Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 8

Chapter 8

Autar Hajiya Book 1 Complete Hausa Novel 1,201 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

suke gani. Mmn khady [03/08 10:51 pm] Zee Elkaseem: 🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊 *AUTAR HAJIYA* 💃🏻 🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊 ®NWA 👇🏻 _ZEE MMN KHADY_ 😘 *_Page_* 76-80 ✍🏽 washe Gari da misalin karfe biyu na rana, dubban mutane suka sheda d'aurin Auren khaleed da Amarensa, Zainab _(AUTAR HAJIYA)_da Fadila. Da misalin 'karfe hud'u na yamma aka fito da Auta dan kaita gidan mijinta, bayan an kaita d'akin mahifinta yayi mata nasiha me ratsa jiki, da kuma yimata nuni da tayi ha'kuri, dan duk Wanda yayi ha'kuri duniya baze ta6a ta6ewa ba. Bayan an fito da ita daga d'akin mahaifinta aka wuce da ita d'akin Hajiya, itama Hajiya tayi mata nasiha me ratsa jiki, 'karfe hud'u da rabi aka fito da Auta aka sakata mota, ba abinda take sai kuka, da kyar aka rabata da hajiya, A unguwar lay out dake cikin garin katsina, misalin 'karfe biyar suka isa gidan, can suka iske 'yan'uwan khaleed dana Fadila dan ita tin 'karfe hud'u aka kawota. Bayan sallar magrib ne aka fara gabatar da walimar da 'yan'uwan khaleed suka shirya, wanda aka gayyato shahararriyar malama wacce zata gabatar da wa'azi kan zaman aure da kuma nasiha ga Amare, wato malama *AMINA ALIYU MOHM'D (BINTUSH~SHEIKH)* Bayan malama ta bud'e taro da Addu'a, tayi wa'azi akan ha'kuri sanna tafara nasiha ga Amare kamar haka: "Alhamdulillahi Allah Kaine abin godiya, daka azurtamu da rai da lafiya, bayan wa'azi da nayi akan ha'kuri yanzu kuma inaso inyima Amare nasiha akan zaman Aure, Wanda shima dai ha'kurin akeyi, yaku wad'annan Amare ina ro'konku da kada kuyi kishi irinna jahilai, kada kuyi kishi irinna wad'anda basu san ciwon kansuba. Kuyi kishi irinna matan Annabi Muhammad _(S.A.W.)_ Kada kuyi kishin da ze tada hankalin mijinku, kuyi kishi Wanda kullum burinku Ku kyautatama mijinku, kunsan shi rai yana son me kyauatata mashi, sannan daga 'karshe na horeku da tsafta, Ku zamto masu tsafta kada ku yarda mijinki yaga wata 'kazanta ajikinki ko ya sha'ki wani abu a jikinki sa6anin daddad'an kamshi. Haka dai malama tayi nasiha me ratsa jiki, daga 'karshe aka rufe taro da addu'a Kowa ya tafi gida, bayan an raba sadakar Qur'an Kowa izif sittin, Ana Allah shima malama Albarka, Akan wannan wa'azi datayi. Da misalin 'karfe takwas na dare, gida yarage daga Auta sai 'kawayenta guda biyu sadiyya da Zahra'u sune suka tsaya suka gyagayara mata kome suka share ko'ina suka kunna turaren wuta, ko'ina na sashen ya bige da 'kamshi sannan sukayi bankwana suka tafi. Itama Fadila 'kawayenta ne suka tsaya sukayimata 'yan gyare-gyaren daya dace, sai misalin karfe tara da rabi suka bar gidan, *TO FAH MASU KARATU GIDA YA RAGE DAGA AUTAR JAJIYA SAI FADILA• 🤔 SAI ALLAH YA KAIMU GOBE MUJI WACE IRIN WAINA ZASU TOYA*😂 Mmn khady [10/16, 7:55 PM] ‪+234 816 616 9254‬: [04/08 8:00 am] .: 🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊 *AUTAR HAJIYA* 💃🏻 🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊 ®NWA 👇🏻 _ZEE MMN KHADY_ 😘 _*Page*_ 81-85 ✍🏽Da misalin karfe goma da minti arba'in da biyar basuji shigowar ango ba, dama kowace na d'akinta, kasancewar gidan irin plate house ne, farko idan ka shigo get d'in ka wuce harabar gidan akwai 'kofa waccce zata sadaka da general falo na gidan, cikin falonne 6arin dama d'akin Autar Hajiya yake, Wanda ya kasance cikinsa akwai falo d'aya sai bedroom guda biyu, a 6angaren hagu kuma d'akin fad'ila ne, itama kamar yanda na Auta yake, sai d'akin me gida khaleed da yake tsakiyar nasu d'akunan shikuma falo ne da bedroom d'aya, kowane da toilet cikin bedroom d'insa, daga side din kowace kuma kitchen d'inta yake. Fadaila ce ta kalli agogon dake manne jikin bangon d'akinta, 'karfe sha d'aya saura minti biyar amma bataji shigowar ango ba, saboda haka toilet ta shiga ta she'ka wanka, bayan tafito ta d'auko wani tsadadden less ta sa, bata tsaya d'aura d'ankwaliba, bayan ta tsara make-up yafa d'ankwalin kawai tayi a kai, sannan ta fito general falo ta zauna jiran shigowar angonta. Auta kuwa itama tana d'akinta ta gaji da jiran shigowar ango, saboda haka, itama wanka tashiga, bayan ta she'ka wanka, ta fito, ta tsaya gaban dressing mirror tana tinanin me ma zatayi, yanzu dai kam batada lokacin yin make-up da wannan daren, lotion kawai tashafa me d'adin kamshi, sannan ta feshe jikinta da turarruka masu kyau, tanufi wadrope ta d'auko rigar baccinta, ta Sanya, tsayawa tayi tana kallon kanta, yanda rigar tayi mata, sharara tamkar batasa kome ba, dan duk illahirin surar jikinta bayyane take, tayi niyyar canja riga saboda tana kunyar khaleed yashigo ya ganta haka, amma kuma tana jin zafi-zafin da ake a garin, saboda haka tace bari ta d'an sha iska, idan taji shigowarsa sai ta caja, gado ta haye,ta kwanta lamo, zuciyarta cike da tinani kala-kala, daga nan bacci yayi awon gaba da ita. Karfe sha d'aya da rabi khaleed yayi horn Bakin get d'in gidan me gadi ya bud'e mashi yashiga,. Fadila na zaune Falo saboda haka, da sauri tanufi d'akinta ta 'kara shafa humra, me dad'in 'kamshi sannan ta dawo falon ta zauna. Da sallama ya shigo falon, cikin kashe murya Fadila ta amsa salamar, tare da mi'kewa ta rugomeshi tayi Mashi sannu da Zuwa sannan ta kar6i ledar daya shigo da ita ta ajiye gefe. d'akinsa ya nufa tabishi, acan ta had'a mashi ruwan wanka, sannan ta taimaka Mashi ya cire kayan jikinsa ya shiga wanka, bayan ya fito daga wanka, wasu 'kananan kaya ya sanya masu sakai-sakai, sannan ya umarci Fadila da ta tashi suje falo. Bayan sundawo falo sun zauna, khaleed ya umarci Fadila data d'auko ledar daya shigo da ita, ta tashi tana wani yanga tana karairaya, ta d'auko ta ajiye, sannan ya umarceta ta d'auko plate da cup's, kitchen tanufa ta d'auko duk wani Abu datasan zasu bu'kata. Tana fitowa daga kitchen d'in taga ba khaleed, bata kawo kome a ranta ba, tana tinanin yana d'a'kinsa, saboda haka zama tayi tana jiran fitowarsa, amma har kusan minti talatin be fitoba, saboda haka d'akinsa tanufa, da sallam ta Shiga d'akin amma saitaga ba Kowa ciki, sai tayi tinanain koyana toilet ne, Bakin 'kofar toilet d'in ta kanga kunnenta bataji alamar mutum aciki ba, Ahankli ta tura 'kofar toilet d'in nan ta'kara tabbatar da baya ciki. Take zuciyarta ta ayyana mata inda khaleed yake, a fili ta furta *~Wallahi bazan yarda ba~* Zee Elkaseem Mmn Khady [04/08 11:19 am] .: 🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊 *AUTAR HAJIYA* 💃🏻 🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊 ®NWA 👇🏻 _ZEE MMN KHADY_ 😘 *_page_* 86-90 ✍🏽 khaleed kuwa a lokacin daya umarci Fadila data d'auko plate kitchen, tana shiga kitchen d'in da sauri yanufi d'akin Auta , dan tunda yashigo hankalinsa na gun d'akinta ko zata fito amma shiru bata fitoba. Ahankali ya tura 'kofar d'akin kwance ya hangota kan katafaren gadonta wanda yasha shimfid'a da wani 'katon bedsheet, da manyan filo da 'kanana. Baccinta take cikin nutsuwa da kwanciyar hankali, ahankali ya isa Bakin gadon ya tsaya yana k'are mata kallo, kaf surar jikinta bayyane take, ga fitila d'akin kunne haske fayau ko'ina, lokaci guda yaji jikinsa yafara kyarma, besan lokacin daya hau kan gadon ba ya rungumota jikinsa baki d'aya yafara shafata, yakai hannunsa kan kirjinta yafara wasa da dukiyara fulaninta. Cikin bacci tajita jikin mutum, gashi kuma anata romancing d'inta, cikin firgici ta bud'e idonta khaleed tagani ya 'kura mata ido baya ko 'kiftawa, ta bud'e baki tana shirin

Table of Contents

Chapters

20 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});