Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 17

Chapter 17

Farar Taska Book 1 Complete Hausa Novel 1,201 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

acewar sa tun da ya rabu da matar komai nata baya son gani kona ƴaƴan ta acikin gidan sa. Bayan farfaɗowar Ummy babu abinda take sai kuka idan ta tuna auren ta da Audi ya ƙare, mutumin da take gani duk duniya shi kaɗai ne ɗan uwa daya rage mata, shine suturar ta kuma rufin asirin ta, ta shafa cikin ta tana kallon Saratu, tace "Dan Allah Malam wadata yaje ya bashi haƙuri Saratu ko dan yarannan ya mayar dani". Saratu ta zauna tana faɗin "Maigari da kansa yayi masa magana bai ji ba bana jin yanda yake jin haushi da takaicin mu ni da Malam wadata saboda mun taimake ki ya saurare mu. balle yanzu da yake cikin fushi ki barshi ya sauko, kiyi hakuri Ummy kowane ɗan adam da irin tasa jarabawar, Zaki cigaba da zama damu kada ki damu". Ummy ta rumtse idanunta a hankali kafin ta buɗe cikin hawaye, "ina son shi Saratu, wallahi har cikin raina ina son mijina, ban gane hakan ba sai a yanzu da bana tare dashi, duk wannan azabtar dani da yake ina da yaƙini akan zai daina shiyasa bazan gaji da yi masa uzuri ba nasan wata rana zai dawo hanya madaidaici ya sharrin giya da Shamwilu ne" Saratu ta bata rai wannan karon, tace "haba Ummy ta yaya namijin dake wulakanta ki, yake dukan ki, babu ci, babu sha, babu sutura, sannan babu magana mai daɗi, baya kaunar ki keda ƴaƴan sa har kike ikirarin kina son sa kina son zama dashi, wannan dukan da yayi maki da ace yazo da ƙarar kwana fa? da yanzu fa babu ke a duniyar amma saboda kina da sauran numfashi a gaba Allah ya ɗauke jinjirin ya barki, duk wannan bai saka ya tausaya maki ba lokacin da kike cikin neman taimako ya sake ki a bainar mutane kuma kice kina son zama dashi, me yake damun ki Ummy? Tace "wallahi Saratu ina son shi a haka, na tabbata Audi yana sona ina ganin haka a kwayar idanuwansa, da zai nutsu ya daina shan wannan giyar zan sami soyayyar sa, kin sani tun iyayen sa suna da rai itace babbar matsalar da suka so ganin sun raba shi da ita hakan bai yiwu ba har Allah ya karbi rayuwar su, kuma dukan da yazo yayi min wallahi sharrin Shamwilu ne shine ya haɗa ni dashi, Shamwilu shine na biyu a babbar matsalar dake tare da Audi dan Allah ku roƙa min shi ya mayar dani". Tsaki Saratu tayi cikin takaici kafin ta tashi ta fice batare da tayi magana ba, tana fitowa suka haɗa ido da Malam wadata dake sauraren su, murmushi yayi yana faɗin "banda abin Saratu waye yake ƙoƙarin shiga tsakanin mata da miji, ai ko naman jikin ta yake gutsira tunda take son sa zata iya zama dashi, ki daina faɗa da fushi da Ummy ki rarrashe ta a yanzu kafin ta sami lafiya". Shiru kawai Saratu tayi batare da tayi magana ba saboda bacin ran Ummy da take ciki, tana fitowa ta sami Feenah tare da Huzaifa wanda tun kwanciyar Ummy asibiti kusan kullum yana gurin, wata shaquwa mai tsananin gaske ta shiga tsakanin su biyu, a shekaru irin na Safeenah shekara goma sha biyu kuma tashin ƙauye ya saka Huzaifa bai furta mata kalmar so ba ko da wasa, ya boye hakan har zuwa sanda zata san menene so da kuma Auren, Ummy ma duk lokacin da ta buɗe ido ta gansu tare wani sanyi take ji a ranta ta tabbata Huzaifa zai iya riqe mata amanar Safeenah kuma ba irin riqon da Audi yayi mata ba. Daren ranar sai ga Shamwilu ya zo, ya saka sabon yadin sa sai faman murmushi yake yi, yaran suka gaida shi ya amsa da sauri fuskar sa a sake yana ƙara kallon Ummy da ta tsuke fuskar ta, ya ajiye leda gefen Saratu yana faɗin, "ga wannan a rabawa yara, sauran na mai jinya ne" ya dubi Ummy, "Ummina ya jikin? tayi kasafe tana kallon sa jin sunan daya kira ta dashi bama ita ba har saratu mamaki take, yace "dan Allah kice su bamu wuri ina son magana dake ta sirri Ummina". Saratu ta tashi tana faɗin "ai dole zan tashi na fita Shamwilu amma kafin nan idan zaka fito ka ɗauki kayan ka bama buƙata" kafin yayi magana ta tattara yaran suka fito, yace "kamar wacce take baƙin ciki da zuwa na gurin ki Ummy, da alama zamu fuskanci maƙiya a auren da zamu yi, nikam da so samu ne ki tattara saratun nan kiyi watsi da ita domin bazata barmu zaman lfy ba" tace "ina ji sai da kasha giyar kafin kazo nan ko, to bara kaji wallahi ko maza suka ƙare a jere bazan taba auren ka ba Shamwilu, ko kana tunanin bansan munafurcin da kaje ka ƙullamin a gurin Audi ba, saboda kai nake kwance a wannan asibitin a yanzu kuma saboda kai Audi ya rasa jinjirin sa, saboda kai na rasa Aure na, da baka je ka gayamasa qarya akai na ba da bai zo ya dake ni ba wallahi tsakani na da kai Allah ya isa Shamwilu" ya sassauta muryarsa cikin sanyin hali, yace "naji duka laifina ne amma kiyi haquri saboda ina matuƙar son ki ne Ummy, wallahi ni kaɗai zaki aura a duk faɗin jeren nan ki kasance acikin farinciki, ina son ki da gaske Ummy" tace "Wallahi bana son ka, duk duniya babu wanda na tsana kamar kai" ta tashi da sauri ledar da ya ajiye ta dauka ta jefa masa a jiki tare da nuna sa da yatsan ta, tace "Maza ka ɗauki tsiyar ka tun kafin raina ya baci ka fice min da gani, bazan karba ba ballantana kaje ka gayamasa duniyar dake cikin jere ka kawo min na karɓa, kuma ka sani sai na gayawa Audi abinda kazo kayi a yau, sai na gayamasa cin amanar sa kake wallahi". Yace "Shikenan naji zan fita, kin ga wannan abin da kika min wallahi sai na rama.....ya juya cike da bacin rai ya fice, fitarsa ke da wuya Saratu ta shigo da sauri saboda tana labe tana jin komai, tace "kin kyauta, dama ko Audi haka kike rufe fuska ki ci masa mutunci da tuni kin daɗe da kwatarwa kanki ƴanci". Ummy tace "Raina baci yake idan na ganshi Saratu duk wani farin cikina shine yake gusar dashi, shine yake da kaso tamanin na ƙiyayyar da Audi yake min da yarana, ina addua watarana Audi ya gane hakan ya gane Shamwilu ba mai ƙaunar sa bane" Saratu ta zauna tana faɗin "akwai lokaci yana zuwa. Bayan kwana huɗu aka sallami Ummy jikinta yayi ƙwari sosai, Audi na ƙofar gida suka dawo daga asibiti da yaran, kallon ta yayi acikin kwana huɗu kacal duk ta canza kamar ba wacce take cikin jinya ba, haka yake ji a ransa kamar ya shekara bai saka ta a ido ba, idanun daya kafe ta dasu ya saka shamwilu kallon inda yake kallo, Ummy ta karaya daga kallon da Audi yake mata, ji take kamar taje ta rarrashe sa ta bashi haƙuri ya maida ta a gidan sa, ta tuna labarin da saratu ta bata na cewa ko da suka zo ya jefo duka

Table of Contents

Chapters

18 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});