Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 4

Chapter 4

Autar Hajiya Book 1 Complete Hausa Novel 1,195 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

nakeso nake 'kauna kamar kai_ Khaleed yace "kinyi shiru Kodai akwai Wanda kukayi al'kawarin aure ne? Tayi murmushi, wanda har saida kumatunta suka lo6a, tace "babu wani bayan kai, kuma na Amince da ka sanar iyaye su shiga maganar, sai Kuma fatan Allah shige mana gaba, yace "Ameen, Amma nayi matu'kar farin ciki, gaskiya auta ina sonki, so irin Wanda be musaltuwa, wani sanyi taji ya mamaye zuciyarta, tare da jin wani irin shau'ki a cikin ranta. Haka suka kwashe kusan awa biyu suna Fira, kafin Daga bisani yayi haramar tafiya, har Bakin mota tayi masa rakiya, bayan sunyi sallama da Hajiya, Wata leda ya Ciro Daga motar ya mi'ka mata, "ga tsarabarki, ta kar6a cikin jin kunya tare dayimasa godiya, Tananan saida yashiga mota yatafi, harya 6ace tana d'aga mashi hannu sannan takoma gida, cikin farin ciki ta tarar da Hajiya zaune falo ta mi'ka mata ledar. Hajiya ta amsa tare da tambayarta "na miye? Auta tace "tasaraba ce khaleed ya kawomin, nan suka zazzage kayan suna cikin dubawa me gidan ya shigo, falon yanufa kai tsaye dayake ya jiyo maganarsu a can. Hajiya tayi mashi sannu, itama auta cikin girmamawa tace "Baba sannu da zuwa, yace "yauwa zainabu, sannan ya kalli kayan dake gaban Hajiya yace "wannan kayan fa, tace "khaleed ne yazo yanzu be dad'e da tafiya ba, yakawoma auta tsaraba. Kayan cosmetics ne masu tsadar gaske, sai takalma kala biyu, suma tsadadadu, sai swiss less guda, sai atamfa super aura, sai turaruruka designer's, masu dad'in kamshi. Zee Elkaseem Mmn khady [10/16, 7:54 PM] ‪+234 816 616 9254‬: 🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊 *AUTAR HAJIYA* 💃🏻 🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊 ®NWA 👇🏻 _ZEE MMN KHADY_ 😘 _Page_ 36-40 *Bayan wata d'aya* Soyayya tayi nisa tsakanin khaleed da Autar Hajiya, dan yanzu yanda takejin khaleed a zuciyarta, bazata iya rabuwa dashiba, kome rintsi kome wuya, bata had'a sonshi dana Kowa ba, shima haka yake mata wani matsanancin so. Yanzu dai iyaye sun san da maganar soyayyar khaleed da Zainab, dan har anyi maganar aurensu, ansaka ranar auren nan da wata ukku. Ranar da auta tasan an saka ranar aurenta da khaleed, ranar jitayi kamar anyimata busahara da gidan Aljanna, saboda tsabar farin ciki , shima 6angaren khaleed d'in haka, dan tinda yake beta6a had'a son auta dana wata mace ba, ko fadila yana sonta ne kawai saboda wasu dalilai amma ko kad'an bazaya iya had'a son da yake mata ba da Wanda yakema auta. ***** ****** ****** "Wai ni khaleed bangane me kake nufiba, Cikin gadara da nuna isa take maganar "kana nufin ka raina za6in danayima a matsayina na mahaifiyarka ban isa dakai ba, sai kawai inji labarin wai ansaka ranar aurenka da Autar Hajiya, dan Baku d'aukeni a Bakin kome ba kaida mahaifinka, kun maidani shashasha, to wallahi baka isaba, wato ka za6i 'yar'uwarka shikuma mahaifin naka dan yaga d'iyar d'an uwansa ce shine ya Amince hadda sa ranar aure ba tare da saninaba, sai bayan anyi anyi kome angama ranar aure kawai ake jira tazo sannan aka sanar dani. Tinda matar tafara magana khaleed be ce uffan ba sai da tayi shiru sannan yafara magana cikin nutsuwa, da Alamar rarrashi, yace "kiyi ha'kuri Momy nasan idan na tinkareki bazaki yarda da maganar aurena da Zainab ba, shiyasa na ro'ki daddy akan kada ya sanar dake har sai an tsaida ranar, amma dan Allah Momy kiyi hakuri, badan banison Fadila nayi haka ba, kawai manufata shine bayan na auri Zainab da kamar shekara ita kuma sai in aureta daga baya. Wani irin salati ta kwad'a Wanda yasa 'yan'cikin sa juyawa, sannan tafara magana cikin masifa, Wato khaleed ni zaka cima mutunci ka nuna dangin ubanka sunfi dangina daraja a gareka, to wallahi ban Amince da wannan manufar takaba, sai dai kafara auren fadila sannan daga baya ka auri Autar, dan bazan hanaka aurensuba, dan su duka 'yan'uwanka ne, kuma Addini be hanaka auren Mace biyu ba ko ukku, kai harma hud'u, Amma kasani Fadila, itace ta farko idan kuma ka'ki za6ina to wallahi sai dai kafasa aurensu su duka. Khaleed rasa yanda zeyi yayi, dan yasan halin mahaifiyarsa sarai, zata iya wargaje maganar aurensa da Auta, wacce kuma itace macen daya fara so a duniya kuma har yakoma ga mahaliccinsa baze so wata mace kamar yanda yake sonta ba. Cikin tsoron halin mahaifiyarsa, yace "na Amince momy zanyi yanda kikace, zan fara auren Fadila Daga baya sai in auri Zainab d'in. Bata san lokacin da ta saki wani murmushi ba tace "yauwa to ko kaifa, murmushi yayi na k'arfin Hali dan gabaki d'aya ji yake Momy tagama takura rayuwarsa. Amma dan Allah Momy ina Neman wata alfarma, tace "ina jinka Yace dan Allah Momy idan antashi sa bikina da Fadila, asa wata d'aya saboda baniso a canja lokacin da aka sa bikina da Auta, cikin nuna rashin damuwa tace "wannan kuma matsalar kace, idan ma sati d'aya kace a sanya iyayenta shirye suke,kamar yanda kake shirye. A ranar Momyn khaleed ta sanar da daddynsa, yanda sukayi da khaleed, be musa mataba, ya Amince da duka bayanin datayi mashi. Anje Neman auren Fadila, wacce ta kasanece 'ya ce ga 'Kanwar Momyn khaleed, Fadila kwarkwararrar 'yar duniyace, wacce boko yagama zaunawa jikinta, da kwalwarta, wayayyace ajin farko, zata kai shekara ishirin da biyar a duniya. Cikin sati d'aya aka gama magar auren khaleed dafadila, ansaka ranar biki wata d'aya da sati biyu. _To fah jama'a kunsan dai ba abinda Auta Hajiya tatsana kamar namiji me mata kuma gashi sahibinta wanda tafi 'kauna zaya fara auren wata kafin ita tab, 🤔 lallai akwai bada'kala_ *kudai kubiyo Zee Mmn khdy dan jin yanda zata kasnce* 08166169254 Zee Elkaseem Mmn khady [10/16, 7:54 PM] ‪+234 816 616 9254‬: [01/08 7:32 am] .: 🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊 *AUTAR HAJIYA* 💃🏻 🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊 ®NWA 👇🏻 _ZEE MMN KHADY_ 😘 _Page_ 41-45 *Bayan sati Biyu* ✍🏽 "Auta,....... Hajiya ce ta kwala mata kira tana daga kitchen, da sauri ta iso tace "gani, Hajiya ta mi'ka mata wani d'an karamin bokiti, "anshi ebo min ruwa nan in tsame d'an wakennan, sauri nake fita zanyi, da sauri Auta ta kar6a ta ebo ruwan takawo ta ajiye sannan ta d'auko kujera irin ta zaman tsakar gida ta zauna tace "Hajiya ina zaki ne?, Hajiya tayi murmushi tace kai lefe zamu koh, Auta ta kalleta cikin rashin Sani tace waye zeyi aure? Hajiya tace to waye zeyi aure kuwa in banda yayanki, Amma ay nasan dai ya sanar dake, Auta tace "Hmm Hajiya nifa ban gane wane yayana kike nufiba tukun, _kwata-kwata Auta bata kawo khaleed aranta ba dan tasan ita kadaice za6insa kuma be had'a sonta dana kowaba_ Hajiya tace "yayanki khaleed mana, kina nufin be sanar dake nan da sati biyu za'a d'aura auren sa ba, Jitayi kanta na juyawa, zuciyarta tayi mata nauyi, idanunta sun daina ganin haske, kanta yayi wani irin sarawa, lokacin kuma ta nemi numfaahinta ta rasa, Hajiya na daga kitchen kawai sai gani tayi Auta tafad'i kasa ba Alamar numfashi tattare da ita, da sauri tanufi inda ta fad'i tana furta Kalmar *Innalillahi,wa'inna,ilahirrajiun* A d'imauce take gigizata tana kiran *Zainab*....... amma ko Alamun motsi batayi, cikin tsananin rud'ewa ta dauko waya takira me gidanta, ta sanar dashi Auta ce ba lafiya, gata kwance ko motsi batayi, Cikin tsananin rud'ewa suka nufo gidan

Table of Contents

Chapters

20 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});