Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 17

Chapter 17

Autar Hajiya Book 1 Complete Hausa Novel 1,197 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

Ta dade nan tsaye kafin ta yanke shawarar ta wuce d'akinta da gudu kada tabari Fadila ta kamata. Haka kuwa akayi da gudu, tashigo falon da niyyar ta wuce d'akinta ta kulle kanta, bazata fitoba sai khaleed ya dawo, amma ina, tariga ta makara, dan ko kusa da 'kofar d'akin bata kaiba Fadila ta dam'kota. Zee Elkaseem Mmn khady [13/08 6:54 pm] .: 🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊 *AUTAR HAJIYA* 💃🏻 🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊 ®NWA 👇🏻 _ZEE MMN KHADY_ 😘 ```Page``` 156-160 ✍🏽 Auta tagama tsorata da yanda Fadila ta dam'kota, tanayimata wani mugun kallo, Lokaci guda 'yan cikinta suka motsa saboda tsoro, harta hangoma kanta irin dukan dazatci gurin Fadila. Amma a fili saita nuna dakewa, ta kalli Fadila Alamar ba tsoro ko 'kadan a tartare da ita, tace "dallah malama sakeni, kin wani kamani kin ri'ke ko nayimaki satane, tafad'a tana wani hararta. Wani guntun murmushi fadila tayi mai d'auke da takaici, ta kama hannun Auta ta kaita kan kujera ta zaunar da ita, sannan itama ta zauna kusa da ita, ta kalleta tace "Yanzu Auta abinda kakayimani kin kyauta, ki duba kiga yanda kika shiga tsakanina da mijina, menayimaki dazaki saka mani da wannan, Wani sanyi Auta taji cikin zuciyarta, dataga Fadila bata nemeta da fad'aba, danko da dafarko tafara tinanin yanda zasu kwashe, amma sai taga Alamun Fadila na Neman sulhu ne. Har cikin ranta taji tausayin Fadila, yakamata, dan ita dama tincan mutum ce mai matu'kar tausayi. Cikin sanyin murya Auta tafara magana, "ni dama ba da niyyar wani Abu nayiba, naga kin shigone kamar zaki dakeni, nikuma kinga dole in nemarma kaina mafita. Fadila tayi wata nannauyar ajiyar zuciya, cikin Zuciyarta tace ```{"Da kinsan abinda nazo dashi lokacin da baki sakamin da abinda kikayimaniba}``` "Koda kikaga na shigo ba da niyyar tashin hakali Nazo ba, nazo ne kawai muyi magana. Auta tace "To ayni bansaniba, da saikiyimin sallama kafin ki shigo, tunda naga kin shigo ba sallama sai inyi tunanin ba arzi'ki yakawokiba, "Amma kiyi hakuri, tafad'a tare da juyar da fuskarta gefe, tana wani turo baki. Fadila ta 'kara zama tare da matsowa kusa da Auta, Auta tad'an matsa, dan ita har yanzu da d'an sauran tsoro tattare da ita, gani take fadila nada wata manufa cikin zuciyarta Fadila tace "Amma miye yasa kike 6atamin duk wani abu dana dafa, a gidannan? Auta ta turo baki tace "to ay ke kikafara, dan rannan da kaina na kamaki, kina zubamin gishiri a binci, kawai kyaleki nayi a lokacin, idan bazaki manta ranar danayi sakwara da miyar agushi. Fadila tayi murmushin takaici, mai cike da nadamar abinda ta aikata tun farko, *_(Dama ance farau batada zafi sai ramau)_* "To yanzu dai nazo neman sulhu, yakamata mubar duk wannan abun damukeyi, kinga bekamata ace mun zauna muna yima kanmu abunda be daceba. Auta tace "ni dama ban d'auki abun da zafi ba, kawai dai kinsan hausawa sunce _*"Ramuwar gayya tafi gayya zafi*_ Amma kome ya wuce Allah shige mana gaba, Fadila ta Amsa da "Ameen. *```To you my namesy Autar Hajiay```*💃🏻 _ina mi'ka gaisuwa ga masoya a duk inda kuke_ ~kibiyo *Zee Mmn khady* akwai sauran labari~ Zee Elkaseem Mmn khady. [10/16, 7:55 PM] ‪+234 816 616 9254‬: 🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊 *AUTAR HAJIYA* 💃🏻 🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊 ®NWA 👇🏻 _ZEE MMN KHADY_ 😘 ```page``` 171-175 ✍🏽 koda Hajiya ta farfad'o daga dogon suman datayi, doctor ya'kara dubata ya tabbatar da lafiyarta, sannan yace za'a iya tafiya da ita, amma ari'ka kula da kiyaye abinda ze jefata cikin tashin hankali. Daga asibitin gidan khaleed aka wuce da ita kai tsaye, dan an riga an wuce da gawar a can. Cikin likaffaninsu ta iskesu, hankalinta yayi matu'kar tashi, ta fashe da wani sabon kuka, tana cewa. *shikenan zainab kin tafi kin barni bayan kinsan banida wani d'a ko d'iya sai ke, Allah kai ka bani zainab kuma kai ka kwace abinka badan baka sonta ba, ya Allah ka ji'kan zainab ka kai haske cikin kabarinta* Haka tacigaba da kuka tanayima Auta addu'a nan mutane aka shiga rarrashinta ana kwantar mata da hankali. A asibiti kuma momyn khaleed da momyn Fadila sunacan suna jiran abasu dama su shiga su duba me jego da babynta, sai bayan magrib aka basu izinin Shiga, Haka suka shiga jikinsu ba 'kwari ko kad'an, Zaune take kan gado, ga baby gefenta, kuka take kamar zata fitar da ranta, idanunta sun kumbura fuskarta tayi ja, tayi face-face da hawaye, jin motsin shigowar mutane yasa ta d'ago da fuskarta wadda ruwan hawaye yagama wankewa, takai dubanta garesu. Momyn fadila itace gaba, tana zumud'in ganin fadila da babynta, ```Innalillahiwa'inna'ilaihirraji'un``` Ta faurta lokacin da idanunta suka sauka kan Auta, Zaune kan gado ga babynta kusa da ita. Momyn khaleed ce ta dafe, 'kirji Alamar mamaki tace *"Auta dama ba ke bace aka cemana kin mutu ba* .Auta ta fashe da wani sabon kuka, tana cewa, Momy fadila.....fadila.... ce tatafi ta barni, wani sabon kuka ya kwace mata. Momyn fadila najin haka tanemi numfashinta ta rasa, nan tafa'di sumammiya, Momyn khaleed tarud'e da ganin yanda 'yar'uwarta ta suma, Da sauri ta ebo ruwa ta yayafa mata, nan ta farfad'o, Zaunar da ita Momyn khaleed tayi tana rarrashinta, tana gaya mata, irin Rahamar da Wanda yamutu gurin haihuwa yake samu, tace "kawai yanzu Addu'a Fadila take nema garemu ba kuka ba. Wani sabon kuka Momyn Fadila ta fashe dashi, dan rarrashinma da akemata jitake kamar ana zuba mata garwashin wuta cikin zuciyarta, shiru suka d'anyi nawasu yan mintittika, bakajin kome sai sheshshekar kukan Auta, Momyn khaleed ta maida hankalinta kan Auta tana rarraahinta, sai jin fad'uwar Momyn Fadila tayi, A hanzarce tajuyo gareta, tarin'ka jijjigata tana kiran sunanta, amma ina ba maganar lumfashi tattare da ita, cikin tsananin rud'ewa momyn khaleed tafita tana Neman taimako, wasu leburori ne mata suka taimaka mata, suka d'ora momyn Fadila kan gadon da ake tura marassa lafiya aka nufi Emergency da ita, nan fa lokitoci suka taru anata Abu d'aya amma numfashi ko Alamarsa babu jikin momym Fadila, amma kuma da an Auna sai aga zuciyarta na bugawa Alamar akwai rai tattare da ita. Oxygen aka sanya mata *(Abin jawo numfashi)* Sai lokacin Momyn khaleed ta buga waya ta sanar da daddyn fadila halin da ake ciki, aiko cikin tsananin rud'ewa ya iso asibitin, dan shima yayi tinanin Auta ce ta rasu amma yanzu ance Fadila ce d'iyarshi wacce yakeso, wasu guntayen hawaye suka zubo daga idonshi, yasa hannu ya goge. Sai 'karfe hud'u na asuba Momyn Fadila ta farafad'o, da misalin 'karfe takwas doctor yabata sallama dan ganin jikin nata da sau'ki sosai. Lokacin kuma aka sallami Auta, bayan likitan ya tabbatar da lafiyarta data babynta. 'Karfe tara dai-dai suka isa gida, lokacin an fito da gawar Fadila data babynta, Aiko da gudu Auta ta fito daga motar, tana goye da babynta, yayinda momyn khaleed ke goye da 'diyar da fadila ta bari. Bata ko kalli yawan mutanen dake gurinba tabi tacikinsu ta isa gaban makarar ta ri'ke tana cewa ```Wayyo sister fadila kada ki tafi ki barni, fadila ki dawo mu zauna mucigaba da gina rayuwarmu yanda muka tsara.... Fadila kin manta munce zamu rike yaranmu mu had'a kawunansu su tashi tsin-tsiya mad'aurinki daya, wayyo sister fadila ki dawo garemu....``` haka tayita surutai tana kuka, nan aka kakkamata ana bata ha'kuri aka

Table of Contents

Chapters

20 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});