Chapter 22
Chapter 22
ka ƙyale? Mijinki ne fa, shi kenan na gode." Ya samu ɗan tsayin lokaci, sannan na ji sallamar mata. Inda na ke zaune na ji gabana ya faɗi. "Ku shigo jakadiya." Jakadiya na gaba ragowar na biye da ita har gaban wanda ya basu iznin shigowa ɗakin. "Barka da dare?" Haka na ji an ce cikin siririyar murya. "Barka da zuwa amarya." Jin an zauna kusa da ni yasa hankalina ya dawo dai-dai. "Yasmin." Na ji an ambaci sunana. Ban iya amsawa ba. Bai jira na amsa ba ya ci gaba. "Wannan ita ce ƙanwar ki Asabe, daga yau kin zama babba a gidan nan, saboda haka ki riƙe girman ki." Ya juya ga Asabe ya ce, "Asabe." "Na'am, Sarkin Sarakuna." A take na ji wasu abubuwa guda uku sun tsaya a ƙirjina. "Wannan ita ce Yayarki,kin gan ta, aure ne tsakanina da ita, ina son ta matuƙa, ita ce sirrin zuciyata, ita ce ƘASAITAR jikina, saboda haka kiyi biyayya a gare ta,idan kuwa na samu akasin haka, zan saɓa miki matuƙa." "Yasmin ga Asabe.” Na ƙi motsawa. "Asabe ga Yayarki Gimbiya Yasmin.” "Allah ya ja da ran Gimbiya Yayata.” Na ji an dafa mini ƴan yatsun ƙafa ta. Wannan ya ba ni damar matse jaririna a jikina, har yasa ihu. "Yasmin,kawo shi. Ke sakar shi kin matse shi da yawa. Jakadiya ku tafi gani nan zuwa." Ina jin fitar su jakadiya, sai na ji abubuwan nan uku sun danne mini ƙirji,da ƙyar lumfashina ke fita. Ina jin shi yasha kokawar ƙwaƙule Abdul-Nasir da ke ƙwalla kuka, amma na hana. Ina ji ya hayo gado sosai, ya bi bayana. A daidai kunnena na ji yana magana, tare da zuge zub ɗin rigar baccina. "My love, kada ki sa zuciyata ta fashe mana,ki yi tunanin alƙawarin da ki ka ɗauka a Kaduna, wannan alƙawari sai da na nanata shi a gaban Sarki, saboda hotunan da aka kai masa da kaset, na san ba ki san ko waɗanne ba ne. Waɗanda ki kasa aka yi a mota lokacin da ki ka tsare ni, lokacin da ki ka sa aka kai ni a hotel na yi ƙwana uku ban ga ƙyakƙyawar fuskar ki ba." Ya saɓule rigar jikina yasa hannunsa ta bayana ya rungume ni. "Yasmin ba zan iya son kowacce mace ba sai ke. Please ba ni Abdul ki tuna wahalar da muka sha kafin mu same shi.” Lallashin yasa na miƙa masa Nasir,sai na ji yana ta lallashin shi, amma ya ƙi yin shiru. Ya zagayo ya ɗora shi a cinyata ya zaro mama ya saka masa a baki. Yaro ya dinga sha, wannan yasa na saka kuka. "Me ye na kuka Yasmin?" "Ɗanka ne fa." Na cuci kaina dana tuno abin da na sa aka yi maka a hotel. Haya na ɗauki wata karuwa, aka ba shi baliyan maganin bacci, ya sha, shi ne ta cire masa riga, ita ma ta cire ta ƙwanta a ƙirjinsa, shi ne nasa aka ɗauke su hoto. Haka sai kuma muka haɗa kai da ita a kan ta san yanda aka yi aka haɗa wannan kaset ɗin. Haushi takaici suka tarar mini. Ya tsugunno gabana, "Honey zan tafi" na yi shiru. "Ba za ki yi mini addu'ar dawo lafiya ba?" Wani ƙwarin gwiwa ya zo mini da na tuna abin da Aunty Salwa take gaya mini a kan idan namiji na son abu,ka nuna ka fi shi so, haushi ma ka ke bashi. "Na ji kin yi shiru?" "Yanzu zan yi magana ka riga ni. A dawo lafiya, a gaishe da amarya.” "A'a, sai dai ki zo mu je ki raka ni.” "Ba damuwa, jira ni Abdul Nasir, ya kammala sai na raka ka. Ka sa manyan kaya mana." "A'a waɗannan ma sun isa,gudun kada ta sha wahala wajen tuɓe mini." Na harare shi kaɗan, "Ni tashi mu tafi." "Ba komai in na je zan gaya mata,in ce harara ta ma ki ka yi. Amma bayan kin gama kuka." "Ni ba kai nayi wa kuka ba, kaina na yi wa kuka. Ka ga a daina wannan maganar, tashi mu je. Amma gaskiya sai an gyara ka." Na miƙe na ajiye Nasir,na isa na ɗauko wata sabuwar doguwar rigar hutawa da alkyabba na iso gaban shi. Yana tsaye na cire kayan jikinshi na sa masa sababbi, ban da turare da na dinga fesa masa. Ni ce har da farar hoda sai da na shafa masa, saboda ya ƙara fitowa. Kallon mamaki na ga yana yi mini. Na ɗauko takalma na durƙusa na ajiye masa. Ina ɗagowa zan juya ya riƙo hannuna, madadin ya yi magana, sai kawai na ga ya haɗa ni da jikinsa, haɗa kumatuna ya yi duk biyun ya ɗago su sama, sai kawai na ga ya haɗa bakina da nasa yana tsotsa kamar zai mayar da ni ciki. Har wani jikinshi ke rawa. Na ɗago kansa, "Lafiya Yarima?" Bai iya amsa mini ba. Zame jikina daga gare shi na yi, na tafi cire rigar baccin jikina, ina faɗar. "A yi rakiyar ango da rigar bacci?" Sai da na tabbatar ni yake kallo, sannan na saki rigar baccin ƙasa, daga ni sai ɗan wando, sai kuwa rigar mama, sannan na ɗauko kaya na fara sakawa. Jin an riƙe mini hannuwa, waɗanda ke ƙulle zanena ta baya, shi yasa na ɗan yi alamar na tsorata. "Au! Da kai ne har ka bani tsoro?" Na juya zan cigaba, ya riƙe ni. "Yasmin kin daina sona ne?" "Me ka gani?" "Ga ni nayi murna ki ke yi zan tafi in barki." "Ba haka ba ne ba,dama ai yanzu dole ne so ya ragu, tun da mun zama mu biyu, balle ita fa ganinta ka yi ka ce kana son ta. Ni kuwa fa,ƙyauta ta aka yi....." Ya zagayo gabana tare da nuna hankalinsa ya tashi, ya riƙe kafaɗuna ya zame hannayena da ganin yanda yake yi ya rasa yanda zai yi, ya ɗauko rigar da alkyabba ya miƙo mini. "Sa ka zo mu tafi. Ya juya ya ɗauki Nasir,ni kuwa a hankali na saka kayana, ganin na cika nawa, ya zo ya kama hannuna, hannu ɗaya na tallabe da Nasir. Kusan in ce ja na ya dinga yi ba ma tafiya ba da sauri. Bai zame ko ina ba sai ɗakin jakadiya, wanda yake sashen gidana. "Jakadiya." Kiran da ya yi mata kenan. Ta fito da sauri tare da kifawa ƙasa da sauri. "Ga ni Allah ya huci zuciya, daidai nake da a hukunta ni idan har an same ni da laifi." "Mansura! Ina Mansura?" "Tana ciki?" "Kira ta.” Ta miƙe da saurinta ta shiga wani ɗaki,a inda na ga ta shigo da amaryar da aka kai min ɗakina. A tsaye na yi wa kaina tagwayen tambayoyi. "Shin Mansura ya aura? Ina mijinta? Amanata suka ci ko me? Ai kuwa...." "Jakadiya ya aka yi?" "Allah ya ja da ran Gimbiya,dama haɗa baki muka yi da Mai Martaba Yarima, ya ce a rufawa Mansura kaya a kai masa ita domin a zolaye ki, saboda ya zamo jan kunne a gare ki na ƙin daina yiwa mijinki alƙawarin kin amincewa ya yi aure.” "To kin ganta nan, nuna mini ta yi bata sona yanzu don na yi haka." Na san halin Yarima a kaina, wannan yasa na yi
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23