Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 20

Chapter 20

1,212 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

motsi ba ta yi ba daga inda take zaune. Bayan Hajiya Kilishi ta taimaka mini na yi wanka da ruwa mai zafin gaske, wanda ta cika bahon wanka, ta ce in shiga. Bayan na shiga ita kuma ta zuba wani a wata tasa mai faɗin gaske (silba), ta dinga tsoma tawul a ciki tana gasa mini jikina. Ni kuwa kamar kada ta daina saboda daɗin da nake ji. Ina fitowa aka ba ni kunnun goruba cike da ƙwano aka ce in shanye shi. Ban ƙi sha ba, amma ni na san ba zan iya shanye shi ba. Lallai dole na yi mamakin har yanzu a ce Yarima bai shigo ya gan ni ba. Shin ko dai tsorona yake ji? Ko kuwa ya daina sona yanzu? Kasa ɗaurewa na yi da na kalli agogon bango na ga har baƙwai da rabi na safe ta wuce, amma Yarima ba wanda bai shigo ya yi mini sannu ba, har da Dad ɗina da yake nuna kawaici a kaina, sun shigo da shi da Mai Martaba Sarki. Ni dai kasa ɗaurewa na yi har na tambayi Hajiya Kilishi. "Hajiya ina Yarima ne? Ko ya yi tafiya?" "A'a yana nan, amma na ji Mai Martaba Sarki na cewa jikin nasa da sauƙi, yanzu haka suna wajen shi." Hankalina na ji ya tashi matuƙa, da a ƙwance nake, amma sai gani na tashi zaune. Ya zan yi ni yanzu? Na tambayi zuciyata. Sai kawai na ji na miƙe tsaye. Hajiya ta yi saurin kama ni. "Me ye?" "Hajiya zan iya zuwa wajen Yarima?" Eh,mu ma yanzu can zamu. Su Mamee ma na can tun ɗazu. Amma ganina da kinyi haƙuri sai Sarki ya tafi da mutanen shi,ki ƙwantar da hankalinki, ba abin da ya same shi, razana ce kawai ya yi." ##### [3/1, 22:22] Ummi Tandama😇: *ƘASAITA BOOK 3* *NA* *MARYAM KABIR MASHI* Page 12 Ya ya zanyi? Dole na bi maganar manyana. Haka dole na koma na ƙwanta, amma hankalina duk baya jikina. Gudun kada a ce mini Yariman ya mutu, amma kaɗan-kaɗan na tambayi duk wanda na ga ya shigo, cewa, "Ina Yarima?" Sai dai su bani amsa da yana nan lafiya. Ƙarfe biyu saura minti goma sha ɗaya na ga Yarima ya shigo cikin sauri. Yana shigowa ina ƙwance, ganinsa yasa na yi saurin tashi tsaye. Ya iso ya kama cinyoyin hannuwana duk biyun, ya zame hannayensa suka sauko ga ƴan yatsuna. Ya dawo da hannayensa ya shafi wuyana da su, ya tallabe kumatuna ya kalleni. Sai a lokacin na ga ya yi murmushi, ya mayar da ni ya rungume gam a jikinsa, ya ɗagoni ya zaunar da ni a bakin gado, shi kuwa ya tsugunna a gabana, da gani ya rasa ya zai yi mini. Sai na ga yasa ɗan yatsana a bakinsa. A tunanina wasa zai yi mini,sai kawai ya cije ni, na sa ƙara irin wacce ke dawo da hankalin Yarima a gareni, sai kawai na ga yasa dariya. Nima ban san lokacin da nasa tawa dariyar ba. Sai na ga ya hayo gadon shi ma yana mai cigaba da dariya, ya mayar da ni ya rungume a jikinsa. Sai kawai na ji lema na tsiyaya cikin rigata ta bayana, na ɗago kansa. "Yarima me ye kuma na fitar da hawaye bayan ga ni?" "Yasmin da kin mutu da ya zanyi da ra....." "Haba Yarima, kamar ba Musulmi ba,za ka dinga kawowa kanka irin wannan tunanin, ba ka san Allah mai rahama mai jin ƙai ne ba. Yanda Allah ya ɗauke maka ni, haka zai musanya maka da wacce ta fi ni." "Ki yi shiru Yasmin,ke dai kawai ki taimaka mini da murna, da addu'ar godiya ga Allah da ya bar mini ke." Hawaye ya tsiyayo a kumatunsa. "Ba zan taɓa iya ƙwatanta miki yanda na ji rayuwata ta koma ba a cikin ƙanƙanin lokaci." "To ba sai..." Jakadiya ce ta yi sallama, muka saki juna, sannan na ce ta shigo. Ta shigo tana rawar jiki da yaro rungume a hannunta. Har a lokacin ban fahimci me ta shigo yi ba, sai da ta durƙusa gabanmu tare da gaisuwar ta ta miƙo mini yaron hannunta. Sannan na tuna ashe fa haihuwa na yi,ni na ma yi tunanin abin da na haifa ya mutu, shi yasa ban ma neme shi ba. Yarima ya miƙa hannu ya karɓa, ya ce da jakadiya, "Su Mai Martaba suna nan?" Ta amsa da, "Suna fada,su Mama ne dai suka tafi." Ya miƙo mini jaririn hannunsa ya miƙe. "Tsaya ki kula da ita,in je in dawo" Jakadiya ta ce, "To." Shi kuma ya sunkuyo ya sumbaci goshina sannan ya tafi. Sai da na ga fitarsa sannan na dawo da kallona ga abin da ke hannuna, "Mace ce ko namiji?" Na tambayi jakadiya. Ta amsa da "Namiji ne." "Ina Suhailat?" "Mama ta tafi da su ita da Ammar." "Me yasa ba su zo yi mini sallama ba?" "Saboda Yarima. Kai Gimbiya ki godewa Allah, Allah Yarima yana son ki,sumansa biyar da aka ce masa kin mutu. Ki duba taurin rai irin na Allah ya ja da rai, amma sai ga shi yana kuka a gaban kowa." Na yi murmushi irin na wanda ya tashi daga ciwo, sannan na lalubi mama na sawa jariri a baki. Sai da ya kama maman, sannan na samu damar kallonsa sosai, abin ka da jariri sai na kasa gane da wa ya yi kama. Ina cikin ƙoƙarin gano hakan Aunty Salwa ta shigo. **** **** **** Rana ta zagayo aka sawa yaro suna Abdul Nasir,amma ba a yi wani taro ba, saboda jikina ya ƙara warwarewa, saboda haka Mai Martaba Sarki ya ce a barshi sai wani satin. Wannan yasa aka ƙara sa masu kulawa da ni su matso kusa da ni domin kulawa da ni sosai. Su Ammar kuwa sun zama ƴan gidan Mama, saboda sai dai su zo da yawo su koma. Bayan ƙwana uku da raɗin suna sai aka shigo falo na uku wanda nake zama domin hutawa, aka ce na yi baƙi. Ban tsaya neman ba'asi ba na ce su shigo. Sauran kaɗan in saki Abdul-Nasir ƙasa, saboda mamakin ganin baƙin su huɗu da na yi. Maza biyu, mata biyu,ba zancen koƙwanto na gane su, duk da sun canja kamaninsu. Cikin al'ajabi na kira sunan ɗaya daga cikin su. "Mansura! Daga ina ku ke haka?" Madadin su yi magana, sai kawai na ga Mansura tasa kuka, ƴar'uwarta Musulum na taya ta ko kuwa in ce suna taya juna. "Su waye waɗannan?" Na tambaye su. "Mazanmu ne, wannan mijin Mansura, wannan kuwa nawa." "Daga ina ku ke haka? Ya aka yi ku ka san muna nan? Wa ya nuna muku gidan?" "Mu ma labari muka samu, shi ne muka ce bari mu zo. Yanzu kuma muna ƙauyen Fembeguwa a zaune, saboda tsoron zama cikin birni gudun kada a sa a kamo mu." Na kalli wacce ke kusa da ni, "A tafi da su wajen Sarkin gida ki ce baƙina ne a basu ɗakuna biyu, kowacce da mijinta. Ke kuma ki sa a basu komai da komai,ki tabbatar sun ci abinci.” Na juya ga su Mansura, "Ku je a baku masauki zan neme ku in kun huta." "Mun gode. Amma za mu koma mu ɗauko yaranmu." "Kun haihu ne?* "Eh,

Table of Contents

Chapters

23 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});