Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 15

Chapter 15

Autar Hajiya Book 1 Complete Hausa Novel 1,194 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

mashi kanta datayi. Wani irin kukan ba'kin ciki Fadeela ta fashe dashi, dan duk abinda sukeyi gabanta sukeyi, kallonsu kawai take takasa magana saura kad'an zuciyarta ta buga, wannan kukan dayazo mata shine samun sau'kin takaici da ba'ki cikin da Auta ta 'kunzuga mata. Da sauri ta tashi tanufi d'akinta, minti biyar batayiba da Shiga, sai gata ta fito, sanye da gyale, da takalmi a 'kafarta, sai yar poss a hannunta, Sai lokacin ta iske khaleed ya sake Auta, amma suna zaune kusa da juna kowanensu yana cike da sha'awar d'an'uwasa saboda wasanni da sukayi, abin ba'a cewa kome 🙈. Bata ko kallesuba tanufi 'kofar fita daga falon, fuuu kamar zata tashi sama, khaleed ne yayi saurin tashi yabi bayanta yana tambayarta "Fadila ina zaki? Bata ko saurareshiba tayi gaba abinta. Tana fita get d'in gidan takoyi sa'a wani me napep ya ajiye wata mata wani gida kusa dasu, nan tafad'a mashi inda ze kaita, tashiga. Khaleed na fitowa napep d'in na barin 'kofar gidan, "ya salamm ya furta, can kuma sai yayi wani guntun tsaki yace ```"kinyi laifi kuma kifi wanda kikayiyamawa zuciya``` Gida ya koma ya iske Auta zaune inda yabarta, nan take tambayarsa, "Lafiya kuwa saboda me Fadila ta tafi, be bata amsa ba sai rungumota dayayi jikinsa yafara shafata ta ko'ina, Auta batayi 'ko'karin hanashiba saida taga yana neman wuce gona da iri, sannan tayi saurin tureshi, ta tashi zaune, nan khaleed ya marairaice mata yayi kalar ban tausayi yace (please Auta help me) ki taimakeni nariga na shiga wani yanayi, cike da tsoro Auta ta kalleshi taga yanda idanunshi suka kad'a sukayi ja, Lokaci guda ta langa6e tana bashi ha'kuri "kayi ha'kuri my dear kaga ba aykina bane, yanzu idan nabaka kaina mun shiga ha'k'kin Fadila, kayi hakuri kada kasa kanka cikin maza masu rashin Adalci tsakanin matayensu. Haka Auta ta rarrasheshi har ya hakura, nan ya wuce dakinsa, ya shiga toilet yasake watsa ruwa sannan ya dawo yabi lafiyar gado. Itako Auta yana shiga d'akinsa, itama nata d'akin tanufa tana ahiga ta she'ke da dariya tace ~_(Fadila dani kike magana)_~ Zee Elkaseem Mmn khady [10/16, 7:55 PM] ‪+234 816 616 9254‬: [13/08 7:03 am] .: 🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊 *AUTAR HAJIYA* 💃🏻 🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊 ®NWA 👇🏻 _ZEE MMN KHADY_ 😘 ```Page``` 141-145 ✍🏽 Da sallama Fadila ta shiga gidan, falo ta tarar da momynta tana zaune hannunta rike da (newspaper) jarida tana dubawa, Cikin fara'a ta kalli Fadila ta amsa mata sallama, dai-dai lokacin Fadila ta tsinci kanta da tinanin yanzu idan momynta ta tambayeta meya kawota me zatace, Muryar momynta ta katse mata tinanin datake, "Ina me gidan naki na ganki ke kad'ai? Fadila tayi saurin dawowa daga tinanin datake ta kalli momynta tayi murmushi, dan bataso ta gane tana tattare da wata damuwa, tace "shine ya saukeni yana sauri ne yanada meeting a office d'insu shine ya wuce, yace idan yadawo d'aukata ze shigo, Momy tace "owk" Sukayi shiru na 'yan wasu mintittika, Fadila kuwa tunani tashiga yi, a zuciyarta tana cewa: *_Yanzu wannan 'karyar danayi idan khaleed ya'ki biyoni ya zanyi, kokuma idan yazo yace bada izininshi na fito ba , Allah dai yasa ya rufa min asiri_* "Fadila lafiya naga kinyi shiru kamar kina tunanin wani abu, kodai akwai abinda ke damunki ne? Da sauri Fadila ta washe ta tashi tana murmushi tace "lah ba kome Momy, tanufi hanyar kitchen tana fad'in me kuka dafa wlh yunwa nakeji, Bata jira amsar Momy ba tashige kitchen tazubo tuwon shinkafa da miyar d'anyar ku6ewa, sannan ta d'auko lemu a pridge ta dawo falo ta zauna tafara ci, Momy kuwa kallonta kawai take azuciyarta tace *Anya Fadila* "Fadila yanaga kinatacin abinci haka kamar wacce ta kwana bataciba? Fadila tayi saurin kai dubanta ga momynta tace " banci abinciba na fito saboda ina d'okin ganinki Momy, tafad'a tana murmushi, Itama Momyn murmushin kawai tayimata tacigaba da duba jaridar dake hannunta. Har misalin 'karfe shidda da rabi na yamma khaleed bezo d'aukar fadila ba, momy ta kalleta tace "khaleed shuru kodai ya manta dake ne, Fadila taji gabanta yafad'i tace "a'a Momy yana zuwa, inaga har yanzu begama abinda yake bane. Fadila tashiga damuwa hankalinta yafara tashi ganin har angama sallar magrib amma khaleed bezo d'aukar taba, gashi bataso dadynta ya tarar da ita kuma tasan ana gama sallar isha'i ze dawon gidan. Karar tsayuwar motarahi ce ta dawo da ita daga dogon tinanin datakeyi, Da sallama ya shigo gidan, Momy ta amsa tare da yimashi sannu da zuwa, falo akayimashi masauki, bayan sun gaisa ya kalli fadila wacce dama on ready tagama shirin tafiya zuwanshi kawai take jira, yace "ki taso muje ko kinga dare yafara, Wani sanyi fadila taji cikin zuciyarta, da khaleed be fad'i dalilin tahowarta ba. Haka suka bar gidan, Fadila, nata godema Allah daya rufa mata asiri, dan yau da Momy tasan da yanda ta taho gida da ranta idan yayi dubu sai ya 6aci. Haka suka shiga mota suka d'au hanya, tinda suka fara tafiya ba Wanda yacema d'an uwansa kome har suka isa gida. Koda fadila tafito daga motar kasa shiga tayi gidan saida tajira khaleed sannan suka shiga tare, Falo suka iske Auta zaune kan kujera, sanye take da wata riga me hannun bes da wani d'an 'karamin siket iya gwiwa, hannunta ri'ke da remote tana canja tasha zuwa *ZEE CINEMA* dayake ita meson kallon Indian film ce, kanta babu ko d'an kwali gashin nan ya zubo 'kan kafad'unta, cike da murna ta taso ta rugume khaleed, "sannu da zuwa mijina, murmushi yayi tare da bata kiss a kumatu yace "yauwa matata. Fadila kuwa tana tsaye tana kallon ikon Allah, sai lokacin Auta ta kalleta tace "Andawo lafiya, Bata amsa mataba illah wata uwar harara data buga mata sannan taja dogon tsaki "mtswwwww ta wuce d'akinta. Khaleed ma d'akinsa ya wuce, Auta kuwa dariya tayi, dan ganin tagama 'kule fadila, ta koma ta zauna taci gaba da kallonta, canja tasha tayi zuwa *STmusic* aiko ta iske an sanyo wa'kar *justing viiver* cikin wa'karshi me taken _(Love me love, kiss me kiss me)_ dama tana masifar son wa'kar duk ta iya ta, saboda haka taciga da bi, tana 'yar rawa daga inda take zaune. Lokacin Fadila tafito daga d'akinta tanufi kitchen, ta kai dubanta ga Auta wacce tayi kamar batasan da mutum a falon ba, wani 'kululun ba'kin ciki ya tsaya mata tayi tsaki Mtsww "Aykin banza tafad'a sannan tawuce kitchen din. Zee Elkaseem Mmn Khady [13/08 8:10 am] .: [13/08 7:40 am] .: 🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊 *AUTAR HAJIYA* 💃🏻 🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊 ®NWA 👇🏻 _ZEE MMN KHADY_ 😘 ```Page``` 146-150 ✍🏽 Washe gari, Fadila tagama had'a musu break fast, kunun gyada ne ta she'ka musu, yayi gwanin kyau, dan ta masifar iya kunun gyad'a dan duk cikin abinda take girkawa a gidan shi kad'ai ne takeyi susha cikin kwanciyar hankali, kuma wani lokaci har khaleed ya yaba. Yauma shine ta she'ka masu, tare da soya masu dankakali da kwai, bayan tagama ta jera kome kan dinning ta koma d'aki dan yin wanka. Auta kuwa dayake ba itabace meyin girkin tuni ta dad'e da yin wankanta ta shirya cikin Riga da siket na material tayi kyau sosai. Tana jin shigewar Fadila d'aki, sai tafito tana tafiya ahankali, sad'af-sad'af yanda ba Wanda ze iya jiyo 'karar takun

Table of Contents

Chapters

20 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});