, tausayin shi ya kama ni. Ganin kafin in je in dawo har ya yi bacci, na sunkuyo na sumbaci goshinsa, ya buɗe idanuwansa a hankali ya yi murmushi. "Na gaji." "I know,sannu ga abinci nan na kawo maka." Na riƙe hannunsa duka biyun. "Ta so ka ci." Ya miƙe tsaye a inda na yi gaggawar taimaka masa ya cire alkyabbar jikinsa. **** **** **** Lallai kam ni na zama ƴar gata gaba da baya, balle da cikin nan na jikina ya tsufa. Sarki, Mama, Hajiya, Daddyna, Mamee duk ba sa son abin da zai taɓa ni, wanda kullum sai Sarki ya aiko waziri ko jakadiyar sa tazo ta ga lafiya ta. Mamee kuwa, sai dai waya. Dad kuwa ya zo gidana ya kai sau uku, ba wai don ya ganni ba,idan ya ga Yarima sai ya koma. Shi kansa Yarima ya kasa gane kan Daddyna, saboda ko an ce ya shiga ba ya shiga, sai dai ya ce gaishe mu ya zo yi. Shalelena kuwa, kullum ana manne da ni,ko fada ma sai na yi da gaske yake sauka, Kaɗan-kadan kuwa ya hayo sama balle in ina ɓangaren gidansa,in kuwa na gidana ne, idanuwana na ga barandar gaba wacce ta koma hanyar zuwa ɗakinsa. Amma wani abu ƙwaya ɗaya da yake damun zuciyata, shi ne yanda gaba ɗaya suka raja'a da cewa namiji zan haifa, ba sa maganar mace ƙwata-kwata , wannan abu na tayar mini da hankali, ballantana idan na ga Yarima ya ɗaga cikin nawa yana sumbatarsa,yana faɗin ɗan shi ya kusa isowa duniya. A take sai na ji hankalina ya tashi, wannan ne ma yasa wasu lokuta na kan yi shiru tamkar na fita daga hankalina na ƴan mintuna. Buɗe ƙofa da na ji yanzu ma ita ta dawo mini da hankalina, na gyara kishingiɗar da na yi a saman kujerar falon samana, na juya na kalli Yarima wanda ya fito daga ƙofar ƙuryar ɗakina,su Mansura suka yi saurin russunawa suka yi gaisuwa, sannan suka miƙe domin sauka ƙasa. Ya iso ya tsugunna gwiwarsa ta hannu a saman cinyoyina, "Honey,na bar ki ko?" Ya ɗan yi tsaki. "Wallahi Mai Martaba ya ƙi yarda, da yanzu muna can, tare da ke kullum." Ya sunkuyo sosai, "My boy,how are you today?" Yasa hannu ya buɗe cikin kamar yanda ya saba, ya sumbace shi ya mayar da kansa ya ƙwantar a jikina. Na sunkuyo na sumbace shi, gashin kaina duk ya rufe mu gaba ɗaya. Na ɗaga kaina sannan na ɗago shi. "Yarima in tambaye ka mana?" "Ƙwarai kuwa." "Me yasa ba ka son a haifar maka mace?" "Me ki ka gani?" "Ban taɓa jin ka ambaci mace ba,ko ba ƙwa son a haifar muku mata?" Na yi shiru kaɗan. "Yanzu in na haifi mace ba zaka zauna da ni ba?" Sai kawai idanuwana suka ciko da hawaye. Ya miƙe tsaye ya zo ya zauna kusa da ni, wanda hakan yasa na saukar da ƙafafuwan ƙasa. Ya kamo hannuna ɗaya ya riƙe da hannayen shi duk biyun ya fara wasa da ƴan yatsun hannuna,a daidai lokacin da ya fara magana. "Yasmin kin san dai mutum ba ya haihuwar wata halitta wacce ba mutum ba ko? Sai dai ya haifo nakasasshe ko marar lafiyar jiki,ko wanda halittarsa ba ta cika ba,ko kuwa ma ya mutu a ciki ko?" Na ɗaga kaina. "To wallahi Yasmin a ce ki haifo wata halitta ta daban,ko ɗaya daga cikin abin da na lissafa, wallahi ni na san ma na so shi na gama,ko da kuwa jama'a za su ƙi ni a kansa, saboda kawai ya fito ta jikinki, ta balle mace mutum. Yasmin ya zan yi naƙi mace, alhalin kin san mu mata rahama ne a gare mu. Ki tuna ke mace ke kika canja mini rayuwata, ta zame mini abin so da ƙauna, abin sha'awa ga kowa. Ke mace ke kika ƙwantar mini da hankalina lokacin da ya tashi, ke mace ke ce kika rungume ni a jikinki a daidai lokacin da na wuce mahaifiyata ta rungume ni a jikinta. Ki tuna ke mace, ke ce wacce za ta haifa mini ƴaƴana,ki tuna ke ce tsanin rayuwata gaba ɗaya,in kin ga dama ki ruguza min rayuwata, wanda duk duniya babu mai baiwa ɗa namiji daɗin rayuwa sai Allah da matarsa tagari,in kin so kuma ki gyara mini ita. Yasmin ki ƙwantar da hankalinki a kaina,ki dinga haifa mini yarana,ko da kuwa duk mata ne, ina so. Wallahi ina so,ni na san dalilin ki,wai sarauta? Ba dole ba ne a ce dama ɗana ya yi sarauta,ko da kuwa duk maza na haifa har
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23