Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 5

Chapter 5

1,215 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

sauri na ga ya fita, sai na ji yana cewa, "Shigo nan ka ganta. Sau uku kenan tana yin shi a yau,kaga har ya zamanto ba komai a cikinta, kalli yanda take?" Likita ya sunkuyo, "Sannu Madam." Na ɗaga kaina kawai." "Me ke saka ki amai?" Na ɗaga masa hannu alamar ya jira, suna tsaye,Yarima na ta safa da marwa a banɗaki. Har tsayin mintuna goma, sannan na ɗago, wanda a take na ji jikina na rawar zazzaɓi. Ban da jiri da nake gani. Yarima ya riƙe ni muka fito ɗaki. Muna fitowa na yi saurin komawa banɗaki. "Yarima bana son warin turaren wutar nan, kaina juyawa yake yi." Nan da nan ya kuma ruɗewa, "Doctor, ya za'ayi?" "Yallaɓai ko a tafi da ita sashenka mu gani." "Haka za'ayi." Da sauri na ga ya buɗe ƙofar, bayan wacce za'a fita barandar baya, wacce ke kallon ta gidan Yarima, sai da ya buɗe, sannan ya kamo ni. Muna fita madadin in ga fili kamar da, sai na ga an gine ta, ta yi wani zagaye kamar ƙaton fayif na ruwa, ga fulawoyi na gaske nannaɗe da jikinsa. Ban iya tsayawa na lura da yanda aka yi ta ba sosai, ni dai na ga muna tafiya har mun ɓulla ƙofar barandar Yarima. A take na ga ya buɗe mun shiga, sai na ga ɗakin Yarima. Yana isa ya ƙwantar da ni a gadon shi, ya janyo bargo ya lulluɓa mini,sannan ya koma ga kaina ya zauna, inda likita ya matso ya tsugunna gabana. "Madam kamar me ki ke ji yana yi miki ciwo.?" "Zazzaɓi, ciwon kai, sai amai." "Mara fa,ko ciki?" "A'a." "Yanzu za ki iya tuna ko ƙwana nawa rabon ki da al'ada?" "Likita bana son irin waɗannan tambayoyin fa." In ji Yarima. "To Yallaɓai an bar su, sai dai ina son fitsarinta, yanzu zan je in dawo. Awa ɗaya za ka bani." "To ya za'ayi a ɗebi fitsarinta,in ba ya ga rashin hankali irin naka?" "Allah ya ja da rai,ga ƴar ƙwalbar da za ta yi a ciki ta bani. Yanzu zan tafi da shi, zan yi wani ɗan aiki ne da shi. Wannan kuma jininta za'a ɗiba. Ya fito da sirinjin ɗaga aƙwatin hannunsa, sannan ya ɗauko wani abu yasa a kunnanshi, sai na ga ya ɗaure mini hannu da wani abu kamar balt (belt). "Ba hawan jini, Yallaɓai,a taimaka a bayar da jinin da fitsarin." Ya janyo sirinjin zai ɗauki jini. Yana sa allurar na ɗan yi ƴar ƙara. "Ka bi a hankali fa,in har da ciwo ka barshi kawai." "Ai an ɗauka ma, sannu." Ya kama ni ya kai ni banɗaki, sai da muka isa ya tsayar da ni, ya tallabe kumatuna, ya dinga shafa su. Da gani ya rasa me zai ce sai kawai na ga ya haɗa bakina da nasa yana tsotsa, ya sake ni. "Ya zan yi Yasmin?" "Bana jin ciwon fa." "Ga jikinki nan da zafi, ga shi har jikinki ya yi laushi." Ya sake ni ya fito kawa. "Ina fitowa da ƴar ƙwalbar fitsarin a hannuna ya yi sauri ya tarye ni ya karba. "Tashi likita." Ya kalli agogon hannunsa, ƙarfe huɗu da rabi. "Nan da biyar da ashirin ina son in ganka cikin gidan nan." Da rawar jiki likita ya karɓa ya tafi yana cewa, "Insha Allahu Yallaɓai, alheri ne." Ni ke ƙwance, lulluɓe da bargo, shi kuwa tsugunne a bakin gado, yana ta faman shafa mini fuskata da bayan hannunsa, na mayar da idanuwana na lumshe, sai na ji yana cewa. "Yasmin." Da sauri na buɗe ido, sai na ga ya yi ajiyar zuciya. "How do you fell? "Da sauƙi." Ana haka Mama ta shigo har da Hajiya Kilishi da wasu su uku. Ya yi saurin taryarsu. "Mama ga ta nan,zo taɓa jikinta ki ji." "To mu je." Suka iso gabana. "Yasmin ya ya jikin?" "Taɓa jikinta ki ji Mama." "Na gani ma ba sai an taɓa ba, likita ya zo?" "Yanzu ya tafi, amma yanzu zai dawo." "To shi kenan, bari mu jira dawowarsa, sannu Yasmin." Na ɗaga kai, dukkansu ma suka yi mini sannu, sannan na ji Mama ta ce bari su zauna a nan falo, shi kuwa cewa yake. "Mama kada ku tafi fa, Mama mutuwa za tayi?. "A'a." "Za ta tashi." "Eh." Ta juya suka tafi. Ko awa ɗaya ba a cika ba, sai ga likita ɗauke da wata ƴar talabijin ɗin ƙwamfuta da shi da wani ɗauke da wasu tarkace a hannunsa. Ya shigo, ya gama jonawa cikin mintunan daba su wuce biyar ba, sannan ya iso wajen Yarima da yake tsaye a kaina." Yallaɓai muna son za mu ɗauko hoton marar ta kawai." "Bismillah." "Tsaya ina zuwa." Ya iso ya janye rigata a hankali, tare da rigar ciki ta shimi. Cikin ƴan mintuna ya ce ya gama. "Me ye." "Bari mu yi magana da Hajiya, tana falo." Ya juya ya fita. Cikin mintuna biyar ya leƙo ya ce zai tafi,yana fita su Mama suka shigo. "Yasmin mu mun tafi, Allah ya bayar da lafiya." "Mama me ye wai.? Me likita ya ce muku?" Ko nima sai na ji gabana na faɗuwa da sauri da sauri,cutar me gare ni kuma? Na tambayi kaina. Tambayar da Yarima ya ƙara yi wa Mama ita ta mayar da hankalina gare su. "Mama don Allah ki gaya mini?" "Wai me yasa baka tambayar Hajiya ga ta nan sai ni da ka raina? Ku mu je ku ƙyale su." Suka yi gaba abinsu, sai ya bi Hajiya. "Hajiya me ye?" Sai da ta kusa isa ƙofar fita, sai na ga ta tsaya. Bana jin abin da suke faɗa, amma ni tuni har gefen filona ya jiƙe da hawaye, balle yanda na ji amsar da Mama ta bayar. Ina kallon su shi da Hajiya, sai na ga ya dafe ƙirji duk hannu biyun,can kuma na ga ya durƙusa ƙasa da gwiwoyinsa duk biyu. Amma sai na ga yana dariya, ya ɗaga hannu sama, ita ma Hajiya ta yi waje tana dariya. Tana fita, na ga ya rugo a guje ya faɗa saman gadon, cewa yake. "Allah kana ƙaunata, da za ka ƙara mayar da Yasmin ta zama tawa har abada." Ya wuntsulo ƙasa ya tsugunna, sai na ga ya janye bargon jikina, ya ɗaga cikina ya shafa fatar shi, ya sunkuya ya sumbace shi. Ya ɗago ga fuskata, ya goge hawayen da yake ta ƙwarara a gare ta. "Yasmin na rasa da wane baki zan yi miki godiya." Ya sumbaci goshina, ya dawo ya shafa cikina. "Yasmin abin farin ciki ya same mu ya ya zan yi miki bayanin shi?" Ya ɗago ya ƙura mini idanuwan nan nasa masu firgita ƙaramin yaro. Ya ɗago cikina sosai ya rungume shi, tare da ƙwantawa a saman sa. Ya ɗago, "Baby na ne a nan Yasmin. Na zama Daddy daga yau, kada ki ƙara kira na da Yarima, sai dai Baban Yarima." Ya kanga kunnensa. "Lah! Yasmin,kin ji wai ƴan biyu ne." Nan take na gano me yake nufi. Kunya ta yi saurin dirar mini. A take na tambayi kaina, kenan ciki gare ni? To ni ya zan cewa Daddyna,in ya ganni da ciki?. Ya matso ya ƙwantar da fuskarsa a tawa,na rufe fuskata, ya yi murmushi ya sumbaci kumatuna, tare da faɗar. "I'm

Table of Contents

Chapters

23 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});