Chapter 7
Chapter 7
da magrib, suna dawowa, sadiyya tayo Alwala ta kabbara sallah, ita kuma sadiyya wanka tashiga, bayan tafito Daga wankan ta haye gado tayi kwanciyarta, kasancewar tana fashin sallah, bayan sadiyya ta idar da sallar ne suka cigaba, da tattauna yanda party da za'ayi gobe ze kasance, dan kuwa partyn Baki d'aya za'a yishi da fadila da Auta, kuma kowace da 'kawayenta. Zee Elkaseem Mmn khady [03/08 11:57 am] .: ๐๐๐๐๐๐๐๐๐ *AUTAR HAJIYA* ๐๐ป ๐๐๐๐๐๐๐๐๐ ยฎNWA ๐๐ป _ZEE MMN KHADY_ ๐ _*Page*_ 66-70 โ๐ฝwashe gari ana gobe d'aurin aure, yau ne aka shirya wani 'kawataccen party Wanda Za'ayi a liyafa parlance dake cikin garin katsina, duka a 6angarori guda ukku, kowane yana cikin shiri, khaleed da abokaninsa da 'yan'uwansa, Autar Hajiya ma da 'yan'uwanta da 'kawayenta, haka ma Fadila, tana cikin shiri itada 'kawayenta da 'yan'uwanta. Da misalin karfe hud'u za'a fara aiwatar da partyn, sabida haka kafin lokacin Fadila ta gama shiryawa, wani tsadadden material ne red colour tasanya dinkin riga da siket, kayan sun matseta sosai, abinka game jiki, kirjinnan kamar ze fasa rigar, kanta kuma golden gwagwaro ta d'ora takalmanta masu masifar tsini, wanda suka taimaka gurin 'kara mata tsawo, suma golden colour, sai wata 'karamar jaka dake hannunta itama kalar golden, kallo d'aya zakama Fadila kasan amarya ce, fuskar nan tasha make-up, dan me kwalliya ta d'auko ta musamman ta gyara mata fuskarta, ta biyata kud'i me yawa. A 6angaren Autar Hajiya kuwa zaune take itada 'kawayenta, anata labari anata shewa, ko kad'an Auta batada niyyar yin wanka barantana ta shirya, sadiyya ce ta duba agogon wayarta sannan ta kalli Auta tace, Auta kinsan kau 'karfe nawa yanzu? amma ko niyyar shiryawa bakiyiba, kafin tayi wata magana, taji 'karar wayarta, tana dubawa taga sunan Ahmad, wani abokin khaleed ne, hannu tasa ta d'auki wayar sannan ta dannan OK ta kara a kunne tare dayimashi sallama, a d'ayan 6angaren Ahmad yace Ku fito gamu kofar gida muna jiranku, Tayi saurin tashi tsaye tare da dafe 'kirji tace kuna waje fa kace, yace "eh tace "gashi kuma bangama shiri ba, yace owk bari muje gidan su Fadila, idan kingama mundawo, bejira abunda zata fad'aba ya tsinke wayar. Da sauri tashiga toilet tayi wanka, tana fitowa ta d'auko wani lotion me dad'in 'kamshi ta shafe jikinta dashi, sadiyya ce ta 6ata lokaci gurin yima Auta make-up, tin nan Auta tafara yin kyau, fuskar nan kamar wata balarabiya, ga kunshinta Wanda yayi masifar kyau, manyan Flowers ne yayi bakikirin sai Jan ranin daya 'kara 'kawata kunshin. Wani tsadadden farin Swiss less ne, Wanda yasha ado da flowers silver colour ta sanya dinkin doguwar riga, rigar ta kar6i jikinta dan ba 'karamin kyau tayimata ba, sannan ta sanya, takalmi silver colour, sai yar post d'in hannunta itama silver colour,kanta kuwa gwahgwaro me ta d'ora shima kalar silver, tayi masifar kyau, sannan ta d'auko turarurruka masu dadin 'kamshi ta feshe jikinta dasu. Sadiyya ta kalleta tace Amarya kinsha 'kamshi, Auta ta harareta, cikin wasa tace "kin manta, sadiyya tayi dariya tace "oh sorry tuba nike Amarya uwar gida, Auta tayi dariya tace "ki karani kirani Uwar gidana Kawai, Sadiyya tace "to uwar gida sarautar gida, suduka suka kyalkyale da dariya. Suna cikin wannan sukaji tsayuwar motoci, Ahmad, yakirasu yace su fito gasu a waje, nan aka fafa d'ibar 'kawayen amarya ana kaisu. Daga karshe kuma aka d'auki Auta da wasu sauran 'kawayenta dasuka rage. Zee Elkaseem Mmn khady [10/16, 7:55 PM] โช+234 816 616 9254โฌ: [03/08 9:43 pm] Zee Elkaseem: ๐๐๐๐๐๐๐๐๐ *AUTAR HAJIYA* ๐๐ป ๐๐๐๐๐๐๐๐๐ ยฎNWA ๐๐ป _ZEE MMN KHADY_ ๐ *_Page_* 71-75 โ๐ฝ Hall d'in cike yake ma'kil da 'yan'uwa da abokan arziki, tun daga kan 'yan'uwan khaleed da abokaninsa, har zuwa 'yan'uwan Autar Hajiya da kuma 'kawayen Fadila da kuma 'yan'uwanta, Kowa yayima kansa mazauni, ana jiran shigowar ango da Amarensa, Autar Hajiya da Fadila. Bayan hall din yayi shiru, sakamakon Mr DJ daya fara magana cikin speaker's dinshi, Kowa ya maida hankali ga yanda yake jawabi. Can na hango Ango khaleed da Amarensa sun jero, tsakiya suka sanyashi, Auta na gefen damarsa yayinda Fadila ke gefen hagu, suna tafiya ahankali cikin nutsuwa, kallo d'aya zakayima Auta ka fahimci tana cikin wani yanayi, dan yanda taga Fadila ta wani shishshigema khaleed ta kama hannunshi ta ri'ke abin ba 'karamin takaici yayi mata ba, tin nan tafara tinanin me zatayi ta ba'kantama fad'ila rai, kamar yanda ta ba'kanta mata. Sun Isa high table inda nan ne yazama masaukin Ango da Amarenshi, tsayawa khaleed yayi yayima fad'ila nuni akan ta wuce tafara zama kujerar can, yayinda shi tashi kujerar take tsakiya, Bayan Fadila ta wuce ta zauna kan kujerar ta, khaleed na niyyar zama kan tashi kujerar kawai sai ganin Auta yayi kan kujerar, yana shirin yimata magana ne yaji, ta kamo hannunsa, ta wani kashe Mashi manyan idanunta, tace "ka zauna mana my dear, tare da nuna mashi kujerar da itace zata kasance gurin zamanta, ba yanda zeyi haka ya zauna, sai tsarin zaman ya canja, ya kasance Autar Hajiya itace tsakiya, yayinda Fadila ta koma gefe, cikin 'kawayenta. Wani 'kululun ba'kin ciki ya tsayama Fadila a wuya, ta rin'ka cika tana batsewa, fuskar nan tata ba annuri ko kad'an duk 'ko'karin datayi na taga ta share da abin ta nuna be dameta ba kasawa tayi, Itako Auta sai fara'a take, ta dan du'ko da Fuskarta saitin fuskar khaleed har sunaiya juyo numfashin junansu, Labari tari'ka bashi shikuma dama abinda, yake nema, sabkda haka ya biye mata, dan tin lokacin da Auta tasamu labarin ze auri Fadila maganr ta minti goma bata 'kara had'asuba, Shiyasa ya biye mata sukayita labari suna sakarma junansu wani 'kawataccen murmushi. Can zuciya ta 'kule Fadila, batasan lokacin data tashi, cikin tsananin masifa, da bala'i ta fito daga ida take zaune, ta tsaya gaban tebur d'inda aka cika da kayan ciye-ciye da lemuka kala-kala, tasa hannu tafara watsi da kayan, 'karar fashewar kofunan glass d'in gurinne ya maido da hankalin duk illahirin mutanen dake gurin. Cikin tsananin mamaki Auta ta nufi Fadila, wacce idanunta suka rufe saboda tsabar masifa, ta ri'ke hannunta tana fad'in "Haba Fadila lafiya, ya muna taron arziki zakizo ki 6ata mana, cikin tsananin fushi Fadila ta bankad'e Auta, abinka ga marar jiki ta tafi taga-taga zata fad'i dai-dai lokacin khaleed ya iso gurin yayi saurin tarbeta, ta kuwa fad'a jikinsa tana kukan shagwa6a, tana fad'in "my dear menayi mata zata tureni? 'Kara rungumeata yayi jikinsa yana rarrashinta, ita kuwa sai wani 'kara narkewa take. A fusace Fadila ta nufi hanyar Barin hall din tana zubar da hawayen ba'kin ciki, Ahmad ne yabita yana cewa, "Fadila ki tsaya mana a gyara, ai bekamata kiyi hakaba, wallahi muna cikin maganar zamuyima khaleed magana agayara tsarin zaman kawai sai gani mukayi kin tashi kina wannan d'anyen ayki, cikin dusashshiyar murya tace " Ahmad ka taimakeni ka maidani gida kada zuciyata ta buga bazan iya ba. Bayanda Ahmad beyiba akan tayi ha'kuri ta koma ta 'kiya, dole tasa ya d'auketa a motarsa dan kada yabarta tatafi yanda ranta yake 6ace wani Abu yaje yafaru da ita a hanya. Haka aka tashi partyn Kowa na jimamin abinda ya faru, wasu na ganin laifin Fadila, wash na ganin laifin khaleed,wad'anda kuma suka fahimci yanda abun yake laifin Autar Hajiya
Table of Contents