Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 5

Chapter 5

Autar Hajiya Book 1 Complete Hausa Novel 1,193 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

shida daddyn khaleed, dan lokacin da Hajiya tayi waya ta gaya Mashi suna tare. Kusan minti sha biyar sannan suka iso, har yanzu Auta na kwance ba Alamun rai tattare da ita, Hajiya na tallabe da ita tana faman zubar da hawaye, batare da 6ata lokaci ba aka sakata mota sai asibiti, suna zuwa aka wuce Emergency da ita, kahleed shine likitan daya kar6e ta tare da taimakon wasu abokan aykinsa suke kokarin ceto rayuwarata, Kusan minti talatin Amma Auta bata farfad'o ba, hankalin iyayenta yayi masifar tashi, ba kamar Hajiya wacce saboda tsananin kuka idanunta sun kumbura sunyi jawur, kallo d'aya zakayimata ka gane tsantsar tashin hankali tattare da ita. An akai kimanin awa daya, sannan Auta ta farfad'o Amma duk da haka bata san inda kanta yakeba, haka aka fito da ita Daga Emergency, aka maidata wani d'akin, tare da sanar da iyayenta inshaAllah kome normal data farka, babu wani ciwo dake tartare da ita sumar datayima yanada Ala'ka da wani Abu daya d'aga mata hankali, amma muddin aka kiyaye zata cigaba da samun sau'ki, khaleed ne kema Hajiya wannna bayanin, dakuma daddynsa da Baban Auta Wanda su duka shi suke sauraro. Zee Elkaseem Mmn khady [01/08 8:36 am] .: 🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊 *AUTAR HAJIYA* 💃🏻 🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊 ®NWA 👇🏻 _ZEE MMN KHADY_ 😘 _Page_ 46-50 ✍🏽 Hajiya zaune gaban gadon da Auta ke kwance, ta zuba mata idanu tana kallon yanda take maida numfashi, ahankli tafara motsawa alamar farkawa daga baccin datakeyi, Ahankali ta bud'e idanunta ta 'karema d'akin kallo ta tabbatar da asibiti take, sannan Ahankali ta ri'ka tino maganar da Hajiya ta gaya mata, wasu zafafan hawaye suka zubo ta gefen idonta, A zuciyarta tana cewa. _shikenan rayuwata batada wani amfani wanda nikeso yaci amanata ya cuci rayuwata bayan yariga yasan ba wanda nakeso kamarsa, bazan iya mallakama wani namiji kainaba bayan shi, wasu zafafan hawaye suka zubo daga idonta_ Da sauri Hajiya ta matso kusa da ita tana yimata sannu, "auta kiyi hakuri ki d'auki 'kaddara, kisani duk me rai ba Wanda kaddara bata fad'amawa, kuma ki d'auki wannan Amatsayin jarabawa ce daga nahaliccinki, kawai sai kiyi fatan cinye wannan jarabawar. Cikin disashshiyar murya, auta tace "Amma Hajiya khaleed ya cuceni yaci Amanata yagama da rayuwata, Allah ya Isah tsakanina dashi. Ta fashe da wani irin kuka me ban tausayi, ta sauko daga kan gadon datake ta dur'kusa gaban mahaifiyarta, tace "Hajiya dan Allah ki gaya ma Baba bazanyi aureba har Abada, na hakura da aure, dan Allah Hajiya kada Ku 'kara tinkarata da maganar aure. Kama hannunta Hajiya tayi ta mi'kar da ita tsaye, ta maidata kan gadon ta zaunar da ita, sannan tafara mata magana cikin sigar kwantar da hankali, tace "Auta wannan maganar dakikeyi bame yiyuwa bace, ke kanki kinsan halin mahaifinki sarai ba saina sake maimaita makiba, kin San dai baze samaki ido ki zauna ba aure ba, kuma khaleed ba cewa yayi yafasa aurenkiba, maganar aurenki dashi tananan ba Abinda ya canja, ita wannan wacce ze aura d'iyar kanwar momynsa ce, kuma tin yana sudan mahaifiyar ita yarinyar tabashi ita, saboda haka inaso ki nutsu ki kwantar da hankalinki, kisani aurenki da khaleed ba fashi, idan kuma zaki tinkari mahaifinki da wannan maganar to kisani nidai ba ruwana. A hankali aka turo kyauren d'akin, suduka suka maida hankalinsu gurin dan ganin me shigowa, khaleed ne yashigo da sallamarsa, sanye yake cikin milk d'in shadda wacce tasha ayki da zare copee, sai wani daddad'an 'kamshi ke tashi daga jikinsa, lokaci guda kamshin turarensa ya bige d'akin, kallo d'aya auta tayi mashi taji wani masifaffen sonshi ya'kara shiga zuciyarta, lokaci guda kuma ta tuno da cin Amanar dayayi mata, batasan lokacin data tashi Daga kan gadon datakeba taje ta cakumeshi, ta fashe da wani irin kuka, tace "Khaleed ka cuceni kaci amanata, Allah ya isah tsakanina dakai, kuma ka Sani bazan aurekaba koda Kaine auntan maza a duniya. Da hanzari Hajiya ta mi'ke tana 'ko'karin 6an6are hannun Auta Daga jikin khaleed, amma hakan ya gagara dan Auta ba karamin ri'ko tayi Mashi ba, cikin 6acin rai Hajiya ke magana, "ki sakeshi nace auta, saima ta'kara rikeshi tana mashi wani matsiyacin kallo Wanda shi kanshi yakasa gane kona miye. Ji kake tasss, Hajiya ta d'auke Auta da mari, hakan kuma yayi dai-dai da shigowar daddyn khaleed, da kuma babab ita Autar, cikin 6acin rai Hajiya take magana, "waike Auta wace irin shashashar yarinya ce da ina maki magana amma kin raina maganata, cikin sanyin jiki Auta ta saki khaleed tafad'a kan gado ta fashe da kuka, Ko kad'an khakeed beji dad'in marin da Hajiya tayima Auta ba, dan dama yasan duk ranar dataji labarin aurensa zatayi abinda ma yafi wannna dan yanda take gaya mashi batason kishiya, ta tsani kishiya. Zee Elkasee Mmn Khady [10/16, 7:55 PM] ‪+234 816 616 9254‬: [02/08 5:24 pm] .: 🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊 *AUTAR HAJIYA* 💃🏻 🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊 ®NWA 👇🏻 _ZEE MMN KHADY_ 😘 _Page_ 51-55 ✍🏽 "wannan zancen banza ne zancen Wofi, abinda baze ta6a yiyuwa bane, Wato Zainabu kinaso ki maidamu 'kananan mutane ko? ko kinaso ki haramta abinda Allah ya hallata, duk namiji Allah ya halatta mashi Auren mace daga d'aya har zuwa hud'u, saboda haka ke baki isa ki haramta Abinda Allah ya halatta ba. Mahaifin Auta ne keta faman fad'a tinda suka shigo asibitin shida mahaifin khaleed, Hajiya tabasu labarin abinda ya faru tsakanin Auta da khaleed. Cigaba yayi da fad'a ta inda yake shiga ba tanan yake fita ba, Auta kuma banda aikin kuka ba abinda takeyi, kwance take kan gadon asibitin ta juya fuskarta dan bazata iya had'a ido da khaleed ba, dan ita kanta sai daga baya tayi danasanin abinda tayi mashi, cikin zuciyarta kuwa cewa take. _Allah kasa kada Abinda na aikata yazama silar fasa Aurena da khaleed inason khaleed son da bazan ta6ayima wani namij iirinsaba_.... Wani sabon kuka ta fashe dashi lokacin data tsinkayo muryar daddyn khaleed yana cewa, "A'a Alhj baza'ayi hakaba kada fa atakurama yarinya, yakamata atambayeta aji ra'ayinta, tinda ada lokacin data Amince da aurensa ba'ayi da ita ze fara auren wata kafin itaba.... "Haba Alhj ka daina wannan mqganar" Baban Auta yafada' "yaushe zamu zauna yarinya 'karama kamar Zainab tana juyamu, "to kisani cewa aurenki da khaleed ba fashi, ke barima kiji in sanar dake, an sassauto da lokacin bikin yadawo lokaci daya da wanda za'a d'aura mashi nan da sati ukku, inshaAllah lokaci guda za'a kaima khaleed mata biyu, Alabashi kinga idan aka kaiki saiki kashe kanki saboda tsabar kishi, shashasha kawai wacce bata San ciwon kanta ba. Cikin fushi yafita daga d'akin, daddyn khaleed yabi bayansa, Hajiya ma binsu tayi, Harabar asibitin suka tsaya daddyn khaleed yana cigaba da ba d'an'uwansa hakuri " yana cew "Kabi kome a sannu Zainab d'in duka nawa take dazaka ri'ka yimata fad'a kamar kanayi da wata babbar mace, duka bana fa take cika shekara sha takwas, kaga kuwa akwai 'kuruciya tattare da ita. Hajiya dake tsaye tana saurarensu, tace " haba Alhj ai halin Zainab dole sai da haka, idan ba'a tsawata mata haka zata ri'ka mana yawo da hankali, ni kaina naji dad'in haka, kuma 'kara da aka sassauto da bikin ayi a huta. Daddy khaleed yace "Allah sa haka shine mafi Alkhairi, suduka suka Amsa da "Ameen. Cikin

Table of Contents

Chapters

20 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});