Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 18

Chapter 18

Autar Hajiya Book 1 Complete Hausa Novel 1,193 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

shige da ita cikin gida, Hajiya tana cikin gida tanajin hayaniya daga waje, sai kunnuwanta suka ri'ka jiyo mata kamar muryar Autar ta, amma saita share tacigaba da istigifari tana nemar ma Auta rahamar ubangiji, dan tariga tasan Auta ta mutu kuma Wanda yamutu baya dawowa. Da sauri ta taso dan ganin anshigo da Auta tana kuka, wasu mata sun rirrekata, Cike da mamaki ta isa gareta tace Auta dama bake bace kika mutu, bata bata amsaba sai wasu zafafan hawaye dasuka 'kara ganagarowa daga idanunta. Hajiya batasan lokacin data rugume Auta ba tana wani irin kuka me wuyar fassara, na farin cikine kona ba'kin ciki. Da misalin 'karfe sha d'aya yan kai gawa suka dawo, Allahu Akbar ankai Fadila makwancinta. Lokacin Kuma akayi addu'a aka shafa, gidan yayi tsit bakajin kome sai sheshshekar kukan mutane 'kasa-'kasa. 📿📿📿😭😭😭📿 📿📿😭😭😭📿📿📿 ```Kulli nafsin za'ikatul maut, dukkan mai rai mamacine " fadila tarigamu gidan gaskiya``` 😭😭😭📿📿📿😭😭📿📿 Zee Elkaseem Mmn khady [10/16, 7:56 PM] ‪+234 816 616 9254‬: [15/08 9:39 am] .: 🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊 *AUTAR HAJIYA* 💃🏻 🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊 ®NWA 👇🏻 _ZEE MMN KHADY_ 😘 ```Page``` 161-165 ✍🏽 Alhmdulillahi dan kuwa yanzu ansamu jituwa tsakanin Fadila da Zainab ```{AutarHajiya}``` yanzu kowace tarage jin haushin 'yar'uwarta, Saidai fa maganar girki idan fadila tayi, basu iya ci sai dai su d'an yafuta su tashi badan sun 'koshiba, Auta kuwa kalaluwan girki takeyimasu masu dad'in gaske. Watarana Auta na zaune falo tana kallon wani tsohon Indian film mai suna *(Maharaja)* ta maida hankalinta tsaf kan TV sai jitayi an rufe mata ido ta baya, takama lalube tana dariya, takama hannun da aka rufemata fuska ta ri'ke tana dariya, tana cewa "dan Allah ko waye ayimin afuwa kada ayi wani Abu a film dinnan ban ganiba, Sakin fuskar tayi ta zagayo ta zauna kusada ita, tana dariya itama Auta dariyar take, takai kallonta ga Fadila tace "Kai sister yanzu abinda kikayimin kin kyauta, kinja an wuce banga wani wurinba, Fadila tayi dariya tace "to ay sai kiyo tariya, cike da nishad'ia Auta ta mi'ko mata remote d'in tana dariya tace "kar6i tariyo min, dan tasan ba maganar tariya tunda ba kaset bane ta sanya. Fadila tayi dariya tace "ni ban iya wannan tariyar bakedai ki tariyo tinda kece meson kallon, murmushi kawai Auta tayi tacigaba da kallonta. Kusan Awa d'aya da yan mintoci Fadila na zaune tana taya Auta kallo, saida film d'in ya'kare ana shirin sanyo wani, Auta takai dubanta kan agogon dake manne jikin bangon d'akin taga har 12 ta d'an gota. Auta ta kalli fadila tace girki fa? Kinsan fa rana tayi baki d'ora mana ba, gaskiya ki tashi kada kiyi mana horon yunwa, fadila tayi dariya tace wace ni in horaki da yunwa, kinaso me gidan ya d'aga min yellow card kenan abani hutun sati biyu, Auta tayi dariya tace ayko baze fara ba, kinsan kuwa irin son dayake maki, ai ko hutun kwana biyu baze iya bakiba baranatana sati biyu, dariya sukayi su duka. Bayan shiru ya ratsa na yan wasu mintittika Fadila takai dubanta ga Auta tace "Niko Auta me zaihana murin'ka yin girki tare, ranar girkinki muyi tare nima idan nawa yazo muyi tare. Auta tayi dariya, tariga tagama d'agowa da fadila, so kawai take tari'ka tayata dan itama tasamu girkinta yayi armashi kamar nata. Tare suka shiga kitchen suka fara girki, farar shinkafa suka dafa me had'e da makaroni, sannan sukayi miya mai rai da lafiya, cikin 'kan'kanin lokaci suka gama suka jera kome kan dining sannan suka gyara kitchen d'in tsaf sukayi moping, kafinnan kowace tawuce d'akinta ta sheka wanka suka fito falo suka zauna zaman jiran me gidansu, sunyi kyau suduka shar dasu abin gwanin ban sha'awa. Khaleed ne yashigo gidan da sallama suduka suka tashi suka tarbeshi sunayimashi sannu da zuwa, fadila ta kar6i jakar dake hannunsa ta wuce mashi da ita d'akinsa, Saida yaba Auta lafiyayyen kiss sannan ya wuce d'akinsa, ya tarar har fadila tagama had'a mashi ruwan wanka, Wanka yashiga, bayan yafito ya sanya kananan kaya marassa nauyi, sannan suka fito suka zauna kan dining, sunfara cin abinci gwanin ban sha'awa sunata fira suna dariya,. khaleed ya kai dubansa ga Fadila yace waini fadila kodai kema kin Shiga makarntar koyon girkine bansaniba,? Auta tayi saurin tashi ta d'auko filo daga cikin filon kujerun daka zagaye a falon ta mi'koma Fadila tana dariya tace "kar6i sister yimasa waigi kada yafadi ace mune muka kadashi, suduka suka sanya dariya hada kyalkyatawa, Fadila tad'an tsagaita da dariyar datake tace "bawata makaranta nashiga ba illah makarantar sister d'ita gata zaune kusa dakai, ta nuna Auta. Cike da jin dadi, khaleed yad'aga hannunsa sama, yace "Allah nagodema daka bani mata nagari masu sona masu 'kaunata masu son kasancewata cikin farin ciki koda yaushe, ya kallesu su duka yace Allah yayi maku Albarka suduka suka amsa da "Ameen. Ranar dai haka suka wuni cikin nushad'i da annushuwa, dan ranar khaleed be fita ko'inaba, saboda jin dad'in zaman gidan dayayi. ************************* *_BAYAN WATA TAKWAS_* Ahankali take takawa zuwa d'ankin Auta saboda nauyin da cikinta yayimata, tura kyauren d'akin tayi sannan ta shiga da sallama, Auta dake kwance kan kujera 3seater itama da 'katon cikinta, idanunta rufe kamar me bacci, jin shigowar Fadila yasa ta bud'esu takai dubanta gareta, sannan takai dubanta ga cikin Fadila, har cikin ranta take tausayama Fadila yanda take fama da ciki, dan tinda tasamu cukin take ta rashin lafiya, yau zazza6i, gobe ciwon kai, ga kuma rashin 'karfin jiki, babban abin ban tausayin shine tinda Fadila tasamu ciki bata iya cin abincin kirki, ga wani irinkumburi datayi, danma koda yaushe khaleed na kula da lafiyarsu itada Auta. Duk da itama Auta tana d'an ta6a rashin lafiyar jefi-jefi, amma idan ka kalli fadila sai kace Auta ba ciwo take ba. Tare suka fito falo suka zauna suna firar duniya, duk rabin firar tasu ta yanda zasu tsara rayuwarsu ne nan gaba, da yanda zasu had'a kan 'ya'yansu sutashi kansu a had'e. Zee Elkaseem Mmn khady [15/08 11:11 am] .: 🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊 *AUTAR HAJIYA* 💃🏻 🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊 ®NWA 👇🏻 _ZEE MMN KHADY_ 😘 ```Page``` 166-170 ✍🏽 Yau Fadila ta tashi da matsanancin ciwon mara da ciwon baya, ga 'kugunta da takeji kamar ze 6are saboda azabar ciwo, Daga khaleed har Auta sun rud'e sun rasa inda zasusa Kansu, cikin tsananin rud'ewa khaleed yakira Momynsa yasanar da ita halin da fadila take ciki, nan ta umarceshi da sutafi asibiti gatanan zuwa asbitin, tare da taimakon Auta aka kai Fadila mota sai asibiti, An wuce da ita labour room, nurses sun taru kanta anata faman amma, har 'karfe 3 na rana bata haihuba, lokacin Momyn Fadeela ta iso asibitin cike da tashin hankali, nan ta iske Momyn khaleed sai kai komo take cikin asibitin, kallo d'aya zakayimata ka gane tana cikin tsananin damuwa, khaleed kuwa tagumi yayi yarasa me kemasa dad'i. Lokacin wayarsa tayi ringing, hannu yasa ya dauka, sunan Auta yagani yana yawo kan screen d'in wayar, da Sauri ya d'auka ya kara a kunneshi, muryar dayaji Auta tana magana da itace ta d'aga mashi hankali, cikin tsananin ciwo take maganar _"kha....khaleed kazo ka taimakeni zan mutu_...... Dai-dai lokacin wayar ta su6uce Daga hannunta, cikin tsananin rud'ewa khaleed yasanar da momynsa abinda ke faruwa, tare suka tafi gidan, da sauri suka shiga bayan sun

Table of Contents

Chapters

20 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});