Chapter 13
Chapter 13
ya zaunar da ita yanamata sannu, ita kuma sai wani langwa6ewa take, tana lumshe ido, Fadila ta kalleta cike da jin haushi, amma sai ta daure dan bataso a d'ago da ita, tace "sannu dama bakida lafiya ne? Auta tace lafiyata lau, kifin da akasa agirki ne 'karninsa yayi yawa shine ya tayarmin da zuciya, Fadila ta ta6e baki ta samu gu ta zauna, a zuciyarta tana cewa ```lallaima yarinyar nan nizakima duniyanci kice wai bakison kifi sau nawa ke kikeyin girki da kifin akwai dai inda kika dosa```. Auta kuwa 'kara narkewa take tana wani shagwa6ewa, 'karshe ta kwanta kan kujerar datake tayi filo da cinyar khaleed, Shikuwa sai wani rarrashinta yake yana tarairayarta, "sorry my dear ki daure kici abincin bekamata dan kinyi amai ki zauna da yunwa ba. Cikin shagwa6a Auta tace " nidai banison wannan ka siyomin wani, tunda yanzu ba time d'in da zan girka wani, yace "fad'i mi kikeso in sayo maki, cikin shgwa6a tace ka siyomin kome kaga ze Sani farin ciki, yace "kada ki damu my only ina zuwa, makullin motarshi ya d'auka yafita, be kobi takan Fadila ba wacce tacika tayi fam saboda takaici. Zee Elkaseem Mmn khady [11/08 11:44 am] .: [11/08 10:19 am] .: 🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊 *AUTAR HAJIYA* 💃🏻 🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊 ®NWA 👇🏻 _ZEE MMN KHADY_ 😘 ```Page``` 126-130 *_BAYAN KWANA BIYU_* ✍🏽 Auta ana kitchen anata faman girki, yau tasha Alwashin tsayawa tsayin daka tayima mijinta abinci wanda ze faranta ranshi, wanda zesa ya manta duk wani 6acin rai na baya, kuma ya dawo da tsananin so da 'kauna da kulawar dayake mata. Sakwara tayi niyyar dafa mashi da miyar agushi, saboda haka doyarta me kyau ta fere ta d'ora kan wuta, sannan ta dora miya kan wani stove kusa da doyar, bayan ta kammala sakwarar ta maida hankalinta kaf gurin miyar, cikin 'kan'kanin lokaci ta kammala miyar ta juye kome cikin wasu kuloli masu Khan gaske, fridge tanufa da niyyar ta d'auko abarba domin yau *(pineapple juice)*lemun abaraba tayi niyyar had'a musu, tana bud'e pridge din kuwa cikin rashin sa'a saitaga ashe batada sauran abarba, sai lokacin ta tuna aahe fa ta kare tin bayan kwana biyu datayi lemun da ita. 'Dakinta tanufa ta dauko karamar hijab ta sanya sannan tanufi harabar gidan da niyyar taba me gadi ya siyo mata Abarba, Zaune ta iskeshi kan benci yana ri'ke da yar rediyonshi yana sauraren labaran duniya, cike da ladabi ta gaidashi sannan ta bashi sa'kon ba musu ya kar6a yafita ya siyo mata, dayake kusa da su akwai wurin da ake saida kayan fruit. Data tashi dawowa sai bata biyo ta babbar kofar falon ba, ta baya ta biyo hanyar da zata sadata da kitchen d'inta kai tsaye, tazo dai-dai window kitchen dinta kamar ance tayi duba gurin, Wani irin mummunan fad'uwar gaba taji dan ganin abinda ke faruwa a kitchen d'inta. Fadila tagani da kullin gishiri cikin leda ta bud'e had'ad'd'iyar miyar agushinta wacce keta zuba 'kamshi ga nama zud'u-zud'u aciki tsoka zallah tayi amfani da ita gurin yin miyar. Aiko da sauri Auta takoma baya ta la6e dan taga ikon Allah, Gani tayi Fadila tasa cokali ta ebo gishiri ta zuba cikin miyar ta 'karo wani cike da cokali ta juye, saida ta zuba cokali biyar ciakakke sannan tasa cokali ta motse, Ta kulle ledar gishirinta ta kakka6e hannunta tayi saurin barin kitchen d'in. Cike da mamaki Auta ta shigo kitchen d'in, ta bud'e miyar tasa cokali ta motsa lokacin gishirin yagama narkewa cikin miyar, saboda haka zubar da miyar tayi ta ta d'ora wata cikin 'kan'kanin lokaci tagama had'a wata sabuwar miyar ta gama kome ta had'a lemun abarba, tasaka pridge sannan ta gyara ko'ina na kitchen d'in, 'Daki ta wuce ta fad'a toilet ta she'ka wanka, bayan tafito simple kwalliya tayi sannan ta d'auko riga da siket na atamafa ta sanya ta dauko turare ta feshe jikinta dashi, tafito falo sai 'kamshi take bugawa, sannan ta d'auki makullin kitchen d'inta tafita zuwa kitchen d'in, dan tin lokacin dataga abinda Fadila tayimata data gama girkin ta kulle kitchen d'in ta tafi da makullin d'akinta. Bayan tagama jera kome kan dining, lokacinne kuma khaleed yashigo gidan, cikin murna dajin dad'i Auta ta tarbeshi tayi Mashi sannu da zuwa, ciki-ciki ya amsa, sannan ta kar6i jakar hannunsa tayi gaba zuwa d'akinsa shikuma yabi bayanta, bayan ya rage kayan jikinsa suka fito zuwa falo Sun zauna kan dining Auta ta zuba ma Kowa ta ajiye gabanshi, lokaci guda 'kamshin girkin ya mamaye falon, Fadila tasa hannu ta d'ebi loma guda zata kai bakinta, sai kuma ta tsaya ta kalli khaleed tace "my man , ya juyo ya kalleta, tace "nifa wallahi fargabar saka abincinnan nake a bakina, saboda kasan gishiri yana iya yima mutum lahani, kasan fa da mutum ya d'ibgama cikinsa gishiri 'kara yaci ba dad'i. Auta tayi murmushi tace "Fadila kici mana kiji, idan kikaji gishirin yayi yawa ai baza'ayi maki dole akan sai kinci ba, sannan ta kalli khaleed tace "my dear kaci abincinnan hankalinka kwance, nayima Alkawarin daga yanzu kagama jin wani aybu cikin abincina, wancan lokacinma matsala ce aka samu amma yanzu kome yakoma normal inshaAllah. Khaleed bece kome ba, sai dai ya ebi abincin ya kai bakinshi cike da fargabar irin testing d'in dazeji, Cike da mamaki khakeed ya ida saka abincin bakinsa, dan wani irin dad'i yaji yartsa kwanyarsa. Besan lokacin daya sakarma Auta wani tattausan murmushiba, yace *Weldon* my wife, amma nayi matu'kar farin ciki dajin wannan gyara naki, gaskiya yau kin matu'kar faranta raina Allah maki Albarka ya saka miki da Aljannah, cike da jin dad'in yabata da kuma addu'ar da mijinta yayimata, tayi dariya har dimple d'inta ya lo6a tace Ameen mijina, Allah kara dan'kon soyayya tsakaninmu, yace "Ameen my wife. Cike da mamaki Fadila ta kai abincin bakinta, take dad'in abincin ya ratsa mata kwanya, batasan lokacin data cigaba da cin abincinba, dan dama su duka akwai tsohuwar yunwa tattare dasu dan tin lokacin da Fadila tafara 6ata ma Auta abinci da gishiri suka daina cin abinci su 'koshi, Domin dai ita Fadila kotayi ba sosai suke iya Ciba, saboda ba dad'in yau bare na gobe Ranar dai haka suka ci abinci cike da farin ciki da annushuwa, Sa6anin Fadila wacce ba'kin ciki yagama cika zuciyarta. ```Auta dai tagano Fadila ce me 6ata mata abinci, amma kuma bata tanka mataba kuma bata nuna 6acin ranta ba``` *_Kome take nufi da hakan kubiyo zee mman khady dan jin yanda za'a kwashe tsakanin Auta da Fadila_* Zee Elkaseem Mmn khady [10/16, 7:55 PM] +234 816 616 9254: [12/08 3:00 pm] .: 🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊 *AUTAR HAJIYA* 💃🏻 🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊 ®NWA 👇🏻 _ZEE MMN KHADY_ 😘 ```Page``` 131-135 ✍🏽 "Haba 'kawata aini wallahi bayi fushi dake, ace tunda aka kawoni gidannan sai yau kika tuna dani, Sadiya tace "Ayimin afuwa wallahi kinsan hidimomi idan sukayima mutum yawa sai ahankali, Auta ta harareta cikin wasa tace "kinjiki ko, ke har wata hidima ke gareki kamar wata me iyali, Sadiya tace "ay iyalin ake niyyar yi shiyasa hidimomin suka fara tun yanzu, "Hakane fa yau saura 3 week's koh? Sadiya tace "au tambayata ma kike, duka yaushe mukayi waya dake na gaya maki. Haka sukacigaba da firar yaushe gamo, nan Auta ke tamabyar ta "waini ina
Table of Contents