Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 6

Chapter 6

Autar Hajiya Book 1 Complete Hausa Novel 1,200 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

d'akin kuwa khaleed na ganin fitar iayensu yafara rarrashin auta, yana nuna mata irin sonda yakemata, Amma ko kallo be ishetaba, Ahankali ya matso ya dur'kusa kusa da gadon datake kwance, ya marairaice, cikin sigar rarrashi yake magana. "Haba Zainab ki yarda dani, ki yarda da son danike maki, duk duniya ba macen danikeso kamar ke,.... A fusace ta d'ago ta kalleshi cikin tsiwa tace "Akwai khaleed, na tabbata kafi son Fadila a kaina, khaleed ka ha'inceni, ban ta6a tinanin ko a mafarki zakayi mani haka ba. Ya salam...ki fahimceni Zainab, Fadila fa bani nace ina sontaba, had'in iyaye ne,kuma ke.... "Dakata khaleed, bakada kalaman dazasuyi tasiri akaina, ka adana kalamanka, wata kila suyima amfani nan gaba.... _(Hmm zainabu kenan halinki sai ke)_ *Zee Elkaseem* *Mnn Khady* [02/08 6:26 pm] .: 🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊 *AUTAR HAJIYA* 💃🏻 🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊 ®NWA 👇🏻 _ZEE MMN KHADY_ 😘 _Page_ 56-60 ✍🏽 Kwanan Autar Hajiya biyu aka sallamota daga asibiti, duk ta wani rame ta kod'e hancinnan ya'kara tsayi, ga wani haske data 'kara, idan ka ganta sai kayi tinanin tayi ciwon wata biyu ne, dan ba 'karamar rama tayiba, duk tsabar kishine kawai. Ranar sukayi waya da 'kawarta sadiyya, tace dan Allah tazo yau tana son ganinta, sadiyya tace "lafiya dai? Auta tace "lafiya lao kizo mana akwai labari 'kawata wallahi ina cikin tsananin damuwa da ba'kin ciki, cikin rud'ewa sadiyya tace "Damuwa 'kawata?, wace irin damuwa kuma? Auta tace "kedai sai kinzo kome kenan kinji. ••••••••••••••••••••••••••••••••• Sanye take cikin doguwar riga ta atamfa kalar sararin samaniya, wacce tasha d'inkin zamani, dinkin ya matu'kar kar6ar jikinta, dan ba karamin kyau yayi mataba, bata d'aura d'an kwaliba, sai wani karamin gyale me sharara ta yafa akanta, amma hakan baze hana ka hango madaidaicin gashinta ba Wanda yasha 'kuna, tayi parking dinsa tsakiyar kanta. Wankan tarwad'a ce, amma dayake tana amfani da cream da lotion masu tsadar gaske masu matu'kar gyara fata,hakan ya 'kara fito da hasken fatarta, tanada idanu madai-daita, da dogon hanci, Wanda yayi dai-dai da matsakaicin bakinta, Wanda yasha romantic red colour, kallo d'aya zakayi mata ka tabbatar da boko ya zauna jikinta, da kwalwarta, *Fadila kenan*. Da sallama ta shiga falon da akayi Mashi masauki, tafiya take cikin yanga da karairaya, Lokacin khaleed ya d'ago ya kalleta tare da amsa sallamarta, Yanda take tafiya baya birgesa ko Alama, dan tanada 'yar'kiba shiyasa tafiyar bata mata kyau, ga Allah ya hore mata manyan nonuwa kamar me shayarwa. Sannu da zuwa angona, tafad'a tare da zama kan kujerar dake kusa dashi, hannu tasa ta d'auki sauran lemun dayasha cikin cup d'in glass ta kur6a sannan ta ajiye, ta maida kallonta gareshi, tare da tambayarshi, "ya hidima? Yace "Alhamdulillah, My dear lefe yayi kyau amma ka manta, da sarkar gold d'in dana fad'ama ba irin wacce ka sako bace, inaso dan Allah ko zaka musanyo mani ne?....... "Ke Fadila, cikin d'aga murya yafad'a, idan bazaki iya amfani da abinda kika gani acikiba, to ba'ayimaki dole ba, nidai namaki iya 'kok'arina......... Daga mashi hannu tayi, cikin d'aga murya take magana, "Dakata khaleed, bazakaje wata ta 6ata maka raiba kazo ka huce kaina, ko kana tinanin banida labarin abinda ke faruwa, tsakaninka da wannna yarinyar, Auta take ko miye..... A fusace ya mike tsaye, yace ni zan wuce, ba wannan ya kawoniba, zowa nayi inji idan kina bu'katar wani abu, kuma naji bakida bu'katar kome sai anjima, Ya fita Daga falon yanufi harabr gidan inda ya ajiye motarsa, yana niyyar Shiga yaga mamar Fadila, direba ya sauketa, ta dawo daga Unguwa, nan ya gaisheta, ta tambayeshi momynsa, yace tana lafiya, sannan ya shiga motarsa ya wuce. Zee Elkaseem Mmn khady [10/16, 7:55 PM] ‪+234 816 616 9254‬: [03/08 10:20 am] .: 🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊 *AUTAR HAJIYA* 💃🏻 🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊 ®NWA 👇🏻 _ZEE MMN KHADY_ 😘 _Page_ 61-65 *_Bayan sati biyu_*• ✍🏽 Yau sauran sati d'aya bikin khaleed da Autar Hajiya da kuma Fadila, duka 6angarorin guda ukku shirye-shirye suke, ko'ina ka gani suna cikin farin ciki. Amarya Fadila ansha gyara anyi fresh, dan tin ana saura sati biyu bikin take faman gyara kanta, duk wani Abu datasan yana da amfani a jikin mace tana amfani dashi, tin Daga kayan gyaran jiki zuwa kayan tsumi ba Wanda batayi. 6angaren Autar Hajiya kuwa kullum ba abinda take sai tinani, duk tabi ta rame ta kod'e tayi wani irin fari, idanunta sun kara fitowa, a haka dai aketa shirin biki, 6angaren Hajiya kuwa ba irin rarrashin da batayima Auta ba, haka babanta tin yana mata fad'a har ya dawo yana rarrashinta yana mata nasiha, da haka dai aka samu tad'an saki jikinta, aka cigaba da hidima. A 6angaren khaleed kuwa shima hidima yake sosai shida abokaninsa, zuciyarshi fal da farin ciki, dan jiya yaje gurin Autar Hajiya ta saki jiki sunyi magana ta fahimta, wacce rabon daya samu haka tin ranar da tasan ze auri Fadila. Ana saura kwana biyu d'aurin aure sadiyya tazo gidan su Auta, da sallama ta shigo, gidan cike yake da 'yan'uwa da abokan arzi'ki, bayan ta gaisheda mutanen dake tsakar gidan, sannan ta wuce kitchen inda ta hango Hajiya tana faman had'a wasu kaya, tace "Hajiya ina wuni, Hajiya ta amsa da "lafiya lao sadiyya, ya mamarki, tace "lafiya lao tace a gaiaheki, kuma tace abaki hakuri bazata samu zuwa yau ba sai zuwa gobe, saboda tayi ba'ki, cikin fara'a Hajiya tace "ba kome wallahi Allah kaimu goben, sadiyya ta amsa da Ameen, sannan ta tambaya, "ina Autar take? Tana d'aki ki isa, tana ciki. Kwance take kan godo ta juya fuskarta ta kalli bango, tayi lamo kamar me bacci, muryar sadiyya taji tana cewa "Amarya bakya laifi koda kin kashe d'an masu gida...... Auta tayi kamar bata jita ba, dan ko motsi batayiba, daga inda take kwance, sadiyya ta matso kusa da ita ta zauna gefen gadon, takara magana karo na biyu, "Amarya......., nan ma shiru Auta tayi mata, sadiyya ta'kara magana karo na ukku cikin jin haushi ta kaimata duka, tare da fad'in Auta banison rainin wayo, ya inata maki magana zaki wani sahareni...... Da sauri Auta ta tashi zaune tana Sosa inda sadiyya ta doketa, tana murmushi, tace "ina jinki wallahi, abinne naki yabani haushi da kika kirani amarya, aini nafi 'karfin amarya sai uwar gida, sadiyya tayi dariya tace to ai kinsan dai Fadila ta girmeki saboda haka itace babba, kuma itace uwar gida kekuma amarya, Auta tace "tab wallahi bazan yardaba, badai ance d'akin wacce yafara kwana ba itace uwar gida, to wallahi d'akina ze fara kwana. Sadiyya ta kyalkyale da dariya, dan ita yanzu rigimar Auta dariya take bata,tace "to yanzu ba wannan ba kitashi muje gurin gyaran jiki, Auta tace "ke nifa na gayamaki ba wani gyaran da zanyi, a kaini haka yanda nake, wallahi sadiyya konayi niyyar yin wani Abu da natuna ba nikad'ai za'a kai gidan khaleed a matsayin matar saba sai inji duk na sire, Sadiyya tayi murmushi, tace "Hmm auta kenan, to ay yanzu yakamata ki gyara, dan na tabbata ita waccan bazata zauna hakaba, kema dagewa zakiyi, ki gyara kanki yanda koda kin jera da waccan aga kamar sarauniya da baiwarta. Suduka suka kwashe da dariya, haka sadiyya ta rarrashi 'kawarta harta yadda sukaje gurin saloon, Daga nan suka wuce gurin 'kunshi, Basu dawo gida ba sai gab

Table of Contents

Chapters

20 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});