Chapter 19
Chapter 19
sai kawai ta tabe bakinta tayi shigewarta dakin inna cike da jimamin rashin abbu😪 sanda suka dawo gida kai tsaye toilet ta nufa tayi wanka duk tana dauke da gajiya [2:42AM, 3/6/2016] pherty🎤👯: tana tsaye gaban madubi tana tufke gashin kanta abidina ya shigo yayi tsaye daga bakin qofa yana kallonta baisan adadin qaunar da yake mata ba, a hankali yake takawa qafarshi na nutsewa akan kilishin da aka malale dakin barcin da ita, har ya cimmata ya xagayeta da hannuwansa ya sanyata cikin qirjinsa ..wannan dare dai dai yake da darare dari agaresu, domin darene da akabiya bashin soyayya mai yawa aka baiwa so da qauna haqqinsa suke kuma fatan Allah yabasu xuria acikinsa. watansu biyu da dawowa bikin halimatu yataso gadan gadan, cikin ikon Allah aka soma bikin wannan karon hr merah sai dayo tattaki yaxo nigeria hr gidansu abidi tare da matarsa affiya. tunda aka soma bikin take laulayin ciki,abinka da abu a hannu kai tsaye dr.merah ya gano hakan, farinciki a gun abidina hr yafi na wancan karon.... [3:34PM, 3/9/2016] pherty🎤👯: WATA BIYU da gama bikin halimatu suka daga xuwa malaysia badan komai ba sai dan cikawa nusayba burinta na xama cikakkiyar likitar haqori A can ta qara haihuwa ta sami wani namijin mai sunan daddy suke kiransa Abba xaman su a qasar zee ta takurasu da yawa badan komaiba sai dan nadamar da tayi tadawo akan abidi ya maidata tana kuka take roqonsa sai hakan yabaiwa nusee tausayi ta shiga roqonsa akan ya haqura ya maidata fafur yaqi hrya nuja mata.bacin ransa ganin haka yasa taja bakinta tayi shiru..... suna garin halimatu ta haihu itama dai namijin ne, 150 to 155 A gurgujrle pls😒 Shekara kwana gamai yawan rai.... a yaune ake yaye daliban jami'ar dake malaysia....ciki hrda nusayba wadda ta karbi kwallinta mai daraja ta farko, cikin farinciki halimatu ta rungumeta dayake itama tana cikin yin nata karatun a pheonix tare da bilal. Da tsulelen cikinta [11:09AM, 3/11/2016] pherty🎤👯: ta iso nigeria, ga mamakinta abidina ya bata suprise ya buda mata NUSEE DENTAL HOSPITAL, cikin lokaci qanqani asibitin ya samu kafuwa sai son barka. 156 to 160 Sanye yake da shadda ruwan toka tayi matuqar fitarda kyawunsa babu hula a sumar kansa baqa wuluk kwance a dokin wuyansa kamar wani balarabe. ya qaraso dardumar datake xaune ya sunkuya yana yi mata magana cikin kunnenta, sassanyar numfashinsa a fuskarta,qamshin alban din bakinsa a hancinta, qamshi yake na musamman mai kwantarda xuciya barka da asuba sarauniyar xuciyata,inasonki da yawa,rayuwata seems to be difficult without you,my life is vile, idan.na rumtse idanuwana barci baya xuwa idan babu ke nusayba meyasa kika barni jiya? yaga bata kulasaba sai wani yamutsa fuska take kamar tana hadiyar yawu ko magana ta kasa yimasa sai nishibtake idanu a warwaje sai kawai ya dauketa da ita da tirtsetsen cikinta yai waje yasata a mota kana yaciro wayarsa yakira umma da daddy..... kokafin ya iso hrta fita hayyacinta dan ta galabaita sosai batasan inda kanta yake.ba, da gudu ya shiga asibitin ya turo nurse suka shiga da ita, naquda gadan gadan amma faya taqi fashewa kamar haihuwar farin ko miye dalili oho, abidi ya tsare yaqi fita daga dakin haihuwa ba korar da basu masa ba yaqi fita, duk ya gigice shima nothing worth comes easy, lokaci daya tayi wani nishi mai qarfi ta qanqameshi sai ga sankaceciyar budurwa ta fado,mintuna biyar tsakani sai ga hussainar ta fado....... murna gun abidi baa ko magana hr yaka sa rufe bakinsa, ya rungumeta cikin tsantsan qauna ya tabbata nusayba bata rageshi da komai ba xabin iyayensa yana alfahari dashi, nusayba taxama wata jigo ta rayuwarsa,ta xame masa ADON TAFIYA hayake ganin rabon samuntane yaxo dashi nigeria a wancan lokaci hr aka aura masa ita, a tunaninsa xee ce ADON TAFIYARSA malaysia ashe ba haka bane? ya rungumeta cikin wani irin so mai ratsa xuciya da gangar jiki hr yakejin bai iya controlling dinsa to such an extent dat lamarin yaxo wani limit beyond his capability to ignore,har yakejin baxai iya rayuwa idan babu taba, a cikin kunne ya rada mata kin xamemin ADON TAFIYA,ina alfahari dake inasonki nusayba........ murmushi kawai tayi cikin xafin ciwo ta shafi sumar kansa da hannunta daya.... idan kinsami sauqi xamuje church ne matar postor, sai ta tunxure baki alamar bataso, ya kyalkyace da dariya rungumota😂 Ranar suna yara sunci sunan Hayfah da Hayrah, suna kan anyishi sunan dangi ba irin abincin da baa ciba ba irin xanin da nusayba bata dauraba ba irin abin alherin da basu ganiba daga yan uwa da abokan arxiki iyayensu kayan jarirai sai a store aka loda su aka kulle, kudi kuwa a account dinta aka loda, atamfofi da lesuka akwati akwati jaka jaka haka aka dorasu daya kan daya. Nusayba da halimatu sai son barka sun cikawa maxajensu gida da kyawawan ya'ya maxa da mata abin alfahari ga iyayensu. 161 to 165 Masha Allah Laquwata illah billah! Nan na kawo qarshen labarin ADON TAFIYA🚴🏻 sai mun hadu a MATAR WAYE? My regards to masoyan littafaina wadanda nasani da wadan da bansaniba🙋🏻🙋🏻 ol greetings to Sadteeyesh💝 halamcy xarah dange baby aysher ru'aiya mmn boy kdeey maryam ramat nafee anka umboh mmn aleesha Ammin pherty sally princess ammi lurv hamxa mohd dama wadanda ban ambata ba ban manta dakuba, tare da ku room mate😜. Shin da gaske ne soyayya ba lallai ta xamo jigo wajen yin aure ba? wane irin aure ne yake dorewa, wane irine yafi nagarta tsakanin auren so da auren kauna.......duba littafin MATAR WAYE? special tnks to my caring an loving grup 📝Hausa novel 1&2📚 Muqaru da juna(serdy& aysher) mata masu duniya nisa'ul jannah. Sadteeyash na maku fatan alheri🙋🏻 📝Hausa novel📚 ; An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography
Table of Contents