Chapter 2
Chapter 2
can na kai ma kewaye, yace "to bari inje inyi wankan, "Amma kafin in Shiga inaso in tabayeki, tace "to Alhj inaji, yace "Wannan yaron dana gani 'kofar gida yazo gurin Zainab tin yaushe yake zuwa, Hajiya tace "yau ne farkon zuwanshi, da Autar ma tace bazata fitaba dan bata sanshiba, nice nace tafita taji me ke tafe dashi, Alhj yace "kin riga kinsan banison inga yarinya tana tsayawa da samari barkatai, saboda haka ki gaya ma ita Zainab d'in idan har tana son wannan yaron to tasanar dashi yaturo da magabatanshi, kafin yacigaba da zuwa gurinta. Hajiya tayi murmushi tace, "Haba Alhj Daga zuwa d'aya sai ace yaturo kamar muna Neman maraba da d'iyar, ay dole dai su samu su fahimci juna kafin a kai ga maganar iyaye, yace " kidai gaya mata idan tana sonshi ya turo magabantashi, idan kuma bata sonshi kada in'kara ganinsa 'kofar gidannan, "kuma da kikace ba Neman maraba ake da itaba, so kike mu tasa ta gaba muyita kallonta, tinda tagama makaranata, kuma islamiyya sunyi sauka ai Alhamduliilah, Aure kawai yarage muyi mata hankalinmu ya kwanta, haka suka gama tattaunawa sannan ya fito yanufi kewaye, dan yin wanka, ita kuma tanufi d'aki inda Autar Hajiya take tana ta tinane-tinane kala-kala. Da sallama ta shigo d'akin, ta isketa kwance, kamar me bacci, amma ba baccin takeba' tinani ne kala-kala acikin zuciyarta, nan Hajiya ta bayyana mata yanda sukayi da babanta, na maganr ba'kon datayi yau. Cikin tsananin firgici, ta dafe 'kirji tace "wallahi Hajiya bani sonshi, ni banma sanshiba, yau ne fa kawai nafara ganinsa, "Dan Allah ki gaya ma baba abar wannna maganar, murya saukaji kamar Daga sama yana cewa, "ba saita gaya maniba inaji, waike zainabu yaushe zakiyi hankali, ki nutsu ki fitar da miji kiyi aure, yaufa shekara biyu kenan da gama makarantarki, Amma ko kad'an bakiso ayi maki maganar aure, to kisani bazan sanya maki ido ba kina zaune, muddin idan nagaji da zamanki zan za6a makin duk Wanda naga ya kwanta min arai. Wasu hawaye masu zafi suka zubo, kan kumatunta, tace dan Allah Hajiya ki gayama baba wallahi banison miji me mata, wallahi zan iya auren Kowa amma banda me mata, Hajiya tacigaba da rarrashunta tana cewa, haba auta, saboda me bakison me mata, mace nawa ta Auri me mata ukku ma itace cikon ra hud'u kuma ta xauna lafiya. Wani kululun ba'kin ciki taji ya tokare mata zuciya. Azuciyarta tace _Ni in auri me mata ukku ay 'kila kafin a kaini zuciya ta buga namace saboda tsananin kishi_ _kome mata d'aya bazan iya aureba_ Wani sabon kuka ta faahe dashi. Zee Elkaseem Mmn khady [10/16, 7:54 PM] +234 816 616 9254: [29/07 7:16 pm] .: 🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊 *AUTAR HAJIYA* 💃🏻 🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊 ®NWA 👇🏻 _ZEE MMN KHADY_ 😘 _Page_ 16-20 ✍🏽 washe gari haka Autar Hajiya ta tashi jikinta sukuku, a zuciyarta tana ma Adam Allah ya Isah, yanzu gashi sanadin zuwanshi, yajawo mata babanta ya tado da maganar tayi aure, Wanda a da ya lafa da maganar, kuma shi gashi yanada mata barantana ta auresa, itako yanda babanta ya matsa mata akan tafito da miji wallahi da Adam bayada mata data auresa, saboda Adam beda makusa, Amma kuma ya cuceta daya furta mata kalmar "So" Alhalin yanada mata, _Allah ya isah tsakanina da kai Adam_ ta Furta afili tare da zubar da wasu guntayen hawaye. Ranar haka ta kasance ita d'aya cikin gida, tinani kala-kala ya addabi zuciyarta, kasancewar yau litinin Hajiya tana gurin ayki, tana aykine a general hospital katsina, yayinda babanta yake ayki, ma'aikatar agric, fannin dabbobi. Da sallama wani yaro ya shigo, ta amsa masa sallamar, sannan yace auta ana sallama dake waje, tanajin haka bata tsaya tamabayar waye me sallamar ba tace kace ina zuwa, ko ba tamabaya tasan be wuce Adam, takoyi matu'kar farin cikin zuwansa dai-dai wannan lokacin, yanzu ko zata fita ta bige masa warning. Hijab ta Sanya, sannan ta zari silifas d'inta na wanka tanufi kofar gida. Shine kuwa, Wanda take tsammanin, jingene yake jikin motarsa, yauma yayi shiga ta musamman, yayi masifar kyau, cikin gadara da tsiwa ta isa gabanshi, yau ko gaisuwa be samu arzi'kinta ba, ta tsaya gabansa tare da d'aure fuska kamar bata ta6a dariya ba. Cikin fara'a yake magana, "sannu da fitowa gimbiyar mata, ina fatan dai ban takura maki ba danazo dai-dai wannan lokacin, wallahi nakasa daurewa ne da rashin ganinki....... Hannu ta d'aga mashi, tare da yimashi magana cikin d'aga murya, "dakata! Adam kake ko waye, inaso in gaya maka ka fita hanyata, dan wallahi tallahi kaji rantsuwar musulmi wacce daga ita babu wata, to ko duniya zata rage daga ni sai kai bazan aure kaba. Cikin tsananin tashin hankali, da mamakin jin kalamanta, Wanda koda wasa beyi, tinanin jin wannan daga gareta ba, a yanda ya d'auketa yarinya, me hankali, da nutsuwa ga kuma uwa uba ilimi, na addini dana zamani. Cikin sanyin jiki Adam yafara magana, yace "Zainab saboda me kika yanke wannan tsatstsauran hukuncin a kaina,? Ko kinyi bincike ne kingano wani aybu da nike dashi?. "Ko d'aya tafad'a, illah dalili d'aya shine bazan iya auren me mata ba, "idan kuwa ka nace akan saika aureni to wallahi saidai akai gawata gidanka, dan zan iya shan guba in kashe kaina, na tsani kishiya, hakan ne yasa duk Wanda ze zomin da maganar aure bamu dai-daitawa, saboda mafi yawancin masu zuwa Neman aurena masu auren sunfi samarin yawa. Bata jira abinda ze fad'aba tashige gida,zuciyarta cunkushe da abubuwa da dama. Wani kululun ba'kin ciki ya tsaya ma Adam azuciya, yama kasa matsawa daga Inda yake, yakai kimanin minti talatin tsaye a gurin sannan Daga bisani ya shiga motarsa ya tafi, jikinsa ba laka ko kad'an. Tana shiga gida, ta wuce d'aki kan gado ta fad'a ta fashe da wani irin kukan takaici, kuka take baji ba gani. Daga waje kuma anata sallama, amma batajiba, saboda kukan yinsa take tsakaninta da Allah. Jitayi ba'ada niyyar amsa sallamar data dad'e tanayi, saboda haka kutsa kai tayi cikin d'akin, dan tanada tabbacin Hajiya bata nan. Autar Hajiya datayi nisa cikin kuka, sai ji tayi an dafata, da sauri ta d'ago da manyan idanunta da suka canja zuwa ja saboda tsananin kuka, sadiyya tagani wacce batasan lokacin data shigo gidan ba. Cikin tsananin damuwa sadiyya, ke magana, "kawata, meya faru? Naganki cikin wannna yanayin. Bata tanka mataba, illah cigaba datayi da kukanta. Zee Elkaseem Mmn khady [30/07 7:37 pm] .: 🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊 *AUTAR HAJIYA* 💃🏻 🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊 ®NWA 👇🏻 _ZEE MMN KHADY_ 😘 _Page_ 21-25 ✍🏽 Sai da tayi kuka me isarta sannan ta d'ago ta kalli sadiyya, wacce ta kasance 'kawa ce gareta, tin suna yara kuma bata da wata aminiya data wuce ta. Nan tabata labarin duk abinda yafaru, tin zuwan Adam dakuma Abinda babanta ya fad'a na cewa idan bata fito da miji ba ze za6a mata duk wanda yaga yayi masa. Sadiyya ta numfasa, sannan tace "wallahi Autar Hajiya kinada problem, ni narasa gane kanki, kwata-kwata tinda nake ban ta6a gani ko jin me irin wannan tsatstsauran ra'ayin ba irin naki, be kamata ace kin kartake akan ke bazaki auri me mata ba, ki duba kiga kwanaki yanda kukayi soyayya da Bashir kamar bazaku ta6a rabuwa ba, ba irin tsantsar soyayyar dabaki nuna
Table of Contents