Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 9

Chapter 9

Farar Taska Book 1 Complete Hausa Novel 1,191 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

Meelah ta nufe ta da sauri tana faɗin "innar mu kiyi hak'uri wata rana idan ya dake ki da kaina zan rama maki kinji" a kufule yace " wallahi daga ranar da kika ɗaga hannu da sunan zaki dake ni daga ranar zan tsinke duka hannayen ki guda biyu, mtsew banzaye ƴaƴan Farar Taska kawai", sake juyowa yayi da sauri yana faɗin zaku zo ku fice min daga gidana ko zaku biya ni ne, cikin rawar jiki Ummy ta tashi tana gyara zanin jikin ta dake son faɗuwa tace " maigida Dan Allah ka bar su bari naje na nema yanzu amma kada ka dake su ko fito dasu daga gidan dan Allah" ya ja guntun tsaki yana kallon ta da yaran a wulakance kafin yace " Ina jira kada ki bata min lokaci" ya nufi ɗakin sa, ta juya tana kallon su da murmushi a fuskar ta dake jiƙe sharkaf da hawaye tace " Feenah ki ja hannun ƙannen ki ku shiga ɗaki ku jira ni kada ku kuskura ku fito har sai na dawo baya son ganin ku kun sani" Meelah tace "Innar'mu ni zan biyo ki muje kin ji" tace "aa Meelah ku zauna bazan jima ba zan dawo nima" ta juya da sauri ta bar gidan, sai tafiya take batare da tasan inda zata je neman kuɗin da zata bashi ba, wani tunani yazo mata kai tsaye gidan da take aikatau ta nufa, cikin rashin sa'a basa nan, duk inda take saka rai zata sami aikin da zata yi a bata wani abu duk taje basa bukatar aiki a ranar, ga yaron cikin ta sai juyi yake alamar yunwa, ga hankalinta yana gida gurin yaran, haka ta nufo gida jiki a sanyaye cike da fargaban yanda zasu yi dashi, tana tafe tana sharar ƙwallah, kicibis suka yi da shamwilu, yace "Ummy Ina kika fito acikin wannan ranar, ga ciki, kukan me kike haka? tayi ƙoƙarin haɗiye kukan dake son taso mata tace" An yini lfy? Yace " lfy lau, Ina shi Audi ya shiga da zai bar ki, ki fito haka? tayi murmushin yaƙe kafin tace" Yana gida tare da yara suna kula dashi baya jin daɗi" Shamwilu ya bata fuska kaɗan yace "Kai Anya kuwa, yanzun nan fa muka rabu dashi mun dawo daga gona, ko kansa baya ciwo kawai dai yana so ɗaga maki hankali ya wahalar dake, anya kinci abinci kuwa, yanayin ki ya nuna akwai yunwa a tare dake" ta girgiza kanta batare da tayi magana ba, yace "gsky Audi bashi da mutunci ka bar santaleliyar mace haka a wahala, ga juna biyu babu abinci, kinsan ko yau ya sami kuɗi sosai wani da yake biya bashi ina tsaye yazo ya kawo masa kuɗin amma kuma ya kasa siya maku ɗan abinda zaku ci keda yara, ni a gidana komai faɗa na bana hana iyalina abinci ina basu har nama su ci su ƙoshi shiyasa za ki ga yasir hankalin ta a kwance bata da wata damuwa, taci ta qoshi tayi barci ni na fita neman kuɗi, sai qiba kawai take ai" batare da tayi magana ba ta saka gefen mayafin ta tana share wasu ƙwallah, shamwilu ya rage murya kaɗan yana kallon ta, "wallahi Ummy Aisha Audi baya son ki ya sha faɗa keda yaran ki, har zargin ki yake da yaran a wani guri kika yi shegen su, wani lokacin ji yake kamar ya saka maku shinkafar bera ya kashe ku yake ji, Kinga wannan cikin idan kika haife sa lafiya kada ki kuskura ki ƙara bari kiyi wani cikin duk yanda zaki kashe auren ki kashe ki zo ni zan aure ki kuma na kula maki da yaran, saboda tausayin ki ya dasa min ƙaunar ki a zuciya ta, xan kula maki da yaran na ciyar dasu batare da kin fita nema ba, ki yarda dani" har lokacin batayi magana ba saboda tsanani mamaki zancen sa na cewa Audi zai iya kashe su ita da yaranta, shamwilu yace "wannan fararen yaran naki su suke ƙona ransa har yake kiran ki da farar Taska, saboda mahaifar taki bata iya ajiye komai ba sai haifo masa fararen ya'ya mata, ni ko goma zaki haifamin bani da matsala ina son su kuma da zuciya ɗaya zan riƙe ki da ƴaƴan ki". A sanyaye tace "Nagode" kafin ta soma tafiya jiki a sanyaye yabi bayan ta da sauri ya ciro dubu guda biyu ya bata yace " ga wannan kije keda yara kuci abinci nasan Kuna buƙata" kallon kuɗin tayi ta haɗiye wasu yawu da kyar kafin ta dube shi tana girgiza kanta, "nagode akwai abinci a gida da zamu ci" yace "aa wlhy Sai kin karɓa, ko da ace bana son ki ina so ki tuna ni fa abokin mijin kine tun ƙurciya da muka taso tare, ta yaya zan baki kyauta kiƙi karɓa Ummy Aisha? Ai shaiɗan kaɗai yake mayar da alheri shi kansa Audi idan yaji ba zai ji dadi ba" batare da tunanin komai ba ta saka hannu ta karɓa tare da sunkuyawa kaɗan tana masa godiya, da sauri ta fice har tana jin wani kuzari a ranta, yana tsaye yana kallon ta cikin murmushi har ga Allah yana kwaɗaituwa da Ummy Aisha shi yasa yake da burin auren ta ko da hakan zai sa ya rabu da yasira, har yanzu Audi ya kasa gane cewa duk faɗin garin jere babu mace kamar irin Ummy Aisha, da ba zai taba wulaƙantar da ita ba, ji yanda take haihuwar kyawawan ƴaƴa, ya girgiza kansa cikin murmushi ya fice yana addu'a a ransa ranar da zai ji auren su ya mutu da Audi. TWO WRITERS EMPIRE ✍️✍️ Ku garzayo kar ayi babu ku domin samun labaranmu guda biyu wadanda zasu nishadantar daku kuma su ɗebe muku kewa, FARAR TASKA (600) tare da alƙalamin FATYMA XARAH ZAMA DA MAƊAUKIN KANWA (600) daga alƙalamin UMMI A'ISHA Dukka wadannan Labaran guda biyu zaku samesu kan naira ɗari shidda shidda, ga mai bukatar biya sai ya tura kudinsa ta 7044644433 Aisha Ibrahim Moniepoint micro finance bank sai a tura evidence of payment ta wannan no 07044644433 ko kuma recharge card na mtn ta wannan no 08169334980 da shaidar biya. [8/2, 9:17 PM] J💕: *FARAR TASKA* Fertymerh Zarah 💕 7 Da sassarfa ta ƙarasa gidan, kai tsaye ɗakin sa ta nufa, yaran suna jin motsin shigowar ta duk suka fito jiki a sanyaye cikin tsoro idan bata sami kuɗin ba kada ya dake ta, har qasa ta kai gwiwoyin ta cikin ladabi tace "maigida wanna kaɗai aka samu dan Allah kayi hak'uri". Ya tsurawa kuɗin ido kafin ya dube ta fuska ba walwala yace " ajiye ki fice min a ɗaki" jiki na rawa ta ajiye har ta tashi zata fice yace " dawo nan mayya, naga sai wani kallo kike min ƙasa ƙasa na sa ni jarabar taki ce ta motsa shiga daga ciki yau kaɗai ba dan halin ki ba zan bar ki, ki kwanta min a ɗaki". Tace "Maigida dan Allah kayi min rai bazan iya ba, yunwa nake ji wlhy" ya bata rai kadan yace " Nima yunwar nake ji amma na yarda na sauke nauyin dake kaina kada Allah ya tambaye ni bana baki haƙƙin ki, maza maza kwanta daga can

Table of Contents

Chapters

18 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});