Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 16

Chapter 16

1,229 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

ƴan baiwa Yarima haƙuri, da ba shi baki akan ya koma gida. Amma maganar shi ɗaya ce Kaduna ta yi masa, shi hankalin shi a ƙwance yake. Yau kuwa manyan baƙi ne, wato ƙungiyar su Waziri, amma Yarima ya ƙiya. Da na je gaishe su suka dinga roƙona a kan in ja hankalinsa in nuna masa muhimmancin mutanen da zasu zauna a ƙarƙashinsa. Na bisu da to. Amma na san ba zan iya tunkarar Yarima da wannan maganar ba. Su Daddyna sun zo tare da Mamee, amma sai ya ce masu insha Allahu zai yi,su bashi lokacin ya yi tunani. Haka suka tafi suna murna. Amma suna tafiya ya ce ai shi sam,kunyar su tasa ya amsa masu. To ni kuwa dama da na ɗauko hanyar yi masa maganar, kallo ɗaya yake yi mani in yi shiru. Wani lokacin ma har in samu la'adar cewa ba ni da hankali. Sarki Jafar Sada ne yau da kanshi da Iyalansa gaba ɗaya a gidan mu,Mama, Hajiya Kilishi, Ahmad,Yaya Salimat,Sauda, da Idris,Sarki ya yi gyaran muryar da dukkanmu sai da muka nutsu, sannan ya soma magana. "Faysal my lovely son. Da farko zan fara da roƙon Allah ya raya maka zuri'arka, ya yi maka sakayya da aljannar fiddausi. Faysal,sanin kanka ne ba mai raba ni da kai sai Allah, amma akasi ya faru tsakaninmu ta sanadiyyar yaudara da aka fara yi ta hanyar gaya mana aibunka da illolinka. Ban yarda ba da farko, sai da aka kawo mini shaida ta zahiri." Ya buɗe wata ambulan ya miƙawa Yarima kaset da wasu hotuna. "Duba!" Ya ajiye. Ban kawowa raina komai ba. Ta haka ta fara yaudara ta. Ganin raina ya ɓaci matuƙa har na ɗan yi fushin ƙwanaki da kai,ai sai wannan hanyar ta ba shi damar shigo da abubuwan da na san sun daɗe yana tanadar su. Magana dai ni ke son ta wuce,a taƙaice ina neman a yi haƙuri a kan duk abubuwan da suka wuce,a taryi gaba,a kiyaye. Ko kana da magana?" "Baba ni ban ce kayi mini laifi ba,ni ban riƙe kowa ba,ni dai nayi kokawar ƙwato maku ƴanci ne don kuna iyayena, amma ba don na hau gadon mulki ba. Na gode ƙwarai da ƙyautar da ka yi mini da nuna ƙauna, amma na barwa ɗaya daga cikin ƙannena,ai su ma sun girma. Amma ni Kaduna zan cigaba da zama, saboda hanyoyin cin....." Ya miƙe ya je ya tsugunna ya kai gaisuwa. "Amma idan na ɓata muku rai ku gafarce ni." Ya miƙe ya shiga ciki. Falon mu ya yi shiru har tsayin mintuna masu tsayi. Can Sarki ya nisa, "Yasmin, Hajiya Mariya, Hajiya Kilishi, aikin ku ne,kushawo kan ɗanku. Ke kuma mijinki. Koma in ce aikin ki ne. Yasmin ki taimaka ki shawo mana kan mijinki, ya taimaki jama'ar da ba mu san iyakacinta ba." Ba ni da damar yin gardama, sai dai na bishi da, "To Baba, za'ayi ƙoƙari." Ni kuwa har hantar cikina sai da ta kaɗa. Daga nan kuwa aka cigaba da ƴar hira, jin falon ya kaure da surutu yasa Yarima ya shigo shi ma ya zauna aka ci gaba da yi dashi. Sai da suka ci abincin ranar mu, sannan suka tafi,mu kuwa rakiya har mota. Yau an samu shiga, bayan mun dawo hirar mu kawai muka cigaba har ya tafi gona. Bayan mun shiga ɗaki ne har ma mun yi niyyar ƙwanciya kenan an gama duk wata hira. Na ɗauko Novelle Gelly ina shafawa a jikina, domin jikina ya ɗau ƙamshi gaba ɗayan shi. Gefen gado na zauna, amma gabana ke ta wani irin mummunan faɗuwa, saboda maganar da nake son ta fito daga bakina. Ban kashe fitila ba na hayo gado na zauna kusa da shi tare da robar man ƙamshin jikin nan a hannuna,sai kuwa kaɗawa take yi, da alama jikina ke rawa. Sai da na karanta addu'a sannan na ambaci sunan shi. _Ya waliyyan ni'imati,wa mallazi inda kurbati,ij'alni matahu bardan wasalam alayya kama ja'altana barda wassalamun ala Ibrahim (Ƙafa baƙwai). "Honey." Na kira shi a sanyaye. "Ina jin ki Sweetyna." Ya faɗa, har da ɗora hannunsa a saman cinyata. "Magana nake son mu yi da kai mai mahimmanci." "Ina jin ki. In kuma so ake in ƙara wani cikin, to ban manta ba." Ya faɗa har da ɗan taɓa mini gefen cikina. Na yi murmushin da yake haɗe da fargaba. "Honey maganar sarau...." Wata tsawa da ya daka mini. Bani ba,na yi imani maigadi ma ya tsorata. Ni kuwa har na kai bakin gado, saboda na yi zaton duka ne zai biyo baya. Tun kuwa da na sauka, na durƙushe nake jin ɗan cikina na mutsulniya, tamkar ɗan kifi a ruwa. Bai ƙara cewa ƙala ba daga wannan, sai ma ya juya min baya. Gaskiya na san na yi awa ɗaya durƙushen nan, ina saƙa hanyoyin da zan bi. Ganin ba shi da wani alamun motsi ballantana in san hanyar da zan bi, sai na ce, "Wash! Wash!! Wash!!! Cikina." Ina faɗar cikina na ga ya yi saurin saukowa. Tun daga can na ji yana cewa, "Me ya samu cikin? Da ke nake,me ya samu cikin?" "Ciwo yake. Marata!" "Tashi mu gani." Ya yi saurin isowa ya kama ni. Na lanƙwashe. "Ba zan iya ba, ina jin ɓari zan yi." "What? To kin ga ni ga irin ta nan,kin sawa ranki abin da ba ruwanki, ga shi nan za ki janyo mana asarar ƴaƴana. Taso mana mu tafi asibiti." Ya sake ni, ya tafi ya buɗe durowa ya ƙwaso mana kaya. Ya zo ya kama ni. "Tashi, sannu." Ya yi alamar ɗaga ni. Na riƙe hannunsa. "Yarima!” "Ba na ce bana son kina kirana da wannan sunan ba?" "Na sani,ka yi haƙuri, amma yau ne na ƙarshe, tunda ka nuna mini ba ni da amfanin komai a wajen ka. Yau zan haƙura da auranka,gara ka auro wacce take da muhimmanci da amfani a wajenka." Sannan nasa kuka. Ina jin sa ya tsugunno. "Yasmin me ya faru? Me na yi miki? Ba ki taɓa gaya mini magana mai ɗaci ba sai yau." "Yau ma kamawa ta yi." Ya ɗago kumatuna. "Haba Yasmin, ya zaki tayar da hankalin mijinki...." "Ba ka son a tayar da hankalin ka, amma kai zaka tayar da na mahaifinka?" "Ba ruwan ki da maganar mu." "Kenan ba ruwan ka da ni? Don Allah in tambaye ka?" "Ina jin ki." "Yanzu me ye nan cikina?" "Ɗana ne." "Kana son shi ko baka so?" ###### [2/28, 08:27] Ummi Tandama😇: *ƘASAITA BOOK 3* *NA* *MARYAM KABIR MASHI* Page 10 "Wacce irin magana ce wannan Yasmin?" "Ka ce mini eh ko a'a." "Ina son shi mana." "In ya zube za ka ji ciwo." "Ƙwarai kuwa." "To ka yi tunanin irin ciwon da za ka ji,ka ƙwatanta shi ga in ka rasa ɗan da ya girma za ka ji ciwo. To mahaifinka abin da yake ji a zuciyarshi ya linka naka dubu, kuma tunda ba ka jin ban haƙurin shi, to ni ma ba zan ji ban haƙurin ka ba, zan bar maka gidanka da ƴaƴanka, amma zan tafi da cikin jikina,in je Likita ya cire mini...." "Ki rufa mini asiri Yasmin,duk wata taƙamata taki ce,kin zauna da ni a lokacin da na shiga babban tashin hankali, sai kuma yanzu a

Table of Contents

Chapters

23 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});