Chapter 14
Chapter 14
inji ina sonta." "Amma Allah ya ja da rai kayi kuskure babba, saboda iyayen ka na cikin bala'i, amma sai ka ce ba ruwanka, yanzu haka fa Sarki ya auri matar nan uwarsu shi wanda aka naɗa, sai fa yanda ta yi da shi. Mama kuwa in zata fita sai dai fa ta fita ta ƙofar nan ɓoyayyiya ta je duk inda zata ta dawo." "Ban yarda ba, saboda da Mama ta gaya mini. Kin ga tashi ki tafi. Honey ba ta dubu goma ta sha ruwa a hanya, kada ki ƙara dawowa gidana,kina jina?" "Allah ya ja da...." Ya daka mata tsawa. Nan take na ce, "ya isa. Tashi mu je waje,ki jira ni." Na shiga ɗaki, ita kuma ta tafi waje. Ina fita na ja ta zuwa bayan gida, na tara masu aikinmu na ja masu kunne a kan kada su sake su faɗa cewar akwai baƙuwa a gidan nan . Na ba ta ɗaki na ɗiba mata sabulu, sannan na bayar a sayo mata kayan sawa. Satin jakadiya shida kenan a gidanmu, ta yi ƙyau, ta mayar da jikinta tamkar ba ita ba. Yanzu abin da ya rage ƙoƙarin shawo kan Yarima. Jakadiya ta ce mini babu wata hanyar da zamu bi mushawo kan shi illa mu jira zuwan Mama,idan har muka samu Mama ta gaya masa halin da ake ciki baki da baki,wata ƙila ya amince ya tashi tsaye ya nemawa al'ummar da ke ƙarƙashinsa yanci. Ikon Allah! Yau kuwa safiyar Laraba sai ga Mama ta zo, ganin ta sake lafiya ƙalau kamar yanda take yi mana kenan, ta nuna ba a cikin wata matsala take ba. Dalili ne ma yasa na ɗan tambaye ta ina su Mansura da jakadiya, sai na ji Mama ta ce. "Lafiyar su ƙalau." Kan ganin bata da niyyar cewa komai yasa na aiki ɗaya daga cikin masu aikina na ce a kira mini baƙuwar nan. Shigowar jakadiya za ta yi daidai da ɗaga gwangwanin lemon da Mama ta yi. A madadin ta ci gaba da sha, sai aka samu akasin hakan, saboda firgitar da ta yi. Gaskiya dai ta bayyana daga bakin Mama, wanda Mama har da kukanta take faɗar wasu abubuwan. Hankalin Yarima kam ya tashi. Cikin sakan ɗaya jinin sarautar sa ya gudanyo jikinsa, saboda har wata rawar jiki na ga yana yi. Sai da ya nisa ya kai sau baƙwai, sannan ya miƙe yana cewa. "Zan je sai na kashe su." Mama ta yi saurin riƙe shi tare da zaunar da shi, ta koma ta zauna ita ma. Ya dube ta ya ce, "ina nan zuwa da bindigata, sai na kashe shi." Mama ta yi murmushi, sannan ta yi kirarinsu na manya, shi ne "Ta yaro ƙyau take yi, amma ba ta ƙarko. Ai Yarima duk yanda ka ke tunanin mutanan nan sun riga sun wuce mu. Abin da ya kamata mu yi kawai shi ne mu ma mu dage da roƙon Allah ba dare ba rana. Na farko jakadiya kin fi mu sanin hanyoyin da za'a bi a karyawa Sarki abin da ke jikinsa." Nan take na ji Yarima ya ce, "Aƙwai wasu addu'o'i da ayoyi ina da su na karya sammu ko wani mugun baki. Ban da ayoyin da Manzon Allah (S.A.W) ya ce mana, tare da koyar da mu yanda zamu aikata su." Zan sa a yi saukar Alƙur'ani mai girma,sau sittin da baƙwai, wanda kowanne daga ciki za'a tofa a ruwa a yarfawa wanda ake tunanin an yi masa sammu, ba wata hanya da zamu bi illa wannan. Sannan mu duka mu dinga tashi cikin dare muna gabatar da wannan nafilar, da kuma wacce Allah ya hore mana. In zamu iya kuma mu ma muyi sauka da kanmu. Ga addu'o'in da sallar nafila. Nafila ce raka'a huɗu, kowacce nafila da Ayatul kursiyu ƙafa baƙwai 7, dukkansu bayan ka yi sujjadar ƙarshe sai ka karanta wannan addu'ar. _Wallahu galibun ala amrih,walakin na akasaran nasi la ya'alamun (7),_ Idan mun sallame sai mu karanta wannan addu'ar. _Allahumma wahastu nafsi wa irdilaka_ sau baƙwai(7), sai mu karanta Laƙada ja'akum, ita ma sau baƙwai(7). Manzonmu Annabi Muhammad (S.A.W), ya ce wanda yake karanta waɗannan kalmomi guda goma, Allah zai kare shi daga sharri biyar a duniya,biyar a lahira. Ga su nan kamar haka:--- _1) Hasbunallahu liddini_ _2) Hasbunallahu liman ahamman_ _3) Hasbunallahu liman hasadani_ _4) Hasbunallahu liman kadani bi su'in._ _5) Hasbunallahu indal masala fil ƙabar._ _6) Hasbunallahu indal mizan_ _7) Hasbunallahu indal masala fil ƙabar_ _8) Hasbunallahu la'ila ha'ildalaihi tawakkaltu wahuwa Rabbul Arshir azim._ Allah yasa mu dace. Cikakken bayanin maganin sammu,wato yanda za'a bi a karya sihiri,ko wani mugun Aljani mai taurin kai,ko sanin me mutum ya kamata ya yi,mata ko maza. Ana iya neman littafin nan kantin Al'Ameen Bookshop GUZURIN MATA MUSULMAI IZUWA ƊAKIN AURE. Wanda Malam Bashir Aliyu (Bashir) ya wallafa. Za'a samu duk wani ƙarin bayani a ciki. Cikin wata ɗaya da ƙwana biyu muka gama duk wani tsarin da muke son muyi. Ta hanyar Mama kuma muka samu ta baiwa Mai Martaba maganin da yarfa masa wannan ruwan sauka. Ban da masallatai da Yarima ya dinga bi yana cewa a tayamu roƙon Allah. Ba na mantawa da duk zuwa Makka da zan yi,wato aikin Hajji,ko Umarah, sai na yi roƙon Allah ya daidaita tsakanin Yarima da Mai Martaba. Yau ga shi zan iya cewa Allah ya amsa roƙona,dama kuwa faɗa ce ta malamai, cewa duk muminin ƙwarai ba zai ziyarci ɗakin Allah da buƙatunsa ba face Allah ya biya masa buƙatunsa. Sai dai zasu iya ɗaukar ƴan lokuta, wasu kuma sha yanzu magani yanzu ne. Ko dai ka dawo ka ga alherin abun,ko kuma ma kana can kana dawowa ka samu abin da ka roƙa ya faru. Mu kanmu ba mu san lokacin da Yarima ya je ga hukumar ƙwantar da tarzoma ta ƙasa ba (Mobile) bayan ya samo taimakon gaggawa, sai dai yau muka wayi gari muka ji an kama Sarkin ƙarya Abdulrahman da mahaifiyarsa, da Yayarsa Hadiza da duk mabiyansu. Allahu Akbar! Yau ba wanda bai yi wa Mai Martaba kuka ba, shi da ɗan sa Yarima, wanda suka samu shekara ta biyar ba su ga juna ba. Gaban bainar jama'a Mai Martaba Sarki Jafar ya rungume ɗansa, wanda ya ɗauki sama da mintuna goma, ya ɗagoshi ya kalle shi, sai kuma ya mayar da shi jikinsa ya ƙwantar. Daga baya ne yake tambayar ina jikansa Ammar. Yaro ɗan shekara biyar da wata huɗu ne kawai babu. Amma har ya zama ɗan saurayi saboda girman jiki da yake da shi. Bayan ya ganshi ne aka miƙa masa Suhailat. Abin ka ga rashin sani, ta ƙi zuwa wajen Sarki. Da yake Allah yasa ta yi saurin tafiya da gudunta, ta iso wajena ta riƙe ni gam tana nuna mini Mai Martaba. Hankalin Mai Martaba ya dawo jikinsa sosai, saboda duk ya ruɗe wajen neman su Waziri. To aikin da ya ragewa Yarima kenan, neman dattawan da suka rufa mana asiri da yanzu an hallaka mu. Bayan komai ya lafa ne muka ɗauko hanyar dawowa Kaduna. A hanya ne na ji zazzaɓi ya saukar mini,ga shi ko mun isa gida Yarima ba zama zai yi ba, zai tafi yawon neman su Waziri. Wannan shi ne dalilin da yasa muna isowa Kaduna
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23