Chapter 2
Chapter 2
a garin ya nema masu admission cikin ikon Allah suka samu, xasu fara ne daga j.s2 sanda suka xo skul din yana tare da principal suna tattauna kan yaran... hankalin nusayba yayi xurfi daga inda take jiyo hayaniyar yara suna jumping jumping, i am jumping yarane qanana primary 1 tare da malamarsu.... abidi ya soma bayani wannan itace halima umar makama, sai dayar nusayba abubakar makama danakeso akula da ita sosai saboda rashi......yayi shiru sakamakon rashin ganinta gurin da yayi ya xare idanu yana kallon halimatu yace ina nusayba ne? da hannu ta nuna masa yaran dake harabar makarantar suna jumping.....can ya tsinkayota babba acikinsu tanayi tana dariya da sauri ya isa gurin ya janyota hade da ja mata kunne daya halima tace pls yaya ka kyaleta kada tayi kuka ya cikata yana fadin intayi kukan sai me? nusayba na riqe da kunnuwanta bakinta a tunxure..... a hakan aka nufi class dasu yarane xalla girmansu sai dai mabanbantane a yare da kamanin gu daya aka basu subiyu su xauna nusayba sai dariya take bakinta yaqi rufuwa saboda.kujerun datake xaune akai bata taba ganin irin suba halima sai bata rai take tana jin haushin nusayba yanda taga ana kallonsu sai a dauka su qauyawane, tace nusayba kibari kinga ana kallonki fa sai kowa yasan daga qauye kikaxo.... ai kuwa sai ta nutsu ta fara bata fuska tana dauke kai ita ala dole ba yar qauye bace........ [10:32PM, 2/5/2016] Pherty🎤👯: 2 weeks later A tare suka fito da halima sanye da uniform dinsu kowane da jikarsa a hannu, suka samesa xaune yana breakfast kowacce taja kujera ta xauna hade da gaidashi bai amsa ba ya xubawa nusayba ido yace jiya yaron da kika daka a skul kigayamin dalilin dukansa ta tunxure baki bayan takai arish a bakinta tace ai shine ya karyamin pencil nikuma na dakesa yayi shiru kamar baxaiyi magana ba yace daya karya maki pencil ba malamine a ajin, nan fa ba qauye bace dakike dukan yaran mutane ana kyaleki nan iyayensu baxasu barki ba kuma malamai xasu dakeki nima xan dakeki idan kika sake...... tayi shiru batare datayi magana ba tacigaba da cusa kwai a bakinta halimatu ta kwantar da kanta tace kayi haquri yaya baxata sake ba pls ka yafe mata kada kayi fushi da ita, ya dauke dubansa ga halimatu ya maida kallonsa ga.nusayba yace ko bakya jine ina magana kinmin shiru ta dago manyan idanuwanta ta xuba.mishi cikin shawaba batare da tayi mgn ba takai tea a bakinta cikin tsawa yace nusayba.... a raunane ta ajiye cup din ta tashi tana tunxure bakinta ni gsky uncle kadaina kirana nusayba ai ynxu niba yar qauye bace na canxa sunana nusee ita kuma halimatu taxama halimcy......ta dauki jakarta tafice. Sadteeyash💝 📝Hausa novel📚 [8/20, 5:55 PM] +234 812 673 9684: [11:25PM, 1/31/2016] Pherty🎤👯: ........ADON TAFIYA🚵🏻 Na Fertymerh xarah💝 1 to 10 Kyakkyawan saurayine dan kimamin shekara ashirin da shidda, tsaye a qofar jirgi yana shaqar iskar nigeria wanda rabonsa da qasar shekara biyu kenan. A hankali yake saukowa cike da qasaita ya gangaro xuwa farfajiyar airport din yana cike da farinciki da nishadi kyakkyawane sosai dogo mai kyan jiki yanada dogon hanci da manyan idanuwa,gashin kansa baqine sidik kwance sai shegi yake da tsantsi yanada mans pride kwance lub lub a fuskarsa yana faman sheqi wanda yayi matuqar fito da kyawun fuskarsa abinka da farin mutum taku yake irin na isassun ya'yan masu kudi masuji da mulki , yana sanye da farar shadda gexner mai kyau da tsada sunyi matuqar yi masa kyau kamar ba dannan qasar tamu ta nigeria ba Airport din cike take da mutane iri iri daban daban daga qasashe da dama malam sani ya qaraso da sauri fuskarsa da murmushi yake gaidasa da hannu yayi masa alamar amsawa kafin ya miqamasa trolley dake hannunsa driver ya karba da sauri kafin ya juya da sauri yabi bayansa. * sun dauki hanya sosai kafin ya juyo yana kallonsa yace malam sani ina xamuje ne amaimakon gida yace yallabai waiwaye adon tfy ka dade rabonka da bakura yau acan xamuje saboda su hajiya nacan, ynxuma daga can naxo daukarka da mamaki yake kallon driver yace lfy dai ko? yace ana bikine na aure, yayi shiru bai sake mgn ba ya maida kansa kan wayarsa hr suka iso garin bakura. can nesa da gidan sukayi parking sakamakon ganin yawan taron jamaa a bakin qofar gidan ya fito daga motar ya rufe dai dai lokacin dayaga mahaifinsa ya riqo Abbu yana rarrashinsa da alama kuka yake da sassarfa ya qarasa gurinda suke tsaye ya riqo hannun abbu yana kallonsa yana kallon mahaifinsa yace daddy meyasami abbu yake kuka, waya mutu ne? cikin kuka abbu yace dole nayi kuka irin wannan toxarcin da akamin, sai dana tara dubban jamaa saboda wannan auren amma ace anfasa [11:46PM, 1/31/2016] Pherty🎤👯: meyasa xasumin haka, meyasa basu sanardani tunda wuri kafin na tara mutanena ba, bnsan ynda xngayawa mutanena anfasa wannan auren ba😭 cike da mamaki idanunsa a bude yace abbu auren wa akeyi? kuma meye dalilinsu na fasawa? cikin kuka yace bansani ba, wlhy bn sani ba inaji dama sunyi niyar toxartani ne bayan tun farko su suka nemi aurenta daga garemu daddy ya dafa qafadarsa yace idan ina raye baxaka taba toxartaba , kai dan uwana ne najini, bayan kai banida wani dan uwa danake dashi a duniyarnan, ban rageka da komai daga cikin jin dadin rayuwar duniya ba duk da kana xaune a qauye ne, baxan so ka toxarta a duniya ba tabbas wannan auren baxaa fasa shiba sai an daura sa. Da waye? Abbu ya tambaya bayan ya tsaida hawayen idanunsa batare da yayi mgn ba yaja hannunsa suka bar wurin xuwa wajen daurin auren suka barshi anan tsaye ya jingina ga jikin motar yana kallon mutanen garin, wasu na sauri su halarci auren yayinda wasu k harkar gabansu kamar daga sama yaji ana fadin An daura auren Nusayba Abubakar MaKama da Abidina Umar Makama, laqadan ba'ajalan ba wayar dake hannunsa ta subulce daga garesa ta fadi, lokaci daya xuciyarsa na shiga harbawa baibi takan wayarba yayi cikin gida da sauri xuciyarsa a dagule yarinyar dayasani 14yrs xaace an aura masa, yarinya rigimamma irinta metasani akan rayuwar aure inbanda qurciya. yana shiga gidan ya tsaya cak sakamakon hada ido da yayi da ummansa nan da nan hawaye na taru a idajuwansa ganin haka yasa umman ta qaraso da sauri amma kafin ta iso, nusayba da akema wankan lalle ta qaraso da sauri cike da murnar ganinsa tayi tsalle ta fada jikinsa tana fadin oyoyo uncle! oyoyo uncle!!! da qarfi ya finciketa daga jikinsa kamar wnda aka xubawa garwashi a jiki, yana kallom jikinsa farar shaddarsa duk ta baci da jan lalle ya dago manyan idanuwansa da suka rine xuwa ja yana kallonta jiyake kamar ya rufeta da duka musamman ma data tsaya ta xuba mishi idanuwanta kamar xata cinyeshi........ Sadteeyash💝 📝Hausa novel📚 [8/20, 5:57 PM] +234 812 673 9684: [4:52PM, 2/2/2016] Pherty🎤👯: ..........ADON TAFIYA🚵🏻 Na fertymerh Xarah💝 11 to 15 Umma ta tsaida idanunta akansa tace mekakeyi haka abidi, meye laifinta aciki batare da yayi mgn ba ya juya ya fice kicibis sukayi karo da daddy ya fada jikinsa ya rungumesa hade da sakin kuka hakan yayi matuqar sanyaya jikin daddy
Table of Contents