Chapter 4
Chapter 4
zai iya janyowa mutane su tsane ni." Ya ɗago ni sosai, "Su tsane ki,su waye mutanen? Wa ya fara canja maki fuska? Gaya mini,kina so in sa duk a kashe su?" Na yi saurin rufe bakinsa cikin tashin hankali, kamar yanda na ga har ya rikiɗe mini ya koma Yariman farko. Na yi sauri na sulale ƙasan mota tare da riƙe hannuwansa. "Za ka yarda da duk abin da na faɗa?" Ya ɗaga kansa. "Wallahi ba wanda ya taɓa canja mini fuska, kowa na sona kamar yadda ka ke sona. Ina son cewa da kai ka rinƙa ɓoye na ka ne ka bar ni in dinga fito da nawa a fili." Sai naga yayi ajiyar zuciya, amma kuma ya kasa magana, sai da ya ɗago ni ya rungume gam, tsayin minti biyu, sai na ji yana magana cikin sanyin murya. "Yasmin ba ki san yanda nake jin ki ba a zuciyata. Kin ɗauka wasa nake ko?" "A'a na san..." Ta yi daidai da buɗe motar da aka yi, ya yi sauri ya rufe cikin ƙiftawar ido, jikinsa kuwa tun a lokacin ya kama rawa. Na gyara sannan na ji ya ɗan ƙwanƙwasa gilashin motar, cikin gaggawa aka buɗe mana ta ɗaya ɓangaren, na fito, shi kuwa ta ɓangaren da yake. Sai a lokacin na fahimci gidan Aunty muka zo,gudun kada in ruga in baiwa kaina kunya da uban gidana yasa na tsaya tafiyar wahainiyar da muke ni da Yarima. Falo kawai muka isa na dinga kwala mata kira. A firgice ta fito daga ɗaki, na ƙarasa da saurin guduna na rungume ta. Ita kuwa sai dariya take yi,tana cewa in sake ta taryi baƙon ta. Mun samu sama da mintuna ashirin a gidan Aunty Salwa,sannan muka yi sallama da ita, wanda har alƙawari ya yi mini a gabanta zai kawo ni in yini in mun huta. Na dinga murna. Ganin jikin Yarima a sanyaye yasa har na fara shiga damuwa, na matsa na kama hannunsa tare da durƙusawa a ƙasan mota. "Honey,me ye ya tayar maka da hankali? Wa ye kuma? Nima fa zaka jefa ni cikin damuwa?" Ya ɗago ni ya zaunar da ni a saman cinyoyinsa, sai da ya sumbaci laɓɓana, sannan ya cire gilashin fuskarsa. "Ke ce Yasmin, hankalina ya tashi matuƙa a kan ba ki da lafiya, amma ki ka ƙi gaya mini. Yanzu me iyayen ki zasu ce? Bana kulawa da ke?" "Wallahi ni kaina ban san dalilin yin amaina ba,ni dai na san lafiyata ƙalau. Ni dai zan iya cewa ƙamshin turaren Daddy ne ya saka ni amai, kuma yanzu ni lafiyata ƙalau, zan iya yin komai, zan iya cin komai." Na koma na ƙwanta a ƙirjinsa, "Kada ka ƙara damun kanka a kaina." Sai na ga ya ɗago ni ko kasa me zai yi mini ya yi, sai kawai na ga ya dungure mini goshina. "Kada ki ƙara faɗa mini haka." A take ma sai na ji ya ba ni dariya. Na sa dariya irin ta nutsuwa, ya rungume ni, shi ma ya yi tasa dariyar irin ta su ta mulki. A hankali na ga gilashin motar mu na sauka, wannan yasa na yi saurin sauka daga cinyar mijina na gyara zamana sosai. Subhanallah! Jama'a ne tamkar su ɓall gidanmu, tun daga get ɗin gidajen har izuwa harabar gidan mu. Jinjina ake yi, gaisuwa, amma yau Yarima ya burge ni, saboda ɗaga masu hannu da yake yi har da murmushinsa, mutumin da ba ya ko motsi idan ya shiga motar nan, to balle ma an canja wata motar wacce za ta iya ƙara masa girman kai, amma abin mamaki yau har da murmushinsa. Motar mu na tsayawa na hango wani mutum a tsaye,shi kam tamkar wani saboda yanda na ga an zagaye shi. Sakan ɗaya da tsayawarta aka buɗe mana,kirari irin wanda ake wa Sarakuna, shi aka dinga yi wa Yarima. Gaisuwa da sauran hidimomi irin na sarakuna. Wani abin da ya fi burgeni, shi ne wannan mutumin da ke tsaye tsakiyar nasa dogarawan, shi na ga an yi saurin kawo aƙwatin kuɗi a gabansa, aka buɗe masa irin na matafiya,brief case. Yana ɗaukar bandir sai dai ya ɓalle ƴar takardar ya watsa su. Amma mutanen mu ko matsawa ba su yi ba, ballantana su san ana zuba kuɗi a gabansu. Sai dai ma dogari ɗaya da yake gabanmu yana share su gefe,gudun kada mu taka. Wannan kuma ina jin dokar Yarima ce,sai ma a lokacin na lura cewa ƴan ɗari bibbiyu ne ake wa wannan watsin da su. A nan na saki da sha'anin Yarima, wato har dogarawansa ma ya san yanda yake tafiyar da su. Wani abin mamaki Yarima bai tsaya wajen mutumin nan ba, ya yi wucewarsa, sai me? Ai tun daga barandar gidana na ga gidana ya canja. Ƴan matan gidana kuwa, duk sun taru a barandar, suna hango ni sai murna. Ni kaina duk sai na ji na ƙara ƙaunarsu. Mansura kuwa har da gudunta, ta iso ta durƙusa gabana ta kama hannuna. Na yi murmushi na ɗago ta, sai tasa kuka. Na yi murmushi na kama hannunta muka tafi. ##### [2/19, 22:29] Ummi Tandama😇: *ƘASAITA BOOK 3* *NA* *MARYAM KABIR MASHI* Page 3 Lallai Yarima " Na faɗa a zuciyata,ganin duk ya ƙyale mutanen da ke bin bayansa ya biyo ni gidana. Sai dai na ga ya yi wa wani dogari nuni da hannunsa. A take na ji dogarin na cewa. "Yarima ya ce a jira shi ya huta. Yarima na gaishe ku. Nan da awa biyu zai fito." Me zai faru? Ina kunna kai a gidana, na ji wani ƙamshin turaren wuta na tashi. Nan take kaina ya fara juyawa. Cikin ɗan sauri-sauri muka gaisa da jakadiya da jama'arta. Haka shi ma Yarima na ga yana gaisawa da su. Ko lura ya yi,ai muna hawa sama a guje na ƙarasa banɗaki. Yarima na bina shi ma tun kafin in kai ɗan wajen alwala,bath amai ya kubce mini. Alkyabbar jikina kuwa sai dai wata. Yarima riƙe da ni na dinga ƙwaranya amai kamar dai yanda na yi a gidanmu. Nan take na ji Yarima na waya cikin mutanen shi na ji ya yi wa ɗaya magana. Wai ina likitan da ya ce ya zo gida ya jira shi? Nan take na ji yana cewa,nan da minti biyar ya hayo sama da sauri yana son ganinsa. Ni kuwa har amai ya kai sai dai ruwa-ruwa, saboda abincin ya ƙare. Ina gamawa Yarima ya kama ni wanda jikinsa har rawa yake, ya cire mini alkyabbar jikina, ya wanke min fuska. Ban da sannu da yake yi mini, ya ɗago ni idanuwansa sun yi ja, ban da hawayen da suka cika su, ya dinga shafar fuskata. Lallai na amince Yarima son gaskiya ne a jikinsa, saboda ya rasa me zai ce mini. Ya kama ni muka fito ɗakina, ina fitowa wani sabon aman ya taso. Na koma ciki da guduna. Ya biyoni ya yi tsaye a kaina, ina ta faman yunƙurin aman da ba komai a cikina. "Mama Yasmin zata mutu ta bar ni. Ki zo Mama." Wannan maganar da ya yi ita ta tabbatar min waya ce ya yi, duk da ban iya ɗaga kaina na kalleshi ba. "Ka hawo kawai." Wannan ya tabbatar mini da likita yake. Da
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23