Chapter 13
Chapter 13
a baya in kawo maka wannan. Tirela kuwa kayan ku ne,a juye a bamu ita mu koma da ita, ya ce kuma idan kuna buƙatar masu aiki ku gaya mani a kawo muku." Anan ne na ji Mama ta yi magana, "Ka ce an gode, amma masu aiki har na tanadar masu su, har da maigadi ma. Motar ma da na tanadar masu, amma tun da ya riga ni kawowa shi kenan, ta shi za'ayi aiki da ita." Tasa hannu a jaka ta miƙa masa bandir ɗin kuɗi, sannan ta ce su je su sauke kayan. Nasihohi da nuna mana cewa abin da ke faruwa jarabawa ce daga Allah, duk shi Mama ta yi mana, sannan ta yi sallama da mu tare da cewa duk lokacin da ta so ganinmu za ta zo, sannan duk abin da ya shige mana duhu ga waya nan a buga mata. Ban taɓa ganin kukan Yarima na gaskiya ba sai yau. Yau har sai da na ji hankalina ya yi matuƙar tashi. Da ƙyar na samu na lallashe shi, shi Ammar har da kuka, na ba dalili,a nan ne na nemi kukan Yarima na rasa. **** **** **** ** Saboda son junanmu da ƙwanciyar hankali ta ƙaru tsakanina da Yarima, babu inda yake zuwa sai gonar kajinshi da shanu da sauran dabbobi da yake kiwo. Daga can kuma ya isa fadamarsa inda yake noman rani, shi ma sai bayan sallar la'asar yake zuwa, kafin magriba kuwa ya dawo gida kullum. Mu kuwa kamar yara muke ga iyayenmu. Sarki ne kawai har yanzu bai yaye mana abin da ya faru ba. Shekaru huɗu kenan har da watanni biyar. Yanzu haka bai san mun haifi yarinyarmu mace ba, mai sunan Mama, wacce muke kira da Suhailat. Ammar kuwa tuni an sa shi a makaranta. Wani abin mamaki kuma har hutu yake zuwa Jos wajen su Mamee, har kuma ya isa gidan Sarki ya yi ƙwanansa, amma sai dai Mama ta ce ɗan ɗiyar ƙanwarta ne,wato jikanta ne. Mu kam Kaduna ta karɓe mu,bamu cikin wata matsala,sai ƙaruwa da muke yi. Shi ne yanzu ana zuwa har gida ana koya mana karatun litattafan addini ni da Yarima. Ga shi kuma yanzu ya iya neman na kansa, wanda a da sai dai ya ga kuɗi bai san ta yadda ake samun su ba. Yau ma Yarima na ƙwance a doguwar kujera daga shi sai singileti fara da dogon wando,ni kuwa ina ƙwance,wato saman jikinsa,muna ta hirarmu ta yaushe zan je Jos, saboda na samu shekara kenan har da wata biyu ban je ba. Na fahimci Yarima yanzu ba ya son ana yi masa hirar Jos, amma ni a wajena ta zama dole. Bai kai ga bani amsa ba muka ji sallama. Na ɗan yi gaggawar tashi zaune, sannan na ce, "A shigo." Sa'a mai rainon Suhailat ce ta shigo ɗauke da Suhailat yarinyar da ta shekara ɗaya da wata huɗu kenan. Ta durƙusa har ƙasa sannan ta ce, "An yi baƙuwa tana waje. Na tambaye ta sunan ta domin inzo in gaya maku, amma ta ce ace baƙuwa ce daga Jos." Nan take Yarima ya ɓata rai, "Ki ce mata ta koma can Jos ɗin, nan gidan duk ƴan Kaduna ne ba ƴan Jos." "A yi haƙuri Yarima." Ya juyo da saurin gaske, ya kira sunana. "A yi haƙuri kuskure ne,je ki kice ta shigo." Ta tashi ta fita. Kafin ta shigo na yi saurin miƙa masa doguwar rigarsa ta shan iska. Ya karɓa tare da yi mini ƙorafin kada in ƙara kiransa da Yarima, baya so. Na bishi da na daina. Wata fuska na gani, wacce da gani na san fuskar, sai dai ganin ta yi mini tsufa, ta rame,ko ince ma ba tsoka ko ɗaya a jikin fuskar. Dattijuwar da ta shigo, ta zauna ƙasa tana gaishe mu. ###### [2/25, 16:04] Ummi Tandama😇: *ƘASAITA BOOK 3* *NA* *MARYAM KABIR MASHI* Page 8 "Sannu Inna,ban gane ki ba, na so dai in ga kamar na taɓa ganin ki, amma na kasa tunano a ina na taɓa ganin ki." Sai na ji ta saka kuka tana cewa, "Ai dama na san da wuya ki gane ni Gimbiya ni ce jakadiya." Kafin ta ƙarasa daga ni har Yarima mun miƙe tsaye tare da kiran Innalillahi wa'inna ilaihir'raji'un! Kamar haɗa baki muka ƙara cewa, "Jakadiya me ya same ki haka?" "Ai Gimbiya Allah ya yi da ragowar shan ruwana gaba, da tuni da sai dai in kun tunano ni ku ce Allah ya ji ƙaina. Yanzu mu ai mulkin kama karya ake yi mana a Jos, saboda azzalumin Sarkin da aka baiwa sarauta." "Wa aka ba sarautar?" Yarima ya yi tambayar. "Wani ne wai shi Abdulrahman, wai ɗan Sarki ne, shi ne yanzu duk abin da ake yi sama da shekara uku duk baku da labari?" "Ba mu da labari, wajen wa zamu ji?" "Wajen Mama." "In ta zo mu bata gaya mana komai. Ni kuma ko na je Jos ba na zuwa ko'ina sai gidanmu,ni kuwa ban taɓa ji ba,mun san dai ance an yi naɗin sarauta a Jos, amma ba mu san me aka naɗa ba." "Ai abin ba daɗin faɗa,kin gan mu nan jiya muka gudo daga gidan yari. Wahala ta duniya ba wacce ba mu gani ba...." Tasa kuka. "Ke har da fyaɗe an yi mini, tsofai-tsofai da ni. Ke yanzu dai Allah ya yaye mana masifa kawai." "Ina su Mansura." Na tambaya cikin sigar tashin hankali. "Sun gudu su duka waɗanda ki ka sani, maza da mata, saboda kamo su kawai aka dinga yi ana yi masu fyaɗe kullum. Maza kuma a kaiwa shugaban nasu, shi kuma aikinsa kenan amfani da maza. Gimbiya ƙartin mutane ya zo da su sune dogarawansa, sun kai ɗari biyu, ban da ƴan iskan ƴan mata." Ta sake fashewa da kuka. "Dole ne in neme ku in sanar daku yanda ƙasarku ta koma. Ku yi mana arziƙi ku je ku taimakawa al'ummarku." "Ina Mai Martaba yake ne ake yin irin wannan abubuwan kafirci?" Yarima ya tambaya. "Yana nan,ai ya riga ya tsafe shi, sai yanda ya ga damar yi da shi. Waziri da manyan mabiyansa fa an neme su an rasa." "Innalillahi wa'inna ilaihir'raji'un!” muka haɗa baki. "Yanzu su waye kusa da Sarki?" "Wasu ne ya kawo ya zuba masa. Kai bacin su Ahmad fa da ƙila ma an gama da su Mama, to su ke tsaye a kan iyayensu, duk sun ajiye karatunsu, sun zama masu gadin iyayensu." "Yanzu ke ya aka yi kika gane nan gidan?" "Gidan su Gimbiya na je na samu maigadinsu, shi ne ya yi min ƙwatancen nan gidan. Shi ya gaya mini ma kuna nan garin, da duk abin da ya faru a baya, saboda mu bamu sani ba. An dai taɓa jin labarin kuna ƴar takun saƙa da Sarki, har na cewa Gimbiya ta tashi tsaye,sa hannu aka yi maku kai da mahaifinka." "Me ye sa hannu kuma?" "A je mugayen matsafa su shiga tsakanin masoya biyu." "Allah ya kiyaye. Yanzu ki tashi kiyi tafiyarki,ni yanzu hankalina a ƙwance ya ke ni da iyalina, saboda haka ba na fatan abin da zai zo ya dagula mini lissafi. Sarauta kuma Allah ya tayashi riƙonta. Amma ni yanzu ko ma sha'awarta ba ma yi, ballantana
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23