Chapter 24
Chapter 24
ne suka fara rayuwa yakeji......moto ya shiga driver na jan sa hadi da nufar gidan Dan larabawa dashi". Anyi nasarar fiddo da diya mace,wanda Faroq da inna awannan rana ya xama masu ranar da baxasu taba mantawa dashi ba,a rayuwa". A ranar mutan Rugar suka taho,kuma anan aka shirya Hafsatu aka kaita gidan ta na gsky". Bayan kwana bakwai da rasuwarta ne aka maida sunan Diyarta da Hafsa,wanda Mutan rugar suke kirar ta da Hasile". A hannun inna Aka bar Hasile,wanda Aliyou kam tundaga wannan rana yakasa Xuwa gidan Inna,Ba lafy kullum yana cikin ciwo da rashin Hafsa a rayuwar sa". Sai da aka watse kusan Kwanan Hafsa Sha hudu sannan ya iya xuwa Gidan Inna,wanda ganin Hasile yasa Shi cuno masa dogon famin xiciyar sa,tabbas kaman Hafsatu tayi kaki ne ta aje". Don kaman su ya baci". Haka xai xauna ya tasa Ta yy ta kuka...sai Inna ta shigo dakin tayi ta rarrashin sa hadi da masa nasiha. A haka Hasile ta fara girma,Inna na bata madara,dom Ammie ne ta dauki nauyin komai....Shikam Aliyou maganar Karatu ya jingine gyefe..kullum bayi da aiki sai raino. A haka Hasile ta kai kusan shekara biyu,bb wanda ta sani sai nurry dad din ta,da Uncle Farouq,sai inna don daga baya ne tasan Ammie... Mahaofin Aliyoune ya sama masa Admission a Uk.wanda badon yasoba yaya fara shirin tfy karatu can. A inda xai karatan medicine". A kwanakin da Haidat baya nan,Inna bata da sukuni,Kullum Hasile tana kukan rashun Nurr Dad din ta .idan Ammien Haidar taxo,tayi shirru tana jirar shigowar sa,abuka ga yarinta idan taga Shiru² bau shigo ba,sai ta kuma saka masu ihu tana tsalamasu,ahaka xasuyi ta rigi² da ita,suna rainon ta...A haka Aliyou yy Wata uku acan yagasa sukuni sai da yadawo ganin Hafsan nashi". A ranar da yadawo shiru sukeji,don sai murna takeyi,shima kam sosai yaji dadin yanda yaga Su Ammie na Kula masa da Amanar sa...a hakayy sati guda sanan ya koma". Dawowan da xaiyi na buyu ne,ya tadda Inna Da su Farouq duka basa gidan,da yatmbyi mai hayan,sai yace masa ai kwanan su Shida kenan da tfy Rugar su,har yau basu dawo ba. Acan ko Ruga tun da suka je ne,Macido ya kyekyeshe ido,shikawai abashi Hafsa...abar masa diyarsa...Zuciya irin na Omar nan yace"Sai Inna ta bashi yar shi...Kuma su da rugar Hunkuyi harabada,sun barta...Haka inna ke kuka ta baima maccido Hafsatu da suke kirar ta da Hasile,amma da yake shi kafaffafen mutum ne haka yasa hannu ya amsa. Tun bayan da suka bai masa Hasile,aranar Omar ya ce subar Ruga haka kam akayi,wanda a hanya ne Inna tace"BazTaxata iya xaman kd ba. Ahaka suka nufo xaria. Tun daganan inna bata kara komawa kaduna ba...tabbas tasan mutuwa yankan kauna ce,ra rabu da Diyarta kuma wanda take gani taji sanyi yanxu itama an rabata da ita..tayi kuka kuma ta fammala ma Allah komai. A haka suka cigaba da ryuwar su a Zaria,inda Omar ya samu aikin soja...ya fara karatun sojan..Aliyou kam da Ammie kullum suna saka ran Dawowar Inna da Omar da diyar su Hafsa,duk shiru har shekaru biyar a haka suka cire rai da dawowan su". Nan shima Aliyou yabar kaduna yakoma Abj gidan Danlarabawa da zama". Bayan yan watanni Ammie ma ta biyo bayan sa,don Garin Kd bata masu dadi sam...... Tun daga nan Inna bata kara xuwa Rugar hunkuyi ba,sai da Hasile takai shekaru Goma,Amma koda taje badan bakin Hasile ina Nurry Dad din ta? Wanda tambayar yasa Hankslin Inna ya tashi,sai a lokacin ta tuno da koina Aliyou yake baxai taba mantaww da Hafsa ba,tom amma yaya xaiyi? Uban ta ya yi masu yankan kauna har da diyarta". Tun daga wannan xuwan Bata kara komawa ba,don Omar sosai yy ta sababi,yana zagin maccido...don yy fushi dashi kwarai". Abunka ga uwa tuno mata da Haidar Da Hasilen tayi,yasa Inna nufar kd,amma nan itamataji labrn barin su kdanan...haka ta koma da jimami da bakin ciki..... Nisawa Ammien Aliyou tayi,tana kallon Yanda Hasile ke xubar da hawaye,tabbas batasan haka rayuwarta ta kusa ba!. Itama Ammie hawwyen ta goge kana tace"Wannan shine lbrn ki Hafsa! Kuka ta rushe dashi,yyn da Ammie ta rungumeta,tana bubbuga bayanta a hankski na rarrashi...Cikin muryar Kuka Hasilen take cewa"Ammie yanxu Hamma Haidar shine Nurry Dad dina? Shine Hamma na,kuma miiiji na,Daddy na?. Ammie??? Ta kuma korar sunan ta,kamin tace"Ina son nurry dad dina,kuma inason Hamma Haidar dina ya xanyi kenan? Dole ya xabi daya,ko ya so Wannan amanar tasa,ko kuma yaso ni ni Hasile". tayi mgnar tana mikewa daga tsaye... Cike da dauriya Ammie tace da ita ina xaki Hafsa? Ammie xan koma part dina ne!. Murmushi ammie tayi kana tace..... Mmn teddy🧸 [10/7, 1:02 PM] Maman Teddy🧸: Maman Teddy: *Loading......* GDN KWARATA! Na Maman teddy🧸 80/81 *@Alheri Writer's asso.📚* Ban yarda ki karantamun lbri ba tare da kin biyani Kudin sa ba,domun kuwa lbrn na kudi ne idan kina bukatan cigaban Lbrn zaki yi mgna ta wannan number 08081202932 . Vip payment #500 mtn card,Normal #200. Idan har kika karanta baki baya ba keda Allah! Bismillahir rahmanur rahim". ______________________ "A kullum ni ba'abun da nake kuma karfafan ki dashi sai hakuri Hafsa...kici gaba da hakuri da Haidar,domun kuwa babu wanda yayi hakuri ya kuma dawo yy nadama ko bakin ciki anan gaba sai da farin ciki,don haka mahakkurci a kullum shine mawadaci....idan kk yi hakuri xaki ga ribar sa anan gaba". Murmushi Hasile tayi,kana ta kalli Ammie a sanyaye tace"Inshaalh Ammie,baxakiji Abun da xai tada maki da Hankali ba,sai dai farin ciki. Sannan Ammie ina rokon ki wata alfarma daya... Kallon ta Ammie tayi,kamin ta daga kanta tana girgixa mata alamun ta fadi maganan ta,nisawa Hasilen tayi,kana tace"Don Allah Ammie kar ki sanar da Hamma Haidar cewa na fahimci shi din ne Nurry Dad dina. Ta fadi mgnar tana sauke idon ta bisa saman fuskar Ammie. Wannan ne kadai kkso Hafsat? Baxan sanar masa ba,ki kwantar da hankalin ki kinji dayata?. Tom Ammie ni nakoma! Tom ki kula mun da bby na". Murmushi Hasilen tayi tana saka kai hadi da fice daga falon. ********************* Hankalin Aliyou Haidar gaba daya yagama tashi,ya gaxa sukuni,sam sai yaji babu dadi da yake fushi da amanar tashi,bayan shine yy mata laifi babba". Kasa zaune yy da tsaye,A hakan ya nufi Saman Table din dake tsakiyar falon yana daukar wani file da Key din moton sa ya nufo xuwa babban falon gidan! Kurr yayi Mata da ido ganun ta cikin Shigar da bai tsammani ba,kuma shida yace ta koma part din Ammie meya dawo da ita? Bin ta da kallo ya tsaya yana yi ya saki baki sam bai lura da Surayya dake gyefe ba,wanda da'alama fita xasuyi.....sanye Take cikin Tsadaddiyar lace din ta mai launin maroon da Milk...wanda tayi masa Dinkin Zamani ta riga da Skirt. Dinkin ya xauna ma jikin ta damm....Abunka ga mai diri,nan duk inda ta juya sai yy kaman tana karkadasu ne da gangar". Mayafin ta ta yafa mai launin milk...sai ta kalmin ta maroon duk da Plate mara tudu,amma Abunka ga doguwar mace kyawunta sosai suka fito. Foce din ta tasaka hannu tana dauka,hadi da cema Wa surayya muje gani nan.... Gaba surayya tafarayi kana ita kuma ta juya ga Aliyoun da sai asannan da yaji maganar tasu na zasu fita ne ya ce
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33