Chapter 16
Chapter 16
ta, hannunta ri'ke da wani 'karamin cup, dining tanufa inda fadila tagama jera kayan break fast d'insu, ta bud'e, plask d'in dake d'auke da kunun gyad'a wanda yaji peak milk yayi fari 'kar, ta zuba abinda ke hannunta cikin cup, ta d'aga plask din tad'an jijjiga yanda ze gauraye kada a gane anzuba wani abu daga baya, tayi saurin komawa d'akinta. Zazzaune suke kan dinning kowane da cup me d'auke da kunun gyad'a a gabansa, dankalin da kwai suka fara ci saboda kunun akwai zafi, Khaleed ne yafara d'aukar cup din gabansa yakai baki, dan yana sauri yafita aiki dan yau yanada patient's dayawa a hospital, Wani irin d'and'ano yaji na daban, cikin kunun Wanda ko a mafarkin baya tinanin jinsa cikin kunun, Cike da 6acin rai ya kalli Fadila, ya daka mata harara tare da Jan wani irin dogon tsaki "Mtswww, Fadila bata kai ga fara shan kununba saboda haka batasan yanda testing d'insa yakeba, cike da 6acin rai tatashi tafara magana tana d'aga murya "gaskiya khaleed nagaji da cin mutunci da cin zarafi dakakemin cikin gidannan, shikenan ni kullum nice abin wula'kantawa dan kana ganin wannan kod'dad'iyar yarinyar tare da kai..... Kafin ta ida rufe baki, sai jin abu tayi ajikinta, wata irin 'kara ta saki dan kunun yanada sauran zafi, zuciya takai khaleed ya watsa mata shi, cike da masifa yatashi yana cewa "ke har kinada bakin dazakice anyi maki rashin adalci, kenan adalcinne yasa zaki zambad'a mamu uwar kanwa cikin kunu, wannan kanwar da kika zabga ko kunun kanwa aka zubamawa baze shawuba, barantana kunun gyad'a wanda beda had'i da kanwa. Sai lokacin Auta tayi magana, tace kayi ha'kuri mijina, kayimata uzuri, wata 'kila da kunun kanwa zatayimana, kasan shima yanada dad'i sosai. Bebi takansuba suduka, cike da 6acin rai ya d'auki makullin motarsa yafita, Har yabar falon Fadila na tsaye gurin kamar an dasata, ba abinda take sai zubar da hawaye, Auta ta tashi ta kalli fadila, datayi tsaye da kunu ajiki, har ga Allah tabata tausayi, amma kuma koma miye ita ta fara, Dariya tayi, tace *"Kije ki wanke*, tashige daki tana cigaba da dariyarta, har Fadila na jiyo sautin dariyar. Haka Fadila ta tattare rigar tanufi d'akinta, tacire, sannan tafad'a toilet ta sakarma kanta showar, bayan ta gama wankan ta dad'e toilet tana kuka. Bayan tagama wanka ta sake shafa lotion me dad'in 'kamshi, ta saka wasu kaya. Auta kuwa tana d'akinta ta kwanta ruf da ciki kan gado, tana danne-danne cikin wayarta, kawai jitayi kamar alamar mutum a kanta, da sauri ta d'ago takai dubanta kan Fadila wacce ke tsaye tana cika tana batsewa. Take wani irin mugun tsoro yakama Auta,dan ganin Fadila yau har cikin bedroom d'inta, tasan idan za'a barta da Fadeela sai dai taci na jaki. *_innalillahi'wa,inna'ilaijirraji'un_* tashiga furtawa duk illahirin jikinta kyarma yake, gashi ba kowa gidan daga ita sai Fadila. ```Su Auta anbani ga tsoro ga jan fad'a 😂 nidai zee barin gidan nayi dan bazan raba wannan fad'an ba, tsuntsun dayaja ruwa shi ruwa kan doka``` 😄 Zee Elkaseem Mmn khady [10/16, 7:55 PM] +234 816 616 9254: [13/08 5:47 pm] .: 🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊 *AUTAR HAJIYA* 💃🏻 🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊 ®NWA 👇🏻 _ZEE MMN KHADY_ 😘 ```Page``` 151-155 ✍🏽 Tafiya yake a mota amma zuciyarsa cunkushe da tinani kala-kala, saida yakusa kaiwa asibiti, ya tuna da ya manta wasu muhimman takardu wanda yau ne yakamata yaje dasu, Juya akalar motar yayi, ya koma gida, me gadi yatashi da Sauri ze bud'e mashi get, amma sai ya tsaidashi, yace" kabarsa kawai zan ajiye anan dama wata yar mantuwa nayi zanshiga na d'auko, me gadi ya russuna yace "to ranka ya dad'e. Shiru ya iske falon alamar matan gidan kowace na 'dakinta, sallama yayi sannan yashiga, d'akinsa ya wuce kai tsaye, Auta kuwa tana kan gado ido ya raina fata, ga fadila na tsaye bata dai tankamata ba, kuma batada niyyar barin d'akin, Cikin sa'a Auta tajiyo sallamar khaleed a falo, wanda ko kad'an fadila bata jiba, kodan tana cikin 6acin raine, oho 🤔 Saukowa tayi daga kan gado, tazo gaban fadila ta kama wuyan rigarta tacimata kwala, sannan ta kwanta kasa ta fasa ihu tana cewa "dan Allah kiyi hakuri, wayyo nashiga ukku zata kasheni, menayimaki zaki kama dukana, wayyo Hajiya kizo zata kasheni, iya karfinta take maganar cikin murayar kuka tana kuma buga 'kafarta jikin gado da bedside, sannan kuma takama wuyan rigar fadila ta ri'ke sosai, hakan yasa dole fadilar ta duko yanda idan kagani sai kace dukanta takeyi da gaske. Fadila kuwa mamaki ne yagama rufeta, tanata kokarin 6am-6are wuyar rigarta daga hannun Auta amma ta kasa, saboda Auta ba 'karamin ri'ko tayi mataba. Khaleed na d'akinsa yana tattara takardun dayazo nema, yajiyo ihun Auta tana Neman taimako, aiko da hanzari yanufi d'akinta dan ganin abinda ke faruwa. Fadila yagani duke kan Auta, itakuma tana kwance 'kasa tana Neman taimako, da sauri ya Isa gurin ya jawo fadila da iya karfinsa, wadda ganinsa yasa Auta tasaketa daga sha'karar datayimata, Wani lafiyayyen mari ya d'auketa dashi, Fadila tayi saurin dafe gurin daya mareta, zatayi magana ya'kara d'auketa da wani lafiyayyen mari, yana huci yace "bakida hankali fad'ila zaki kama 'yar muatne da duka haka, so kike ki kasheta. Lokacin kuma Auta ta tashi daga Inda take kwance tayi wujiga-wujiga, fuskar nan sharkaf da hawaye, idan ka ganta saika rantse kace mugun duka akayi mata. Fad'awa tayi jikin khaleed tana kuka, shikuma ya rungumeta yana rarrashinta kamar wata yarinyar goye, sannan ya maida dubansa ga Fadila wacce ta dafe kunci tana zubar da hawayen takaici, Yafara bal-baleta da masifa, ta inda yake shiga batanan yake fitaba, iya tsawon rayuwar Fadila bata ta6a sanin khaleed nada fad'a haka ba sai yau. Bayan yagama zazzagamata bala'i sannan ya nuna mata Kofa yace *(Get out)* ki fita nace daga d'akinnan tin kafin inyimaki mugun bugun dazaki kasa tashi, sha-sha-sha wacce batasan girmantaba, in banda sakarci me zaki daka jikin Zainab, Ki duba girmaki ki duba nata, kin kai biyunta, duk maganar nan dayake Auta na rungume jikinsa tana kukan shagwa6a. Haka fadila tabar d'akin cike da takaici, tana mamakin yanda Auta ta Jamata sharri cikin 'kan'kanin lokaci. Babban falo ta zauna tana sharar hawayen ba'kin ciki, Kusan kimanin minti talatin Fadila na zaune falo tana kuka, sannan khaleed yafito shida Auta,yana mata magana wacce fadila batajin me suke cewa amma dai taga Auta na dariya hadda kyalkyatawa, Saida sukazo gab da ita khaleed ya kalleta ya buga mata wata uwar harara, yace "gatanan zan tafi gurin ayki, idan kin isa' kin haihu ga iyayenki, kuma kin isa marar mutunci to in dawo in iske gawar Auta a gidannan, yabuga wani dogon tsaki "mtswwww sannan ya wuce, tare da ba Auta lafiyayyen kiss a kumatu yace saina dawo matata, *(Tak care of your self)* ki kulamin da kanki, wani lafiyayyen murmushi tayi mashi tace *(never mind my husband)* karka damu mijina. Haka tarakashi har bakin get saida taji 'karar tashin motarshi Alamar yatafi, Sannan takama hanyar komawa cikin gidan. Saida tazo 'kofar shiga falon tatsaya tana tinani, "{```Yanzu idan nashiga Fadila takamani ba abinda ze hana ta rama marin da nasa akayimata, me sau'ki kenan idan batayimin d'an banzan duka ba}``` Tsayawa tayi tana shawarar yanda zata shiga d'akin, ga kuma fadila zaune.
Table of Contents