Chapter 12
Chapter 12
dan kuwa Auta ba daga baya ba gurin iya girki, ita kanta Fadila ta jinjina ma Auta a zuciyarta, dan ko a hotel abinci baze wuce wannan dad'i ba. Bayan sun gama ne khaleed yafara magana "Amma gaskiya naji dad'in yanda kuka dawo yanzu, kungane wannan rigimar ba abinyi bace, saboda haka inaso inyi amfani da wannan dama inyimaku nasiha akan dan Allah ku had'e kawunanku ku zauna lafiya, ba cuta ba cutarwa, domin zamanku lafiya shine kwanciyar hankalina. Sannan ya kalli Fadila, yace "kinga Fadila jiya na kwana d'akin Auta, to gobema zan kwana d'akinta kinga kwana biyu kenan, daga lokacin kuma zan dawo d'akinki inyi kwana biyu. Suduka sunyi shiru suna saurarensa, kowace da abinda take kitsawa a ranta. Auta tace "to wane lokaci kake ganin ya dace ari'ka kar6ar aykin? Khleed yace "Ku yakamata ku fidda, sai lokacin Fadila tayi magana tace kamar da 'karfe biyar da rabi na yamma, ta kallesu tace hakan yayi koh,? Khaleed yace "yayi. Haka dai suka d'an ta6a fira, wacce yawancinta tsakanin khaleed ne da Fadila, dan Auta ita haushi ke hanata magana, dan ita kome Fadila zatayi bala'in haushi yake bata, wani irin mugun kishin khaleed ne ke kamata duk lokacin dataga yana kula Fadila. A haka aka cikama Auta kwananta d'aya batare da wani tashin hankali ba, dan Fadila ta hakura, kuma kullum girkin Autar takeci, dan kuwa tare suke cin abinci su duka, •••••••••••••••••••••••••••••••••••• Yau yakama ranar da Fadila ta kar6i kwana, saboda haka itace tayi masu abincin dare, Ta had'a kome ta jera kan dining, da misalin 'karfe takwas na dare suka zauna cin abinci, Fadilar da kanta ta zuba ma Auta bayan ta zuba ma khaleed ta tura mashi gabanshi. Auta cike da jin haushi ta debi abincin takai bakinta, bata San lokacin da tasaki wani tattausan murmushi ba dan jin testing d'in abincin, a zuciyarta tace " ~_Salmanu!...... kada inga salame idan haka take_~" Dan jin abincin tayi ba wani testing ko kad'an, aiko take wani irin farin ciki ya mamaye zuciyarta, data tuno cikin kwana biyunan yanda khaleed ke buga santi idan yana cin abincinta, koda yaushe yana yaba mata kan iya girki. Khaleed kuwa koda ya d'ebi cokali d'aya yakai bakinsa, yaji abin ba'a magana, daurewa yayi ya had'iye na bakinsa, haka dai ya daure yaci gaba da ci, itama Auta dataga haka saita ri'ka tutturawa tanaci tana jin dad'i aranta, ita kanta Fadilar daurewa kawai take tanaci dan tasan ba yanda za'ayi tayi girki kuma ta'ki ci' sai afara zargin kota tasarma rashin gaskiyane, amma ko ita kanta tasan abincin beyi dad'iba, saboda haka ta dage tayita d'ibar girki. Bayan sun kammala sun d'an ta6a fira har kusan 'karfe sha d'aya da rabi Auta nata jan khaleed da surutu dan kada su tafi su kwanta, shikuwa ya biye mata dan bemasan lokaci yayi nisa haka ba. Saida Fadila tagaji, ga bacci tanaji, tanata hamma sannan ta kalli khaleed tace "my man bacci nakeji kazo muje kaga dare yayi har sha d'aya, sai lokacin ya duba agogon wayarsa yaga k'arfe sha d'aya da minti arba'in da tara, saboda haka khaleed yatashi sukayima Auta sallama suka wuce d'aki. Itama nata d'akin tanufa, ta cire kayan jikinta ta sanya wata doguwar riga ta bacci ta haye gado da niyyar yin bacci, amma ina kasawa tayi lokacin data tuno yanzufa khaleed yana d'akin wata ba itaba, kuma ze nuna mata soyayya irin yanda ya nuna mata. Zunbur tayi ta tashi kamar wacce aka tsikara, takama zagayen d'akin zuciyarta nata tafarfasa, falo ta dawo ta zauna ta sa hunnu biyu ta buga uban tagumi, zuwa can taga zaman beyi ta tashi ta dinga safa da marwa tsakanin falo da d'akinta, daga 'karshe da takaicin ya ciyota batasan lokacin data fashe da wani irin kuka ba, tafad'a kan gado tacigba dayi, har misalin 'karfe ukku da rabi na dare Auta na aykin kuka, daga 'karshe dai bacci 6arawo yayi awon gaba da ita. Zee Elkaseem Mmn khady [10/16, 7:55 PM] +234 816 616 9254: [10/08 11:29 pm] .: 🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊 *AUTAR HAJIYA* 💃🏻 🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊 ®NWA 👇🏻 _ZEE MMN KHADY_ 😘 ```Page```121-125 ✍🏽 Haka Auta tacika kwanakinta biyu kullum zata tsaya ta kwantar da hankalinta ta tsara girki tun kafin ta kai kan dining saita d'and'ana taji testing d'insa saita tabbatar da lafiya lao sannan take ajiyewa, amma abin mamaki sai sun zauna cin abincin suji gishiri za'ka'ka, Abin yana matukar damun Auta amma ba yanda zatayi, dan batada hujjar kare kanta akan cewa ba ita ta zuba gishiri haka ba, ba abinda ya kara d'aure mata kai sai lokacin da tayi girki ranar ko gishiri bata zuba ba dan gudun kada yayi yawa, amma babban abin mamaki shine suna fara ci sukaji gishiri zau' abin ba dad'in ji. **************************** Fadila ce cikin shigar 'kananan kaya riga da wando sun matseta sosai, wasu had'ad'un kuloli ne take d'aukowa daga kitchen tana jerawa kan dining, gefe kuma lemun ```5alive``` ne sai ruwan swan, abin gwanin ban sha'awa. Da misalin 'karfe biyu da rabi khaleed ya dawo gida, Fadila ta tarbeshi cike da murna, Auta kuwa tana zaune gefe, cikin sanyin jiki tace "Sannu da zuwa, ciki-ciki ya amsa, sannan ya wuce d'akinsa, Dan yanzu Auta tariga tagama sure mashi, kwata-kwata tagama 6ata ranshi, ace kullum mutum baze iya tsayawa yayi Abu cikin tsariba, sai ace yau ayi girki acika gishiri, kuma gobe ma haka za'ayishi, babban abin takaici sai kaji gishiri cikin zo6o ko kunun aya, wnnan ay rainin wayo ne. Wani 'karamin tsaki yaja "mtsw, sannan ya wuce d'akinsa, Fadila ta bishi tana wani karairaya, koda takai bakin 'kofar d'akin saita juyo ta kalli Auta dake zaune kan kujera abin duniya duk ya dameta, tayi wani shu'umin murmushi sannan tashige d'akin tare da canja salon tafiya tana wani juya mazaunai. Fadilar ce ta taimaka mashi ya cire kayan jikinsa yayi wanka, da kanta taje cikin kayanshi ta dauko mashi kaya marassa nauyi ya Sanya, sannan suka fito falo, dining suka sauna dan cin abinci Auta kuwa ba'kin ciki ya gama cika mata zuciya, bayan shigewarsu d'akinta tanufa tafad'a kan gado ta rushe da wani irin kuka, sai da tayi me isarta sannan tafad'a toilet ta she'ka wanka, bayan tafito ta shafe jikinta da cream me dadin kamshi da gyara jiki sannan ta shafa powder ta dauko man le6e ta shafa, wadrope tanufa ta d'auko wata doguwar riga ba'ka me adon fararen duwatsu daga gabanta ta Sanya, sannan tasa d'an 'karamin gyalen rigar ta rufe kanta dashi, lokaci guda ta fito balarabiya Sak, dan ba 'karamin kyau Auta tayiba. Kan dining ta iske Fadila da khaleed suna jiran fitowarta, guri ta samu ta zauna duk da zuciyarta na cunkushe da ba'kin ciki da kuma jin haushin Fadila amma ko kad'an bata yadda khaleed da fadilar suka fahimci halin datake ciki ba. Bayan Fadila ta zuba abincin ta ajiyema Kowa nashi gabanshi, jalouf d'in taliyace wacce taji kifi, cike da fargaba Auta ta ebi taliyar takai bakinta, ```Ya salam```...... Auta ta fad'a tare dayin hanyar toilet da gudu ta rina'ka kwara amai, saida ta amayo duk abinda ke cikinta, khaleed kuwa binta yayi daga baya yana mata sannu, bayan ta gama ta wanke bakinta khaleed yakamo hannunta suka dawo falon, kan kujera
Table of Contents