Chapter 12
Chapter 12
gaishe shi, sai bai amsa mini ba. Ban damu ba, saboda na yi tunanin jama'a ce ta yi masa yawa, saboda haka na yanke shawarar bin shi gida domin yi masa gaisuwa ta musamman. Ina shiga fadar sai cewa ya yi in fita. Amma a lokacin na yi zaton ɗan wasa ne na tsakanin ɗa da mahaifinsa, amma ina kin ga yanda ta kasance mana yanzu, na koma sai dai in hango mahaifina daga nesa. Jama'a sun sa baki, amma lamarin sai ƙara jagulewa ma yake yi." Ya koma ya zauna sosai, tare da janyo ni jikinsa. "Yau lamarin ya yi zafi Yasmin,saboda yau Mai Martaba ya ce na fitar masa daga gida, komai ke cikin gidan bai ce na ɗauka ba, face sutturun mu, sai kuwa motar da Waziri ya ba ki." Ya gyara ya janyo mukulli daga aljihunsa. "Kin ga waɗannan mukullan, Waziri ne ya ba ni su,wai gida ne gare shi a Sultan Road Kaduna, ya ce na je can na zauna. Yasmin kunyar ki ta hana ni shigowa inda ki ke, da tunanin kada in gaya miki ki guje ni, kema,ni na san hankalina ya tashi matuƙa, koma in ce yana cikin tashi.Amma rabuwata da ke sai ya fi nakasa mini rayuwata, saboda yanzu al'amarin ya zo da ɗan sauƙi, tunda duk ƴan fada na sona, kuma har yanzu ba su goyi bayan Sarki ba,su ma kansu suna mamakin abin da ke faruwa, dukkansu kuma suna iya ƙoƙarinsu, amma al'amarin sai haƙuri." Ya yi ɗan shiru. "Ni yanzu Mama kawai nake ji, tunda ya ce Allah ya isa idan na shigar masa gida. Yanzu ban san yanda zan yi in dinga ganinta ba, balle in yi sallama da ita a yanzu, saboda plan ɗina in bar ƙasar nan kawai,in koma Greece shi ya fiye mini ƙwanciyar hankali. Ni dai tun da kina tare da ni da sauƙi. Mahaifiyata kawai nake tausayawa." Yanda gabana ke faɗuwa idan har ka saurara kana ji, saboda tashin hankalin maganar da Yarima ke yi mini. Hawaye kuwa da ke fita a idanuwana, duk sun jiƙe gaban rigata. Jin har ya gama amma ban yi magana ba, shi yasa na ga ya ɗago kaina, sai na ga ya yi murmushi mai haɗe da takaici. "Yasmin,kada ki tayar da hankalinki, komai ki ka ga ya yi tsanani, to sauƙi na tare da shi." "Yanzu yaushe ya ce ka tashi?" "Gobe. Yau fa har wajen manyan shi muka je, amma cewa ya yi muddin Azahar ta yi gobe in har ban tashi ba, duk abin da ya faru da ni ni naja." "Mama ta sani?" "Eh, na aika mata da Waziri, sannan na yi mata waya, ta ce in tashi kada ya wulaƙanta ni a gaban jama'a. Yasmin na rasa abin da ke yi mini daɗi a rayuwata. Ni yanzu ya ya ma zan yi?" Cikin ƙarfin hali na tashi zaune na kalleshi sosai, wanda taimakon Innalillahi ya yi min shi tare da tunano abin da Allah (S.W.T) ke cewa cikin littafinsa mai tsarki: _Fa innama al'usrin usra."_ Ma'ana:--- _Lallai ne tare da tsananin nan da akwai wani sauƙi, lallai ne tare da tsananin nan da akwai wani sauƙi."_ saboda haka idan ka ƙare (ibada) sai ka kadu kana roƙon Allah, kuma zuwa ga ubangijinka ka yi ƙwaɗayi. "To yanzu ke wacce shawara ki ka ga ta dace da mu? Mu bar ƙasar ko? Saboda ni abin kunya ne...." "Sam ba ka tare da abin kunya har abada. A shawarata ka bi maganar Waziri, ka zauna Kaduna,kana jin me ke faruwa, sannan duk ranar da mahaifiyarka ta so ganinka za ta zo har inda ka ke. Yanzu tashi za kayi mu ƙwashe duk kayan mu tun yanzu,muna da motoci,a hannunmu kafin gobe a ƙwace. Kada mu gayawa yaranmu abin da ake ciki,mu ce masu tafiya ce ta kama mu, shekara ɗaya za mu je mu dawo kawai. Yanzu kuma ka tado direbobinmu su kai mana kayanmu Kaduna tun cikin daran nan, ina ga shi ne rufin asirinmu." "Haka za'ayi, tashi ki kirawo jakadiya ki gaya mata komai, ta taimaka miki haɗa kayanki da na Ammar. Kayan sawa kawai, sai kayan ƙwalliyarki, amma na jiki,sarƙoƙinki, daga su kada ki taɓa masu komai. Kafin ku gama nima na gama haɗa nawa." Na ce, "To." Na tashi na tafi, wanda har na kai ƙofa na ji ya kira sunana. Ina juyowa ya ce in jira ya rakani dare ya yi. Jakadiya na kuka tana haɗa kayanmu. Ban da Ammar da ke goye a bayanta,kaɗan-kaɗan kuwa ta ce, "Amma tare zamu tafi ko Gimbiya?" Sai dai in bata amsa da, "Sai abin da Yarima ya ce." Ƙarfe huɗu na dare mun gama komai, har direbobin sun tafi da kayanmu. Abin da ya rage a hannunmu aƙwatin duniyarmu da ƴan kayan da za mu sa da safe. Gari na wayewa tun wajen ƙarfe taƙwas gidanmu ya ruɗe da kukan sallama. Mun yi wannan dabarar ne ta barin gida tun safe domin mu samu a kai mu cikin motar gidan nan, tare da tawa motar da Waziri ya ba ni. Ƙarfe tara da rabi muna falon Daddyna,yana yi mana nasihohi tare da yi mana alƙawarin za su yi iya ƙoƙarinsu su binciko me ke faruwa. Sannan ya yi mana alƙawarin kai mana ziyara. Ya Kawo addu'o'i ya bamu, ya ce mu dage sosai a kan yin su, Allah zai bayyana ainihin gaskiyar abin da ke faruwa. Mamee ma haka ta yi mana ita da Aunty Salwa,sannan suka yi mana alƙawarin za su zo cikin sati na sama, domin ganin inda muka koma. Suka yi mana nasiha a kan mu zauna lafiya kada mu kuskura mu baiwa wasu fuska su shiga tsakaninmu, sannan kada mu yarda wannan abun da ya faru ya kawo mana raini a tsakaninmu. Haka dai muka rabu kamar in ce ba zan je ba, amma ganin yanda Yarima ya zama cikin ƙanƙanin lokaci yasa na ji ba zan iya ba. Sai da muka wuce garin Fambigowa cikin wani ɗan daji, sai muka hango mota jib baƙa da wata ruwan shanshan bale Honda Accord. Wasu mutane suna ɗaga mana hannu. Dalilin ganin mu kuwa direbanmu ne yake faɗa mana shi ne har ya jamu. Yarima ya ce ya sauke gilasan mu gani, sai da muka iso daidai su, sai na ji Yarima na cewa wai kamar motocin gidan su. Muna dawowa baya Mama na fitowa daga jib ɗin nan baƙa. Ana cewa tsakanin ɗa da iyaye sai Allah, na amince,yau Mama tamkar zata mayar da Yarima ciki. Tun kuwa da ta karɓi Ammar ba ta miƙo mana shi ba,yana saɓe a kafaɗarta, suka dinga hirarsu ta abin da ke faruwa. Ƙarshe dai Mama ta ce mu dawo motarta mu bayar a mayar wa da Sarki da tashi. A motar Mama muka isa har Kaduna unguwar Sultan Road,ko awa ɗaya ba mu yi ba da zuwa muka ji ana ta odar mota a get ɗin gidan. Ɗaya daga cikin direbobin da suka kawo mu ya je ya buɗe ana buɗewa muka ga Jeep Itama baƙa. Joseph wanda direban Daddyna ne, shi muka gani. Ya zo ya durƙusa ya gaishe da Mama da Yarima, sannan ya miƙawa Yarima makullin da ke hannunsa. "Dama Alhaji ne ya ce in biyo ku
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23