Chapter 9
Chapter 9
yin magana, ya had'e bakinsa danashi yacigaba da kissing d'inta, lokaci guda ya tsinci kanshi cikin wani irin yanayi, itako auta 'kara narkewa tayi jikinsa, tana mashi shagwa6a shikuma sai kara matseta yake jikinsa kamar wani ze kwace mashi ita, Ji yayi anturo 'kofar da 'karfi, a firgice yakai dubansa ga 'kofar, Fadila yagani tsaye tana cika tana batsewa, shi kwata-kwata yama manta da ita, wani irin haushinta yaji dan ta yankemashi jin dad'insa, cikin d'aga murya yace, "Fadila meya shigo dake nan? Bata bashi amsa ba kuma bata motsa daga inda takeba, cike da jin haushin abinda tayimashi yace "get out, ki fita nace maki ganinan zuwa. Ita kuwa Auta ganin Fadila yasa ta'kara narkewa jikin khaleed, ta dauki hannuwanta duka biyu ta sa'kalosu a wuyanshi, tana mashi wani shu'umin kallo wanda ya'kara rikitar dashi, tace "haba my dear, meyasa ka shigo baka sallameta ba, kamata yayi ka sallameta kuyi sallama kafin ka shigo, kaga yanzu tazo muna cikin jin dad'in rayuwarmu ta mana cikas. Da gudu Fadila ta juya tabar d'akin dan jin hawaye na niyyar zubo mata saboda tsabar takaici, falo ta zauna tana share hawayen ba'kin ciki, a zuciyarta tana cewa *_Lallai yarinyar nan ni zata gwadama duniyanci, to wallahi sai nayi maganinta cikin gidannan saina nuna mata nafita iya duniyanci_* Nan suka isketa zaune suma suka zauna, Auta yanda take haka tafito, bako d'an kwali kanta, gashin kanta ya zubo kan kafad'unta, saboda haka hankalin khaleed yana kanta duk wani motsi nata sai ya had'iyi yawu, Da kanshi ya d'auko ledar ya d'auko plate ya juye dankwala-dankwalan kajine guda hudu, sai fresh milk daya ajiye masu gefe, da ruwan roba na swan. Nan ya Uamrcesu dasu zo su ci, Auta dama ta kwanta da 'yar guntuwar yunwarta saboda haka matsowa tayi taci me isarta, sannan ta kora da fresh milk tasha ruwa, shima khaleed yaci sosai, sannan yasha ruwa, Fadila kuwa kasa cin kome tayi saboda zuciyarta cunkushe take da ba'kin ciki. Bayan sun kammala ne khaleed yayi masu basiha akn zaman tare, sannan daga 'karshe, ya sanar dasu abubuwan dayake so da wanda bayso, dan su kiyaye. Sannan ya kallesu yace idan akwai me magana zata iyayi, Fadila tace "babu, Auta tace ni maganata kawai itace duk abinda kakeso shi nakeso wanda bakaso kuma shine baniso kaga ra'ayimu yazo d'aya kenan. Nan suka cigaba da fira sam-sama, yawancin firar ma tsakanin Auta ne da khaleed, Fadila duk takaici yahanata magana. Saida suka kai 'karfe sha biyu da rabi suna falo, lokacin khaleed yafara jin bacci dan dama akwai gajiya tattatare dashi, saboda haka yace to yakamata mu kwanta hakanan dan dare yayi saosai, Fadila tace "Eh gaskiya nima baccin nakeji, kazo mutafi dan nima gajiyarce a jikina, Fadila ta tashi tanufi d'aki tana lumshe ido alamar bacci, ganin Auta bata tankaba yasa khaleed ya tashi yabi bayan Fadila, Auta tayi saurin shan gabanshi tace "Ai d'akina zamuje ko, Fadila najin haka ta juyo tace "kamar ya d'akinki, amma kinsan ay na girmeki, kuma niyakamata ace anba girmana, Auta tayi murmushi tace "ay nan gidan aure ne ba maganar girma, saboda haka kazo muje kawai, nan rigima ta kaure tsakaninsu, wannan tace d'akinta za'a fara kwana wannan tace nata za'a fara kwana, khaleed yarasa yanda zeyi dasu kawai sai ya koma falon ya zauna kan kujera three seater ya zauna, suma suka biyoshi suka zauna, kowace da abinda take sa'kawa a zuciyarta. Shikuwa khaleed daya gaji da zama kwantawa yayi kan kujerar, tin yana kallonsu yana mamakin halinsu, har bacci yayi awon gaba dashi. Kiraye-kirayen sallar asuba ne ya tasheshi daga baccin dayake, zaune yagansu, suduka sunyi shiru, da Alama ba wacce ta runtsa cikinsu, tashi yayi yanufi d'akinsa yashiga toilet yayi wanka sannan yayo Alwala ya kabbara sallah. Sai lokacin sukuma kowace tanufi dakinta dan gabatar da tata sallar. Zee Elkaseem Mmn khady. [10/16, 7:55 PM] +234 816 616 9254: [04/08 6:34 pm] .: 🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊 *AUTAR HAJIYA* 💃🏻 🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊 ®NWA 👇🏻 _ZEE MMN KHADY_ 😘 *_Page_* 91-95 ✍🏽 Haka rayuwa tacigaba da kasancewa a gidan khaleed, yau kimanin kwana ukku kenan kullum kwanan zaune sukeyi a falo, dan Auta ta kafe ita a dole sai anfara kwana d'akinta, ita kuma Fadila tace Sam bata yardaba, hakan ke sawa khaleed yayi kwanciyarshi kamar yanda ya saba, wato falo kan kujera three siter sukuma haka zasu zauna su tasashi gaba sunata hararar junansu. Yauma kamar kullum, zaune suke babban falon gidan, da musalin 'karfe biyu da rabi na dare, shikuma khaleed yana kwance yanata sharar baccinsa hankalinsa kwance, yau ma atakaice haka sukayi kwanan zaune, asubah nayi ya wuce d'akinsa dan gabatar da sallah suma kowace tanufi d'akinta. Khaleed abin na damunsa yarasa yanda ze 6ulloma Al'amarin, saboda haka bayan yayi break fast ya shirya cikin 'kananan kaya, wandon jeans ba'ki da jar T-shirt yayi matu'kar yin kyau. 'Dakin Auta yashiga, zaune ya isketa tsakiyar falonta, kan carpet hannunta ri'ke da waya tana game, da sallama ya shiga d'akin bayan ta amsa ya'karso inda take ya zauna kusa da ita, ta d'ago da manyan idanunta ta kalleshi tace "barka da kwana, yace "ku zanyima barka kuda ke kwanan zaune, Kafin tayi magana yaci gaba da cewa, yanzu Zainab rayuwar da kuka za6ar mana agidannan kuna ganin ya dace, ace ku duka ba wacce zatayima 'yar'uwarta hakuri, Amma Auta kinga kece 'karama yakamata kiyi hakuri nafara kwana d'akin fad'ila duka fa kwana biyu ne zan dawo d'akinki, haba Auta bakison kwanciyar hankalina ne? Wani irin kuka ta fashe dashi, cike da mamaki khaleed ke kallonta, cikin maganar dayayima Auta miye abin kuka. Kuka tacigaba dayi tana cewa "shikenan khaleed ka nunamin kafi son Fadila akaina, kaje ka kwana d'akinta d'in wallahi nikuma idan har ka kwana d'akinta ranar zan bar gidannan, kuma idan natafi kada kayi tinanin gidanmu zanje, a'a zan tafi inda ba'a sanniba inda bansan kowaba, incigaba da rayuwata acan. "Idan abin gaskiyane it's kace ta hakura ta barmin mana. Haka khaleed yayi rarrashin duniyar nan amma Auta ta kafe akan sai dai ya fara kwana d'akinta, haka khaleed yabar d'akin Auta yana mamakin rigima irin tata. A d'akin Fadila ma haka yasha daga da ita yana rarrashinta akan ta ha'kura ya fara kwana d'akin Auta, amma tace sam ita bata San wannan ba, aiko abin ya 6ata ransa nan ya balbaleta da fad'a ta inda yake shiga ba nan yake fitaba, yace "shikenan kuyi duk abinda kuka iya, yanzu ke Fadila bazakiyi hankali ki ri'ke girmankiba ki kawo 'karshen wannan kwanan zaunen da kukeyi, Cikin masifa itama take magana "Wallahi bazan yardaba, yanda ita bakace ta hakura ta barmin ba nima wallahi bazan barmataba, ai ba fina sonka tayiba. Cikin fushi khaleed yafita, a harabar gidan yanufi gurin ajiye motoci ya hau motarsa ya kunna, me gadi ya bud'e mashi get yadau hanya, Gidan abokinshi ya wuce Ahmad, a ranar can ya wuni be baro gidan ba sai bayan magrib, daga nan kuma gidansu ya wuce be dawo gidaba sai 'karfe tara da rabi na dare. Zee Elkaseem Mmn khady [04/08 8:04 pm] .: 🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊 *AUTAR HAJIYA* 💃🏻 🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊 ®NWA 👇🏻 _ZEE MMN KHADY_ 😘 _*Page*_ 96-100 ✍🏽 Da sallama ya shigo falon, Abin mamaki yau bega kowa a falon ba kamar yanda yasaba
Table of Contents