Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 22

Chapter 22

Gidan Kwarata Book 1 Complete Hausa Novel 1,286 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

suka chanja mata banda Hauwa bb mai kallon ta,run da ta taba Shalelen su abunso Aliyou Haidar". Kowa Tsaksnin ta dashi sai harara da yada mgna". A wannan satin kam su Rufaida har a salinta sai da Suka kwakwulo dabata san ta inda suka sani ba... Kinsan mene Ne Naima? Aa sai kin fada rufaida,wlh Shi idan akace maka mutum Ďan kauyen Bafulkatani ne,tom baya taba wayewa har ya mutu,don sai yy shekara arbain a binni kamin nan". Nan suka kwashe Da dariya har suna tuntsirawa...shiru Hafsat tayi kana ta wuce su batare da tace"Komai ba". Tundaga Ranan Kaman ance Aliyou Haidar ya kuma takura mata da damu ne,Don Tun tana marin shi har ta daina tabarsa da halinsa don ta lura shi irin mutanen nan ne idan suna son abu,idon su rufewa yake sukoma kaman mahaukata". Hakan yasata rabuwa dashi duk wacce hanya da xai hada su bata son haduwar tasu". A haka dai yau dadi gobe akasin hakan....a haka take ta gungurawa tana kokarin kauce mawa Aliyou da nacin shi". Ammie Kin san ina son Hafsan sosai kuwa? Allah dai Haidar? Ehhh Ammie yabata amsa tana kokarin Hada masa Ruwar wanka....Ammie Tom tayaya Daddy Zai amince mun na Aureta? Tofah Aliyou Wannan wani irin mgna ce haka? Na dauka dai Kawai Abun na ka schl friend ship ne... Aa Ammie nifah Auren ta xanyi. Ganin Abun nashi yana shirin samata Rigima,yasata cewa"Tom shikenan Haidar,allah ya nuna mun lokaci...Sosai yaji dadin mgnar Ammien nashi,Don haka ne A washegari Har ita hafsan sai da ya samu ya fade mata abun da Ammien shi tace,amma sai ta mayar dashi Sakarai". Ana haka sukayi hutu,wanda sosai Hafsa taji dadin hakan,don ta huta Da damun Haidar....Sai dai Hauwa da take zuwa gida suna taba zumunci". **************************** Hafsa...Hafsa.... Inna ce tayo kirar diyar nata,wanda yasa Hafsa Saurin fitowa tana amsa kirar Innan nata daga wajen soron gidan nasu". Kicibus sukayi da Shi hannun ta dauke da manjan da Inna ta aiketa sayowa....aiko sam bata san lokacin da Ta juye masa manjan a jikin shi ba". Gaba daya yar farar shaddan tasa ta rine da manja dama ana kafulle an shigo binni daga ruga". A zuciye ya daga hannun shi yana shirin wanketa da mari,aiko nan Yy saurin rike hannun nasa,kana suka hau kallon kallo". Cike da xafin murya Maccido ya kalli Aliyou Haidar yana cewa"kai wanene? Da xan hukunta kanwata kaxo ka rike ni". .murmushi Aliyu yy kana yace mai sonta! Mene? Ehh yanda kaji". Zaro ido hafsa tayi,tana ta'ajibi yaakayi Ya taho gidan su,har ya sani....muryar Umar ne taji yana cewa"Aliyou yayan mu ne,xo mu tafi laifi tayi masa,shigo ka gaida inna! Jin ance ya taho ya gaida inna yasa shi kutsa kansa cikin soron gidan nasu da yakasance tun daga farkon sa har karshen sa ginin jar kasa. Tab dijammm Hafsa,yaudara takkyi dama? Budan bakin maccido abun da yace mata kenan,wanda cikin sauri tayi wajen gidan don tsoron xuciya irin na Maccido". Mmn teddy🧸 [10/6, 12:59 PM] Maman Teddy🧸: *Loading......* GDN KWARATA! Na Maman teddy🧸 84-85 *@Alheri Writer's asso.📚* Ban yarda ki karantamun lbri ba tare da kin biyani Kudin sa ba,domun kuwa lbrn na kudi ne idan kina bukatan cigaban Lbrn zaki yi mgna ta wannan number 08081202932 . Vip payment #500 mtn card,Normal #200. Idan har kika karanta baki baya ba keda Allah! Bismillahir rahmanur rahim". ______________________________ "Shikam Omar nufa da Aliyou yy wurin Inna dake kitchen hayaki ya cika tun daga farkon gida har karshe". Inna Ga Haidar din da nake maki mgn". Omar yy mgnar yana nuna Aliyou Wanda ya dan risina ya gaida Inna dake ta fama da Hayakin Ice". Cike da harka Inna ta amshe aa Wannan Ne Aliyoun Hafsatun nawa? Tom maza kai shi daki,ka barshi daga Waje? Inna tayi mgnar hadi da Sauke idanun ta da sukayi jah sbd icen damunan dake damun ta akan na Omar...Tom Inna yy maganar yana juyawa hadi da nufah da Aliyou Dakin Innan da kwakkwarar Leda babu". Wata fatakakkakkiyar Tabarma ya shimfida ma Aliyou kamin Ya zauna,shima ya jah ya zauna. Itakam inna Bayan Wucewan su da ido takebin Aliyoun da lokaci daya tayaba da natsuwar sa,yaron kirki,sam baya da fahari da Girman kai irin na Yaran masu dashi". Murmushi tayi tuno da mgnar Omar da sukayi da yake cewa"Inna fah Shi Aliyou da gaske yakeyi Aurar Hafsatu zaiyi". Nan Inna tayi dariya a xuciyar ta tana fadin" Inbanda Yarinta ina Aliyou Ina Hafsatu? Dukan su nawa suke,takitaki basu fi shekaru Sha shida ba". Fitowa tayi daga madafin da take tana nufar Dakin Ta...da yake ba ginin Zamani ba,gini ne ta kasa,kasan ma jar kasa ta yambo,sai kofan lagye² n ta". Da shigarta tahau tsokanan Aliyou don ita macace mai harka da barkwanci sosai....Zama tayi tana debo masa ruwa a kwanon sha,sannan suka cigaba da fira,wanda duk da Haidar ba gwanin Fira bane,amma sun taba da Inna...koda Hafsatu ta dawo,tun a tsakar gidan take jiyio firar Inna da Aliyou hakan yasata Yin tsaki,tana mmkin tayaya Aliyou yasan Yayan ta Omar?. A haka ta yi shirin islamiya sai dai muryar ta daga kofa sukajiyo tana cewa"_Inna Sai na dawo! Tom Auta na Adawo lfy?. Da hakan ta fice". Shikam Aliyou bai bar gidan ba sai wuraren Biyar na yamma,kamin nan ya fahimci labr da tarihin Hafsatun duka,don mahaifin ta Allah yy masa Rasuwa tun bata da wayo,batafi shekaru biyu ba Ya rasu,Dama shi sana'arsa Sai da Manshanu a kasuwa,don a salin sa bafullatani ne na Zaria garin hunkuyi". Har Halakar ta Da maccido sai da ya juyo,duk da Inna bata fade masa Wani Abun dake boye tsakanin Maccidon Da Hafsatun ba! Da mahafin Maccido Wato Hardo da Baban Hafsatu Uwa daya Uba daya ne.Hakan yasa shi Yana xuwa Kawo masu Inna Ziyara,duk da itama Innan yar Asalin Hunkuyin ce". Wannan kenan! Tun daga wannan rana,ba'a kwana biyu Aliyou baizo gidan Inna ba,duk xuwan da yakeyi don yaga Hafsatu ne,wanda har yanxu kallon shi batayi,Duk da tana tsoron Yah Omar". Tsakanin Aliyou ko da Maccido sai harara,babu maj kallon wani da sunan Gaisuwar mutuntawa. Hakan yasa Hankalin maccido tashi,ahaka dai ya koma Rugar hunkuyi,su kuma su Aliyou Aka cigaba da Zuwa Makaranta,don hutun mako biyu aka masu takare". Haka xaita shishshige ma Hafsa tana yarfa shi,bai damuwa har ta gaji ta dawo daga rakiyar shi,Yazama na idan Ammien Aliyou taxo daukar shi sai ta dauki Hafsatu takaita gida,sannan su dawo da Aliyoun,A haka har Ammie da Inna aka saba,sosai suke mutumci,Don Itakan ta Ammie Sosai takejin son Hafsatu a xuciyarta,duk da tasan Auren ta Da Aliyiun ba mai yiwuba ne ba". A haka har suka shiga ajina biyu,aliyou kullum mgnar sa da xarar sun shiga ajin karshe xa'a tsaida mgnar Auren su,Tun Hafsatu na damuwa takoma rabuwa dashi bata cemasa Komai,don idan tabi tanashi xatayi ta marin sa a banxa,don bashi xai hana mgn yataso ya fada ba...kullum firar shi Hafsatu". A ranar Laraba ne sam baiga Hafsatu a makaranta ba,sosai ya kasance baya da Walwala...ahaka yake saran Ganin ta gobe nan ma bai ga xuwanta ba...Da ya tambayi Hauwa sai ce masa tayi ai tana lfy,gobe friday xata zo". A washe garin juma'a nan mababu Hafsatu babu hauwan don duka basu xoba! Hakan yasa Aliyou yakomakaman majinyaci". A natashin

Table of Contents

Chapters

33 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});