Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 3

Chapter 3

Autar Hajiya Book 1 Complete Hausa Novel 1,197 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

masa ba, Amma lokaci d'aya kika bad'e ido toka kikace baki sonshi, dan kingano yata6a Aure kuma ya rabu da matar, wai kina gudun kada wata rana yace ze maida ita. Auta ta numfasa sannan tayi wani guntun murmushi Wanda yafi kuka ciwo, tace "hum sadiyya bazaki ta6a ganewa ba wallahi duk lokacin da wani namiji yace yana sona daya furta min yanada aure jinake kamar in kashe kaina, dan na kwammace na mutu dana auri me mata. Sadiyya tace "to Allah kyauta, Allah rage maki wannan zafin kishin naki, tace Ameen ni kaina ina yawan yin wannan addu'ar dan wallahi wani lokaci abin har tsoro yake bani. "Wai ina khaleed ne? shiru naji kin daina zancensa, ko shima yanada matar ne?. Auta tayi murmushi, wanda yasa har kumatunta suka lo6a, tace "Hmm khaleed mutanen Sudan, ay yana can karatu, kawai yasa gaba, ni inaga kila yanzu ya manta dani, shekara hud'u fa kenan rabon da muga juna, kuma tinda yatafi ko waya bamu ta6a yi dashi ba, Amma kuma ni nasan har in mutu bazan ta6a son wani d'a namiji kamar yanda nake sonshi ba. Sadiyya tayi murmushi, tace tabbas kunyi tsantsar soyayya da khaleed, kuma bani tinanin shima ze iya mantawa dake, kuma naji ajikina khaleed shine mijin dazaki aura. Wani farin ciki ya rufe Autar Hajiya, dan tinda take duniya bata ta6a son wani namiji ba, irin son datakema khaleed, Cikin jin dad'in maganar sadiyya tace "Allah ya tabbatar min da hakan, Allah sa khaleed yazama mallakina ni kad'ai batare daya had'ani da wata jaka ba. Sadiyya tayi dariya, cikin tsokana tace au amaryar taki kike kira jaka, Auta ta kaimata duka cikin wasa tace "bani son iskanci, ki dainamin wannan wasan khaleed nawa ne ni d'aya Kedai kawai ki tayani addu'a Allah sa be manta daniba, sadiyya tace "to Allah sa be manta dakeba kuma Allah sa yana dawowa musha biki, su duka suka sa dariya, haka suka sha firarsu, sam Auta ta manta da wani ba'kin ciki datake tattare dashi, jitake kamr har khaleed d'inma yadawo an d'aura masu aure saboda tsabar farin ciki. Sai gab da Hajiya zata dawo sannan sadiyya tayi haramar tafiya, Auta tayimata rakiya, tare dayimata Al'kawarin zuwa gidansu ranar Friday. Zee Elkaseem Mmn khady [10/16, 7:54 PM] โ€ช+234 816 616 9254โ€ฌ: [31/07 10:47 am] ๐Ÿ˜˜: ๐Ÿ•Š๐Ÿ•Š๐Ÿ•Š๐Ÿ•Š๐Ÿ•Š๐Ÿ•Š๐Ÿ•Š *AUTAR HAJIYA* ๐Ÿ’ƒ๐Ÿป ๐Ÿ•Š๐Ÿ•Š๐Ÿ•Š๐Ÿ•Š๐Ÿ•Š๐Ÿ•Š๐Ÿ•Š๐Ÿ•Š๐Ÿ•Š ยฎNWA ๐Ÿ‘‡๐Ÿป _ZEE MMN KHADY_ ๐Ÿ˜˜ _Page_ 26-30 *โ€ขBayan Wata biyuโ€ข* Kwance take kan tabarma, tayi filo da cinyar Hajiya, yayinda ita kuma Hajiya ke tsefe mata manyan kitson dake kanta, cikin shagwa6a ta ri'ke hannun Hajiya tare da rintse ido Alamar tanajin zafi, tace "Hajiya dan Allah kiyi min Ahankali da zafi, Hajiya tace "to sarkin son jiki tsifar kan shine keda zafi, kitson da be wuce 'kwaya goma ba, cikin shagwa6a tace ni wallahi shiyasa ban fiye son kitson ba ma, dan dai kawai kina matsawa sai nayi. Murmushi kawai Hajiya tayi "Uhm" sannan tacigaba da kwance mata kan, bayan ta 'karasa kwance mata kitsin, tasa masharci ta sharce ta shafe mata shi da mayuka masu kyau da dad'in 'kamshi, sannan ta hade mata shi guri day'a ta d'aure mata shi, yayi gwanin kyau ya zubo har kan kafad'unta, ga gashinta da tsantsi, ga tsananin ba'ki kamar na larabawa. "Assalamu Alaikum, sallama yayi tare da shigowa cikin gidan. saurayine, d'an kimanin shekara ishirin da tara a duniya, kya'ky'kyawa ne ajin farko, ba fari bane, Amma kuma baz'a kirasa ba'ki ba, choculate colour ne, me matsakaicin tsawo, jikinsa kuwa baza'a kirasa me 'kiba ba kuma ba za'a kirasa ramamme ba. Hajiya ce tayi saurin tada, sadiya daga kan cinyarta, tace " a,a,a Bakin sudan ne, saukar yaushe, Auta najin haka tayi saurin kai dubanta ga Wanda aka kira ba'kon Sudan, wani mummunan fad'uwar gaba taji, dan ba Kowa bane tagani sai masoyinta khaleed, Wanda bata ta6a jin son wani namiji aduniya ba kamar shi. Cikin fara'a yace "Yau sati biyu kenan da dawowar mu, Hajiya tace " sannu da zuwa, shigo mana, a falo akayimasa masauki, sannan suka gaisa da Hajiya, nan take tambayarsa, ya momynsa, yace "tana lafiya tace tana gaishe Ku, tace "ina amsawa, ya karatu kuma, yace "karatu angama, yanzu kuma sai maganar ayki, tace "Allah taimaka, yace "Ameen, tace kuma yanzu Baban naka yafita da kun gaisa, yace ay mun gaisa dashi jiya, tace kaga kuwa be fad'a mamu dawowar kaba, yace "Eyyah ina tinanin mantawa yayi. Auta kuwa tun bayan shigowar khaleed, tanufi d'aki ta gyara fuskarta, sannan ta yafa wani karamin gyale ta rufe gashinta, sannan ta nufi pridge ta dauko ruwa pure water da holandia fresh milk, ta d'auko d'an karamin cup na glass ta d'ora kan wani madaidaicin tire ta nufi falo, ta ajiye gabansa, Hajiya tafita waje, tacigaba da yan hidindimunta. Auta kuwa guri ta samu ta zauna, kan kujerar, dake facing d'insa, sannan ta gaidashi, ya tsareta da ido, a zuciyarsa yace _wai Autar hajiya ce takoma haka lallai yanzu nakara tabbatar da gangancin danayi na amincewa da auran fadila_ "sannu da zuwa, tafad'a cikin zazza'kar muryarta, me kama da ta yara, yace "yauwa sannu na sameku lafiya, tace "lafiya lau, tasowa tayi tazo gabansa, ta zuba Mashi, fresh milk a cup ta mi'ka mashi, ya kar6a ya kur6a sannan ya ajiye, kallonta yaci gaba dayi yanda Kasan yau yafara ganinta. Ita kuwa wani sabon sonshi, taji ya 'kara mamaye zuciyarta, a ranta cewa tace _Allah sa yanda nakejinka a zuciyata kaima haka kakejina_. Zee Elkaseem Mmn khady [31/07 11:49 am] ๐Ÿ˜˜: ๐Ÿ•Š๐Ÿ•Š๐Ÿ•Š๐Ÿ•Š๐Ÿ•Š๐Ÿ•Š๐Ÿ•Š๐Ÿ•Š๐Ÿ•Š *AUTAR HAJIYA* ๐Ÿ’ƒ๐Ÿป ๐Ÿ•Š๐Ÿ•Š๐Ÿ•Š๐Ÿ•Š๐Ÿ•Š๐Ÿ•Š๐Ÿ•Š๐Ÿ•Š๐Ÿ•Š ยฎNWA ๐Ÿ‘‡๐Ÿป _ZEE MMN KHADY_ ๐Ÿ˜˜ _Page_ 31-35 Saida yagama 'kare mata kallo a zuciyarshi yana cewa _Allah ka mallakamin zainab Amatsayin uwar 'ya'yana, tabbas nayi gangancin Amincewa da Auren fadila,Amma ba kome tinda itama inasonta zan had'a dukansu in auresu_ Ita kuwa auta duk ta tsargu da yanda ya tsareta da ido, gashi ya'ki magana, sun kai kimanin minti goma a haka, sannan yace " Autar Hajiya, kece kika koma haka? Cikin jin kunyar tambayar dayayi mata tayi murmushi kawai, dan batada Amsar dazata bashi, illah tsananin sonshi da 'kaunarshi dake d'awainiya da zuciyarta. Jin dayayi batada niyyar magana, yasashi tasowa daga inda yake zaune, ya dawo kusa da ita, ya zauna kan hannun kujerar datake zaune akai, kasancewar kujerar ta zaman mutum d'aya ce. Wani irin kallo yayi mata, Wanda yasata jin wani yarrr ajikinta, lokaci guda kuma ya kashe mata ido, yace "ya maganar soyayyarmu tananan kokuwa bayan tafiyata kin samu wani?, cike da jin kunya, da kuma jin dad'in zancen daya fito daga bakinsa, itama ta watsa mashi wani kallo, wanda lokaci guda yaji jikinsa yayi sanyi, tace "ai kaine yakamata inyima wannan tambayar, domin tinda katafi ko a waya ka nemeni baka ta6a ba, kaga kuwa kaine zance kasamu wata. Yayi wani 'kyayataccen murmushi, yace "Zainab bazan ta6a had'a soyayyarki da wata mace ba, ina sonki ina 'kaunarki, kuma burina Aurenki, kawai yanzu ki amice in sanar da baba,saboda na matsu na ganki gidana a matsayin matata, ke kinga yanda kika koma kuwa, ai gaskiya nataki sa'a dana iskeki, wani be min shigar sauri ba. Tinda yafara magana Auta jinsa kawai take, a zuciyarta kuwa cewa take _"Khaleed nafika son kasancewa matarka dan a duniya banida wanda

Table of Contents

Chapters

20 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});