Chapter 11
Chapter 11
yana 6ata rai kamar mecin magani, amma ita bata ganin laifin kowa sai na momynta dan itace bata koya mata girkiba, gashi Auta har magana take gayamata a kaikaice, wai makarantar Hajiya ta koyi girki," Hmm tayi kwafa sannan ta wuce d'akinta. Da misalin 'karfe daya da rabi na rana Auta tagama had'a kome ta jera kan dining, 'kamshin girkinta yagama buge ko'ina na gidan kamar yanda ta saba. Dambun shinkafa ne tayi me rai da lafiya, Wanda yaji kayan lambu, Kara's da kabeji da sauransu, ga kamshin kori, nama ta yanka gutsi-gutsi ta zuba gurin yin dambun ta yanda zeyi wuya mutum yayi cokali guda batare daya ci da naman ba, gefe Kuma zo6o ne tahad'a Wanda shima yayi dadi sosai yaji flavor me 'kamshin Abarba yayi sanyi dan jug d'in har ra6a yake. Bayan ta kammala wannan d'akinta tanufa ta she'ka wanka, bayan tagama gyara ko'ina na gidan da kuma kitchen d'inta, ta turare gidan da turaren wuta, abin dai gwanin birgewa. ```{ ๐kaini su Auta an iya kwanare da sa kishiya taji haushi}``` Da karfe biyu khaleed ya dawo gidan, bayan Auta tarakashi d'akinsa yayi wanka, ya canja kaya, wata 'karamar riga ce yasanya sai wando three quarter, sannan suka hallara su duka kan dining, Auta cike da nishad'i da jin dad'i ta zuba ma kowa a plate tare da sanya cokali, sannan ta tsiyayama kowa zo6o a cup d'in glass ta ajiye gabanshi, sannan itama ta zauna, khaleed cike dajin dad'i ya d'ebi abincin yakai bakinsa, tare da lumshe ido. ```Yasalam ya furta tare da saurin furzar da abincin dake bakinsa``` Lokacin itama Fadila ta kai abincin bakinta dan jin meke faruwa, da sauri ta zuddo abincin tare da saurin d'aukar ruwa tasha, dan kuwa wani irin mugun gishiri ne yayi yawa cikin abincin, dan komin dauriyar mutum baze iya cin saba. Cikin tsananin rud'ewa Auta ta ebi abincin taci dan taji meye yasa khaleed zubar da abincin data 6ata lokaci gurin girka Mashi dan ya yaba, wani irin zau taji abakinta *Innalillahiwa'inna'ilaihirraji'un* tashiga furtawa, aranta tace yaushe nayi wannan aikin haka, yaushe na zabga gishiri cikin abincina har ya wuce misali. Khaleed kuwa kasa magana yayi, dan yasan ko be fad'aba suduka sun san kome kenan, baya bu'katar a can-cana maganar. Kitchen d'in Auta yanufa ya d'ebo cake cikin plate dan kuwa yunwar jinta yake sosai, dan har gidan abokinsa Ahmad yaje akayimasa tayin abinci ya'ki ci dan yasan Auta zata yimashi special coaking ๐. Zama yayi ya fara cin cake d'in sannan ya d'auko zo6on da Auta ta zuba mashi a cup yakai bakinsa, da sauri ya cire cup d'in daga bakinshi dan jin wani sabon d'and'ano a zo6on wanda beyi tinanin jinsa acikiba, lokaci guda ya maida kallonshi ga Auta wanda mamaki yahanata motsawa daga inda take, Khaleed yagama 'kulewa da Al'amarin Auta, saboda haka batare dayace kome ba yatashi ya wuce d'akinsa, Cikin tsananin mamaki Auta ta d'auki cup d'in ta kur6i zo6on gishiri taji zau Wanda har ya zarce za'kin sugar, kalmar *innalillahiwa'inna'ilaihirraji'un* kawai take furtawa, Binshi tayi d'akinsa kwance ta iskeshi kan gado ranshi yayi matu'kar 6aci, nan tashiga rarraahinshi tana bashi ha'kuri tare da nuna mashi wallahi batada masaniya akan wannan gishirin da yayi yawa cikin abinci barantana kuma cikin zo6o. Fadila kuwa koda taga shigewarsu d'aki wata irin shu'umar dariya tayi tace ~```Hmm Auta dani kike magana```~ Zee Elkaseem Mmn khady [10/16, 7:55 PM] โช+234 816 616 9254โฌ: [06/08 10:33 pm] .: [06/08 9:42 pm] .: ๐๐๐๐๐๐๐๐๐ *AUTAR HAJIYA* ๐๐ป ๐๐๐๐๐๐๐๐๐ ยฎNWA ๐๐ป _ZEE MMN KHADY_ ๐ *_Page_* 101-105 โ๐ฝ A firgice Fadila ta farka daga baccin datakeyi da niyyar zuwa falo dan kada khaleed ya dawo ya wuce d'akin Auta bata saniba. Innalillahiwa'ainna,ilaihirraji'un tafad'a tare da saurin le'kewa ta windon d'akinta dan tabbatar ma idonta abinda ta gani gaskiya ne, Hasken ranar daya haske idonta shine ya tabbatar mata da cewa tabbas ba mafarki takeba, safiya tayi, da sauri ta fita zuwa d'akin khaleed dan taga nan ya kwana ko kuwa, tana zuwa ta tura 'kofar d'akin tashiga taga ba kowa aciki, kuma babu Alamar mutum ya kwana aciki. Take wani irin kishi ya turni'keta, "shikenan abinda ta kwana ukku tahana idonta bacci sabodashi yariga ya afku, jitayi 'kafafunta sun kasa d'aukarta, batasan lokacin data sulale 'kasan d'akinba kan tiles tayi zaman dirshan tana zubar da wasu zafafan hawaye, a zuciyarta take cewa: *_(Shikenan khaleed ka cuceni ka gama sanyawa yarinyar nan ta rainani, shikenan khaleed ka fito fili ka nuna kafi son Auta a kaina, )_* Shiru tayi na kimanin minti goma tana tunani, tana sa'ke-sa'ke a zuciyarta, zuwa can sai tayi wani shu'umin murmushi, tace *~Hmm Auta idan Kin san wata baki san wata ba "Hmm dani kike magana~* : Tashi tayi daga zaman takaicin datake, tanufi d'akinta tafad'a toilet tayi wanka sannan ta d'auro Alwala ta kabbara sallah lokacin har karfe bakwai da minti sha shidda na safiya, bayan ta idar da sallar ta wuce gaban dressing mirror ta 6ata lokaci gurin gyara fuskarta, sannan ta sharce gashinta wanda koda yaushe yake a 'kone, ta d'aure shi tsakiyar kai, bayan tagama wannan wadrop tanufa wasu Riga da siket na atamfa ta d'auko d'inkin zamani ta sanya ajikinta, kayan sun matu'kar zama ajikinta, dan ba 'karamin kyau sukayimata ba, sannan ta d'auko manyan turarrukanta masu dad'in 'kamshi ta feshi jikinta dasu, bayan humra data rin'ka mungulawa ajikinta. Lokaci guda kuwa 'kamshinta ya mamaye dakin, Tana cikin d'aura d'an kwali ne khaleed yashigo d'akin da sallama, sanye yake cikin farar shadda d'inkin zamani, bayan ta amsa sallamar ta juyo ta kalleshi, tayi mashi wani tattausan murmushi tace "Barka da fitowa my man, wani irin dad'i yaji ya ratsashi har cikin zuciyarsa, dan yayi tunanin Fadila zata tada hankalinta ne idan gari ya waye ta tabbatar da d'akin Auta ya kwana, shima wani murmushi ya sakar mata, har cikin ranshi yaji dad'in yanda ta tarbeshi, ga kwalliyarta ta masifar yimata kyau, lokaci guda yaji ta matu'kar burgeshi, take kuma yaji wani sabon sonta ya shiga zuciyarshi. Ahankali ya 'karaso inda take yayi mata wata kya'ky'kyawar runguma, sannan yabata kiss a kumatu yace "Gud morning my special wife, har cikin ranta taji dad'in kalamansa, itama ta mayar masa da nata sakon kiss d'in a lips, tace "morning my man. Auta kuwa koda ta tashi kitchen tafad'a dan had'a musu break fast, Cikin k'ank'anin lokaci tagama had'a kome na break ta jera kan dining table, sannan takoma d'akinta ta fad'a toilet ta she'ka wanka, bayan tafito ta tsaya gaban dressing mirror tayi simple make-up sannan ta nufi Wadrope ta d'auko wasu English wear riga da siket, siket d'in farine har 'kasa, amma ya kameta daga sama, sannan k'asan ya bada fad'i, jikinsa akwai kwaliyya flowers da copee zare, sai rigar copee colour, tasha ado da duwatsu daga gabanta, rigar batada hannu, sai wani siriri kamar na bes, bayan tasanya kayan sun matu'kar yimata kyau, wani 'karamin farin gyale ta d'auko tayi rolling din kanta, sai ta ida fitowa balarabiya sak. Zee Elkaseem Mmn khady [06/08 11:42 pm] .: [06/08 11:10 pm] .: ๐๐๐๐๐๐๐๐๐ *AUTAR HAJIYA* ๐๐ป ๐๐๐๐๐๐๐๐๐ ยฎNWA ๐๐ป _ZEE MMN KHADY_ ๐ *_Page_* 106-110 โ๐ฝ Zaune suke kan dining suna break, kowanensu ci yake yana jin dad'in abin,
Table of Contents