Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 8

Chapter 8

1,217 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

guda ɗari,in Allah ya so sai ya ba ƴaƴan ƙannena,ƙila ma wanda ba'a ɗakinmu ɗaya ba da mahaifinsa. Dakata ma ki ji, wallahi ni yanzun tun da na same ki a matsayin matata, na ji komai na duniya ma ba na son shi sai ke, ke kaɗai nake so. Baki san ma ni cewa nake dama a baiwa Ahmad sarautar nan saboda in zama free man in dinga zama da iyalina a kodayaushe muna hira,muna jin ɗumin junanmu." Ya ɗago ya kalleni, ya juyo sosai. "No! No!! No!!!." Yasa yatsunsa manya biyu yana goge mini hawayen da suka gangaro. "Shi yasa na liƙewa Mai Martaba a kan ya bar ni na tafi da ke London, muyi rainon cikinmu a can, ya ƙiya mini,ba don komai ba sai don in zamo kullum ina kusa da ke, da na samu haka da wannan tunanin bai ma zauna a zuciyarki ba." Ya ɗago fuskata muka haɗa ido, sai na ga ya lumshe ido ya buɗe a hankali, ya kai bakinsa ga nawa. Mintuna biyu ya ɗauka a haka, na yi dabara na cire bakina daga nasa, sanadiyyar wasu alamomi da jikinsa ya nuna mini. Sai da ya ɗauki tsawon wasu ƴan mintuna yana fitar da numfashi a hankali, sannan ya koma ya zauna. Ganin shirun da ya yi yawa. "Yarima ka manta da ka baro jama'a?" Ya ɗago ya kalleni sosai, ya lumshe idanuwansa tare da ɗan mayar da numfashi. "Yanzu zan tafi, ke ce Yasmin,ke ce." Ya miƙe tare da ɗan shafar saman kaina, sannan ya tafi. Ni kaina na san ina samun kulawa ɗari bisa ɗari a wajen Yarima, da jama'arsa gaba ɗaya. Ban da iyayenmu da suke zirga-zirga a kan ganina. Ni kam yanzu na riga na san Allah ya gama haɗa mini komai, sai dai in yi godiya gare shi. ######## [2/20, 18:49] Ummi Tandama😇: *ƘASAITA BOOK 3* *NA* *MARYAM KABIR MASHI* Page 5 Tun kafin a kira sallar Asuba idanuwana suka bushe, sakamakon jin cikina ya naɗe ya tattare waje ɗaya, ya hana mini sakewa. Ina zaune lafiya ƙalau, Yarima ya tashi ganina a zaune yasa na ga ya tashi zaune a firgicen shi yana tambayata ko lafiya? Kafin in bashi amsa ma har ya ɗauki wayar hannunsa ya fara daddana ta. Na yi sauri na ƙwace ta. "Haba Yarima." "Me ke damun ki?" "Ba komai." "Yana gan ki a zaune, kuma sannan ki ce mini ba komai." "Tun da na ce ba komai ka yarda,cikina ne kawai na ji kamar an ƙulle mini shi waje ɗaya." "Na yarda, amma kin san dai daga ni har ke ba wanda ya san wata alama ta haihuwa, saboda haka ki yi mini haƙuri in kirayo Hajiya Kilishi." "Na yarda, amma ka jira na yi sallah tukunna,ka ga yanzu biyar da mintuna ashirin." Da ƙyar ya amince, sannan muka tashi muka yi alwala tare, wanda ya yi mini sallama ya tafi masallaci. Shida da ƙwata na asuba Hajiya Kilishi ta iso gidanmu. Yanda Yarima ke bin ta a baya na yi imani shi ya je ya ɗauko ta har gida. Ya iso ya zauna ɗan nesa daga gefen gado,ni kuwa kallona da shi ƴar harara da take nuna alamun ya yi laifi, bai wani kulani ba na ga ya mayar da hankalinsa ga Hajiya da ke ɗan yi mini ƴan tambayoyi. Dole tasa ni in tashi tsaye, amma tsayuwa ta gagare ni, ni kuwa ba wani ciwon da nake ji,iyakacina dai ƙuguna ya riƙe gam, cikin jikina ya naɗe waje ɗaya. Ganin haka yasa na ji ta ce wa Yarima ya bugawa Doctor Franca waya, wacce ita ce likitan gidan Sarki, sai kuwa Doctor Harisu, mai duba maza,ko wani ciwo amma haihuwa sai Doctor Franca. Cikin mintunan da ba su wuce ashirin ba sai ga Doctor Franca ta iso. Ina jin Hajiya na tayi mata bayani kamar yanda na yi mata. Cikin ƴar hikima irin ta su ta likitoci ta aiki Yarima akan ya ɗebo mata ruwa a ɗan wani abu, yanda na ga sun kalli juna ita da Hajiya shi ya tabbatar mini suna son ya ɗan ba su waje ne. Ai cikina kawai ta dafa ta ce haihuwa ce, sai dai kuma miƙewa tsaye ma ba zan iya ba, ballantana in iya tafiya. Ana cikin haka Yarima ya shigo da wata tasa a hannunsa, ya ciko da ruwa, har bakinta. A nan ne take gaya masa haihuwa ce, amma sai an samo kujerar tura ta zuwa asibiti. A zuciyata na ce yanzu a haka za a kai ni asibiti? Ban ƙarasa tunanina ba sai dai kawai na ga Yarima na shirin ɗauka ta. Kunya kam ta kama ni, amma ganin Hajiya Kilishi ba ta yi masa magana ba, yasa na lumshe idanuwana kawai. Jin an ɗan tsaya da tafiya yasa na buɗe idanuwana. Labulaye kawai na ga an janye, sai da na waiga ma sannan na gane falon sama muke,babu wata alamar ƙofa a wajen da suka buɗe labulan. Hajiya Kilishi kawai na taɓa wani ɗan makunnin kunna fitila, sai kawai na ga ƙofa ta buɗe. Mamaki biyu ya dirar mini a daidai lokacin da muka shiga ɗakin, ban gama mamakin ƙofar ba sai kuma gani na dasa na ɗakin da muka shiga. Ɗaki ne wanda ba su da maraba da na asibiti. Gado biyu ne a ɗakin irin gadajen asibiti, sai daga can gefe ɗaya an saki wani koran labule. Abin ka ga ƙaton ɗaki, ban ƙarasa gani ba naji an ɗora ni saman gado, wata irin kunya ce ta saukar mini a take sanadiyyar sumbatar goshina da Yarima ya yi a gabansu Hajiya. Madadin in ga ya fita, sai na ga ya zauna gefen kaina,ya sa hannu yana gyara mini gashin kaina, da ya baje fuskata,ko in ce ya baje ko'ina. Madadin in ji sun ce ya fita, sai dai na ga an sako wani ɗan koren labule, wanda ya sauka saman cikina, ma'ana ya raba tsakaninmu da su. Ni kuwa ta kwance sun raba ni biyu suke nufi kenan, kaina da gangar jikina ta sama ta wajen Yarima, daga cikina zuwa ƙafafuna suke wajensu. Sam ni ban wani tsorata ba, saboda dama ita ke zuwa yi mini awo duk bayan sati biyu, sannan kusan duk ƙwana uku sai ta zo ganina, ballantana ma da cikina ya tsufa sosai. Shi kuwa ganin an yi haka, sai na ga hankalinsa ya tashi matuƙa, har da wani irin gumi da ke tsiyaya daga saman kansa. Ganin haka yasa na sa hannuna ɗaya na shafo kumatunsa, ya juyo sosai ya kalleni cikin sanyin murya, na ji ya yi mini magana. "Da ciwo ko?" Gaskiya ni bana jin wani ciwo ko ɗaya, saboda haka na girgiza masa kai alamar a'a. Hannunsa ɗaya da ke maƙale da nawa ya ɗago ya sumbata,ni kaɗai nake jin abin da ake yi mini,amma ba ni da damar nunawa, ganin yanda hankalin Yarima ya tashi. Ba afi minti ashirin da kawo ni ɗakin ba na haifi yarona namiji, amma ni kaina na san cikin mintunan na fita daga kamannina, shi kuwa Yarima ya sha cakuma tamkar zan karya shi. Ni kaina ban san duk jama'a sun san ina ɗakin haihuwa ba, sai da na fito. A nan ne na ga falon sama cike da jama'a. Ina

Table of Contents

Chapters

23 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});