Chapter 1
Chapter 1
[10/16, 7:54 PM] +234 816 616 9254: [29/07 3:49 am] .: 🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊 *AUTAR HAJIYA* 💃🏻 🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊 ®NWA 👇🏻 _ZEE MMN KHADY_ 😘 _Page_ 1-5 _Amincin Allah ya tabbata ga duk wanda ze karanta wannan littafi nawa, duka da ma wanda besamu damar karantawaba_. 👏🏻👏🏻👏🏻 ✍🏽 Kwance take kan d'an madai-daicin gadon mahaifiyarta, hannunta ri'ke da waya, kirar tecno H³ wani game take me matukar sanyata nishad'i, Ta tattara hankalinta duka ya koma kan wayar. Muryar Hajiya ta tsinkayo tana kwalla mata kira, da sauri tasanya pause a game d'in domin zuwa kiran mahaifiyar ta. "Hajiya gani, tafad'a bayan ta d'an rissina gabanta, Alamar girmamawa, matar da takira da Ahjiya ta d'ago ta kalleta, tace "ki shirya inaso in ayke ki yanzu, tace "ina? Tace "kije ki shirya mana koma inane ay zakiji. 'Daki tanufa ta cire kayan jikinta, tayi d'aurin kirji, sannan, tafito ta cika bokiti da ruwa ta nufi toilet. Bayan ta she'ka wanka, tafito tanufi d'akin dai daya kasance nan ne na mahaifiyarta Wanda da Alama itama nan take, kwandon kayan shafarta ta d'auko ta ajiye gabanta, Wanda babu abinda babu aciki, tafara d'and'asa kwalliya, takai kimanin awa d'aya tana kwalliya, bayan tagama ne ta tashi' tanufi wadrope ta dauko wata green d'in atamfa, me zanen ganye golden, nd yellow, wacce akayima ado da yellow Codeless d'inkin zamani riga da zani pieces. Bayan tasaka kayan, sun kuma kar6i jikinta, dan ba 'karamin kyau saukayimata ba, sun fiddo da duk wata kya'k'kyawar halitta da Allah yabata. Fara ce, Amma ba irin tass d'innan ba, farinta dai-dai misali, tanada manyan idanu Wanda akoda yaushe idan ta kalleka, sai kayi tinanin kashe maka su takeyi, amma ba haka bane haka yanayin kallonta yake, ga dogon hanci Wanda ya 'kara fito da anaifin 'kyawunta, bakinta d'an karami, hakoranta farare tas, sai wushiryar data 'kara fito da kyawun su, gefen kumatunta ko magana take yana lotsawa, barantana kuma idan tayi dariya, wannan dimple ba karamin 'kara fiddo da 'kyawunta yake ba. Bayan tagama shirinta tsaf, ta dauko hijab d'inta, kalar golden, ta Sanya tiare ta dauko ta feshe jikinta dashi, sannan ta d'auko plat shoes shima kalar golden, ta Sanya, tanada tsayi shiyasa bata damu da takalmi me tudu ba. Fitowa tayi tsakar gida, inda mahaifiyarta ke jiranta, tace "gani Hajiya. Hajiya tace "yauwa dama gidan Maman Ummi zakije, kicemata ya maganar adashi, yanaji shiru, ko har yanzu, ba'a gama had'a kud'in ba?. Kuma kice ina gaisheta, sannan ta d'auko naira Hamsin tabata, Anshi ki hau napep, ta kar6a sannan tafice Daga gidan, Hajiya namata fatan zuwa lafiya da kuma dawowa lafiya. Taje gidan ayken harta, Isar da sa'kon takuwa yi sa'a dan angama had'a kudin saboda haka aka bata, dama kwasar adashine na Hajiya. Kasancewar hajiyar kud'in zuwa kawai tabata, can kuma gidan dataje, Mmn Ummi tabata, kud'in napep d'in Amma ta'ki kar6a, saboda haka a 'kafa ta tafi, tana tafiya tana zancen zuci, tayi matu'kar danasanin tahowa a 'kafa domin yanda ta lura da duk Inda ta gifta maza ke binta da ido. Azuciyarta tace "Allah ya taimakeni hijab na Sanya, da nabani. ✍🏽Zee Elkasem Mmn khady. [29/07 4:33 am] .: 🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊 *AUTAR HAJIYA* 💃🏻 🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊 ®NWA 👇🏻 _ZEE MMN KHADY_ 😘 _Page_ 6-10 ✍🏽 Da sallama tashigo gidan, kitchen ta iske Hajiya, tana faman dafa masu abincin rana, Hajiya tafito Daga kitchen d'in tana mata sannu da dawowa. Ta fiddo da kud'in ta mi'ka mata tace "gashi kuma Mmn Ummi tace tana gaisheki, kuma tace "dan Allah kiyi hakuri wallahi mutanen ne sai Ahankali, Hajiya ta kar6i kud'in cikin farin ciki, ta kirga su dubu tamanin dai-dai, sannan ta kalli Autar Hajiya tace, "to Auta ga kud'in adashi sun samu yanzu ki gaya mani dami-dami kike bu'kata, kinga gobe idan nafita gurin ayki sai in sawo maki. Autar Hajiya tayi murmushi, taji dad'i har cikin ranta, game da yanda iyayenta suke nuna tsantsar so da Kauna da kuma kulawa a gareta, dan ita iya saninta tinda ta taso gidan, bata ta6a neman wani Abu tarasa ba, duk da iyayenta ba masu kud'i bane Amma sunada rufin asiri, domin mahifinta yana ayki, mahifiyarta ma tana ayki. Da misalin 'karfe hud'u na yamma, Hajiya suna zaune tsakar gida itada autarta suna shan iska, kasancewar yau Alhamis ba'a zuwa islamiyya. wani yaro yayi sallama, bayan an amsa Mashi, ya gaida Hajiya, sannan yace "wai ance ana sallama da Zainab a waje, Hajiya tace je kace waye, yaron yaje ya tambayo sannan ya dawo yace, "wai yace ba'ko ne, dan Allah ta taimaka tafito, Hajiya tace jeka kace tana zuwa. Tayi saurin tashi daga kwancen datake, tace dan Allah Hajiya kice baninan, ni wallahi banison wannan kiran, nifa ban ma San ko wayeba, Hajiya tace "to kifita mana sai kiga kowaye, haba zainabu na wulkanci bashida kyau, kifita ko gaisawa kuyi sai ki dawo ba sai kin dad'e ba. Hijab dinta ta Zara, ta Sanya, wacce tsawonta ya kai mata iya gwiwa, sannan ta fita. Jingine yake jikin motarsa, baki ne amma ba kirin ba, yanda 'kya'k'kyawar fuska, yanada saje Wanda ya'ara fito da kyawunsa, gajere ne dan baza'a ta6a sashi sahun masu tsayi ba, zai kai kimanin shekara talatin da takwas a duniya. Tinda ta fito ya zuba mata, idanu yana kallonta, harta 'karaso, ta gaidashi, ya amsa cikin fara'a, Daga nan bata 'kara magana ba, sai shi yacigaba da magana. "Wato Zainab, hausawa sunce maso tsuntsu shike binsa da jifa, a gaskiya tinda naganki naji kin kwanta min arai, kuma ba kome ya'kara karkatar da Hankalina garekiba illah kamun kanki, da kuma kaywun surar da Allah yayi maki, nidai tafe nake da 'ko'kon barata, idan kin Amice aurenki zanyi dan ba maganar wasa ta kawoni anan ba. "Au sorry nacikaki da saurutu ban ko fad'a maki sunana ba, sunana "Adam kuma ni d'an nan cikin garin katsina ne, ina zaune a Unguwar Al'kali da iyalina, inada mata d'aya da yara ukku, da fatan zaki kar6i soyayya ta. Kafin tayi wata magana ta hango babanta tafe kan mashin d'insa saboda haka bata tsaya bashi amsaba ta shige gida. Nan Baban nata ya Tarar da Adam kofar gida, bayan sun gaisa, yayi Mashi yan tambayoyi. Zee Elkaseem Mmn khady. [29/07 9:30 am] .: 🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊 *AUTAR HAJIYA* 💃🏻 🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊 ®NWA 👇🏻 _ZEE MMN KHADY_ 😘 _Page_ 11-15 ✍🏽 Koda ta shigo gidan d'aki ta wuce, ta d'auki wayarta tacigaba da danne-danne, azahiri idan ka ganta wayar take dannawa, Amma zuciyarta cunkushe take da tinani barkatai. Itako a tsarinta babu Auren me mata, saboda ita mace ce me tsananin kishi, yaushe zata yarda ta auri namiji me aure, Amma wannan mutumin yama raina mata yawo, to wallahi, da matar shi hada 'ya'ya ukku kuma sannan yace yana so ya aureta, ya Allah tsareta da aurensa, wani irin mugun hauhinsa taji ya rufeta, itako da beda mata da zata iya daurewa ta Auresa, kidan saboda yanda babanta ya matsa akan yanaso tayi aure. Da sallama mahaifin nata ya shigo, Hajiya dake zaune tsakar gida ce ta Amsa sallamar, sannan tayima me gidan nata sannu da zuwa, bayan ya amsa da "yauwa" d'akinsa ya wuce, Hajiya tanufi gurin ajiye ruwa tacika boket da ruwa takai toilet, sannan ta iske me gidan nata d'akinsa tace "Alhj ga ruwan wanka
Table of Contents