Chapter 17
Chapter 17
kan ƙanƙanin abu ki ce ba zaki zauna da ni ba." "Kai ka ɗauke shi ƙarami." "Yasmin ke nake ji, ina son ki,ina son zama da ke, muddin na karɓi sarautar nan sai ya zamo na yi miki amarya." Ɗan cikina ya sake wajen ƙwanciya da saurin gaske, saboda tashin hankalin da maganar Yarima ta haifar. Jinyar sakan biyar na yi sannan na yi magana. "Na amince ka yi idan dai har za ka bi maganar iyayenka." "Yasmin kin kuwa ji abin da na faɗa?" "Na ji, cewa ka yi zakayi min amarya,ko ba haka ka faɗa ba?" "Haka na faɗa,kin amince?" "Eh, amma kai ma in ka amince gobe da safe za mu je Jos,ka gayawa Sarki ka amince da abin da yake so, sannan za ka koma Jos da zama,in ba haka ba,yau ba zan ƙwana gidan ka ba." "Wannan ma bata taso ba,dama na ga wata yarinya ɗazun da na dawo daga lambu, sai kallona take yi,kin ga shi kenan sai in koma in gani. "Ƴar gayu ce." Na yi murmushi, "Ƙyan Namiji dama ya auri mace wacce ya gani da idonsa ya ji ta ƙwanta masa a zuciya, ba wai wani ya gane masa ba." "Yasmin kenan, ba ki san cewa matar daraja da ɗaukaka ta bi bayan zaɓin Iyaye....." "Ya isa,mu je mu ƙwanta." "Cikin fa?" "Ya lafa, zan iya kai wa safe." Ya kama ni muka je muka ƙwanta. **** **** **** ** Taro kan ya haɗo jama'a, ta ko'ina, sai isowa suke yi. Manyan sarakuna na ƙasa, gwamnoni,kai har da shugabannin kasashe, duk sun iso filin jirgi na garin Jos. Mu kuwa muna gefen mata, wajen su Mama, amma ni ma da tawa gayyar a bayana. Yarima na can daga sashen su Mai Martaba ya sha alkyabbar alfarma. Abin ka ga farin mutum, ya yi ƙyau, wanda ba ya misaltuwa. Ni kuwa ni da Aunty Salwa daga ni sai ita muna hirar jama'ar da ke wucewa. Bayan kamar awa biyu kowa ya gama zama aka ce Sarkin Malaman Sarakuna ya zo ya buɗe filin taro da addu'a (Adalin Sarki kenan,Sarkin Musulmai Dr. Usman Nagwaggo) Sarkin Katsina kenan. Dattijo fari tas, mai ruwan matasan yara, jikinsa ba ya tsufa. Shi ya fito ya fara jero addu'o'in buɗe taro tamkar wanda ya girma a tsakiyar Larabawa, saboda harshen da ya karya tamkar na matashin Balarabe. Tsayawa bayanin abubuwan da aka yi ma mun san ɓatawa kanmu lokaci ne, balle lissafa manyan da suka halarta. Amma mun san Sarkin Sarakuna na Nijeriya, manya ba wani a gabanka, shi ya yi naɗin sarautar,wato Mai Martaba Alhaji.Dr. Ado Bayero, wanda jama'a ke so kenan. **** **** **** Wani irin mahaukacin gida ne aka bai wa Yarima, har sai da ya ba ni tsoro. Na kalli gidan, daga ni sai ƴaƴana biyu, sai cikin da ke jikina wanda bai wuce wata baƙwai ba. Masu yi mana hidima kuwa ba su ƙirguwa, amma Mama ta ce in dinga yi wa mijina abinci da kaina. Haka kuwa aka yi, duk na ware ɗaki ɗaya na mayar da shi kicin ɗin kaina, wanda ni kaɗai ke shigarsa, sai kuwa ƴaƴana, amma ko jakadiya shakkun shigarta ciki nake yi. Tsarin kundin littafin mulkin aka damƙawa Yarima domin ya yi nazarinsa, duk da ba wai shi kenan Mai Martaba ya daina aiki ba, a'a mulkin na ga hannun Mai Martaba, Yarima kamar ɗalibi ne da malami, wato ya koyi yanda ake yi, tun kafin Mai Martaba ya rasu ko kuwa ya yi tsufan da ko ya yi magana ma jama'arsa ba za su saurare shi ba,ko kuwa a dinga cewa ruɗin tsufa ne, amma yanzu da hankalinsa, duk abin da aka yi ba daidai ba zai tsawatar. Dama su tsarin mulkinsu kenan, shi ne a baiwa wanda ake ganin ya cancanta a baiwa sarauta, tun Sarki na da rai, ba don komai ba sai don ya ga yanda zai tafiyar da nashi tsarin mulkin, saboda in ya yi kuskure a nuna masa hanyar gyara. Shi kuwa Yarima, sabon tsari muka zauna muka gyarawa littafin nan, saboda wani al'amarin da ake yi yakan ɗan taɓa talakawa, sannan shi Addininmu ya nuna za'a tambayi duk wani mai mulki haƙƙin yanda ya tafiyar da talakawansa. *** *** *** *** Tsarin da Mai Martaba na biyu ya yi, ya burge kowa, ya kuma ƙara masa farin jini a wajen talakawansa. Tsarin kuwa shi ne da kansa ya zagaya garin Jos da kewayenta domin sanin halin da talakawansa ke ciki. Wasu lokutan kuwa ma ba a shigowa a mota sai a ƙafa, wasu kuwa ƙwatami ya yi yawa, wasu ƙauyukan kuma da ƙafa ake zuwansu. Wannan rangadi ya ɗauke shi tsayin wata biyu har da ƙwanaki goma sha baƙwai,yana yin shi. Wata rana Yarima ya dawo da fara'a, wata rana kuwa da kuka yake iso mini,saboda irin ganin da idonsa ya yi na halin da talakawansa ke ciki. Ni kuwa ciki ya tsufa, amma har yanzu haihuwa ta ƙi zuwa, wanda zan iya cewa na shanye watan haihuwata, ma'ana na wuce watan haihuwata. Wannan kuwa ya tayar da hankalin Mai Martaba na biyu, Yarima kenan. Ƙarfe tara na dare shi ne ƙa'idar tashin Yarima daga fada, saboda ya samu lokacin hira da iyalinsa. Yau ma kuwa haka ya shigo gida, ya sameni ƙwance a ƙasan kafet ɗin da kusan launinsu ɗaya da katifa. Suhailat na ƙwance a gabana ta yi bacci. Yanayin yanda fuskarsa ta nuna shine yana tausaya mini. Yana isowa ya sunkuya ya ɗauki Suhailat ya kai ta ɗakinsu, sannan ya dawo ya durƙusa a gabana. Ya sunkuya ya sumbaci kumatuna. "Sannu." Na ɗan yi fari da idanuwana "Wallahi Yasmin ina tausaya miki." *Ni kuma kai nake tausayawa, saboda aikin da ke gabanka na jagorantar mu. Ga ni da ƴaƴanka,iyayenka da nawa,ga jama'ar garin. Ga jama'ar garin nan ba ki ɗaya duk fa a ƙarƙashin ka muke. Yanzu in mutuwa ta kama ka ka ce da Allah me?" "Wallahi kuwa,ai shi yasa nake son in ga kin haihu lafiya sai mu zauna mu yi shawarar ya zamu yi balle dama duk inda muka je an ɗaukar min shi a kaset, sai mu sa a tsanake mu ƙara gani." "Honey,tunda haihuwar ta ƙi zuwa me zai hana a fara, tun da idona da bakina za su yi aikin ba cikina ba. Yanzu da ka ce a bari sai na haihu,to in na mutu wajen haihuwar fa..." "Haba Yasmin ki daina irin wannan mummunar maganar ta ƙananan yara,me ki ke so na koma idan na rasa ki?" "Baka zama komai." "Na ji nidai ba na son ki dinga yi mini irin waɗannan maganganun marasa daɗi da ɗaci." Ya juya har da ɓata rai sosai. Hannu na sa na juyo fuskarsa. "Sorry, ba zan kuma ba na daina." Na faɗa cikin muryar nadama. Ya ɗago fuskata ya ƙura mini ido, sai kawai na ga ya kai bakinsa ga nawa. Mun yi minti huɗu ya ɗago. "Yasmin ni fa har yanzu son ki bai taɓa raguwa a zuciyata ba,kin san Allah duk every day, every time, every minute,every second,sai na ji sonki yana ƙaruwa a zuciyata. Ki daina gaya mini maganar da raina zai ɓaci,ki tayarwa da mijinki hankali,kin ji?" Na ɗaga kai alamar eh. "To bari na ɗauko kaset ɗaya
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23