Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 2

Chapter 2

Farar Taska Book 1 Complete Hausa Novel 1,206 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

zo suka bada haƙuri sosai sannan iyayenta suka yarda ta koma, bayan dawowar ta aka zauna dashi aka masa faɗa sosai da nasiha akan ya gyara zamantakewar sa da matarsa kai har da rayuwar sa ma idan ba haka ba zata koma gaban iyayen ta yaje ya nemawa kansa wata matar ya aura, sosai ya tsorata da fushin iyayen nasa, sai ya sassauto ya rage hantarar ta da dukan ta, yana siyo mata abinci da kayan maƙulashe irin na masu juna biyu da addu'a Allah yasa namiji zata haifa masa, ranar da ta haifi Jameelah yaji duk duniyar tayi masa baƙi, da masu karban haihuwar suka fice haka ya same ta cikin jego da raɗaɗin zafin haihuwa yayi mata duka sosai akan ta haifa masa mace, maƙota sai da suka shiga tsakani kuma kowa yayi Allah wadarai da hali irin na Malam Audi na rashin tausayawa, sanda iyayensa suka ji labari sai suka ɗauke ta suka maidata gidan su, dama mahaifinsa ba wata lafiya ne dashi ba kuma shi ba mai ƙarfin arziki bane, haka ya samu ya siyawa Ummi rago da ƙyar, suka saka mata suna Jameelah saboda kyawun nata har ya zarce na Safeenah, bayan haihuwarta da kwana goma Allah yayi wa mahaifin rasuwa, ko kaɗan mutuwar bata taba Malam Audi ba babban burin shi akai mahaifinsa makwancinsa azo a raba gado a bashi haƙƙinsa ba sai an gama addu'a kwana uku ba kamar yanda Shamwilu ya bashi shawara, idan ba haka ba zai wayi gari ya tarar mahaifiyarsa.ta cinye gadon ta barshi, sai yaji hankalinsa ya tashi ya sami mahaifiyarsa da mgnr gado kafin a gama adduar kwana uku, tun daga lokacin daya furta wannan maganar hankalin mahaifiyarsa ya tashi ta fashe da kuka, ba dan mutuwar mijin ba sai dan mamaki da irin ɗan da ta haifa, mahaifinsa ko kau dashi baa yi ba yana mgnr gado, da ƙyar mutane suka rarrashe ta suka bata haƙuri akan kukan da take, sai tayi ta masa addu'a Allah ya shirya mata Audi ko bayan ranta ya kula da Ummy, aka yi masa sallah aka je aka kaisa, sun dawo abokan mahaifinsa sun zauna yace duk su tashi su bar ƙofar gida babu uban da ya isa ya zauna yayi masa zaman makoki a gidan sa, duk ya korasu suka bar wurin kowa da irin abinda yake faɗa akan sa, yana shiga gidan yace da mahaifiyarsa " siyar da gidannan zanyi ina buƙatar kuɗi ki tattara komai naki da kike so kije can ƙauyen ku ki zauna da ƴan wanki, nayi maki alƙawari ziyartar ki akai akai kina saka min albarka, kuma ko na siyar da gidannan zan baki haƙƙin ki kija jari bazan ci ko ƙwandala a kuɗin ki ba" Ummi na gefe kanta sunkuye tana hawaye, tana roƙon Allah ya raba ta da wannan mugun mutum, mahaifiyarsa ta cira kai da ƙyar ta dube sa duk idanunta cike da ƙwallah ta buɗe baki zatayi magana sai ta kasa nan take ta faɗi gurin ko da aka duba rai yayi halinsa zuciyarta ce ta buga, wannan karon yaji mutuwar mahaifiyarsa kaɗan ba kamar ta mahaifin sa ba, har akaje aka kaita itama baiyi magana da kowa ba yana tunani a ransa menene laifinsa da mutanen gari suke zaginsa akan ya kashe mahaifiyarsa, shi fa maganar gado kawai yayi kuma musulunci ne ya yarda da hakan. Iyayen Hafsatu sun sami mummunan labari akan mutuwar sai suka shigo mota daga maiduguri zuwa jere ta'aziya akan hanyar su suka sami mummunan hatsari duk suka mutu a tare, Ummi ta shiga ruɗani matuƙa sosai da wannan abun fiye da zaton mai karatu, tayi kuka har ta gode Allah tayi addu'a da rungumar jarabawar ubangiji, haka tana ji tana gani ya mayar da ita gidan sa ya kuma siyar da gidan mahaifinsa ko ƙwandala bai bata ko siyawa yaranta wani abin ba, yaje yana siyan barasa da kuɗin shi da shamwilu, sai suyi kwana biyar basu saka shi a ido ba da haka har ya canye duka kuɗin gadon sa da duk abinda ya mallaka na iyayensa, ita take zuwa wankau gida gida ana biyanta kuɗi tana ci da kanta da ƴaƴan ta guda biyu, da haka har ta sami ciki na uku, shima sai daya ja mata kunne idan ta kuskura ta haifa masa mace wannan karon kashe jaririyar zai yi bazaa masa rainon ɗiya mata a gidan sa ba. TWO WRITERS EMPIRE ✍️✍️ Ku garzayo kar ayi babu ku domin samun labaranmu guda biyu wadanda zasu nishadantar daku kuma su ɗebe muku kewa, FARAR TASKA (600) tare da alƙalamin FATYMA XARAH ZAMA DA MAƊAUKIN KANWA (600) daga alƙalamin UMMI A'ISHA Dukka wadannan Labaran guda biyu zaku samesu kan naira ɗari shidda shidda, ga mai bukatar biya sai ya tura kudinsa ta 7044644433 Aisha Ibrahim Moniepoint micro finance bank sai a tura evidence of payment ta wannan no 07044644433 ko kuma recharge card na mtn ta wannan no 08169334980 da shaidar biya. [8/2, 6:53 PM] J💕: Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/ER26gPFC7iT6v26Jyz8hCt?mode=ac_t *FARAR TASKA* Fertymerh Zarah 💕 2 Ta shiga tsananin tashin hankali da ruɗani sanin zai iya aikata duk abinda yace zai yi, haka ta cigaba da rainon cikin da yara biyu, taje tayi aiki ta sami abinda zata ciyar dasu su ci su kwanta, wata rana haka suke kwanciya komai basu samu suka ci ba sai ruwa, yara ne ƙanana sai suyi ta mata kukan yunwa, idan kukan ya dame ta sai ta fashe da kuka itama, taje maƙota tana bara akan abinci ko da loma bibbiyu ne ta ba yaranta, idan ta samu ta basu suci ita ta kwanta da yunwa, idan bata samu ba taje ta same sa da kuka ta roƙesa akan ya basu wani abu ko garin rogo ne su siya suci, idan taci sa'a yakan bata 200 idan kuma ƴan iskan na kansa dukanta yake sosai akan bazai ciyar da ƴaƴanta mata ba, ana haka naƙuda tazo mata gadan gadan, maƙociyarta tazo kamar ko yaushe karba mata haihuwa, yana tsaye bakin window sai leqe yake yana addu'ar Allah yasa ba mace bace dan babu abinda zai hana ya kashe ta, sai faɗi yake yana ƙara ɗaga murya " kada ki kuskura ki haifo mace, idan ma kinsan macen ce ki dannata ki mayar da ita dan zan kashe ta", cikin hukuncin ubangiji ta sauka lafiya ta sami mace, sanda ya sami labarin ya zo a fusacce zai sa ƙafa ya take babyn sai ta ture sa da ƙarfinta har ya faɗi ya bugu, tana ganin haka ta ɗauki jaririyar jikinta na rawa ta fita har ƙofar maigari, ta shaida masa komai na yunƙurin kashe mata ƴa da Malam Audi ke shirin yi, nan aka tasa wasu matasa suka zo suka tafi dashi, ya tabbatar masa duk abinda ya sami jaririyar zai miƙa sa hannun hukuma su hukuntashi kuma zai bar masu gari, wannan ne ya saka ya sassauto da fushinsa akan jaririyar amma yayi alƙawari tunda ta turesa ya faɗi jikinta sai ya gayamata, kuma sarki ya kafa masa dokar dole ya ciyar da matarsa da ƴaƴansa tunda ba wani yayi mata cikin ta haife su ba, kuma ya tabbatar masa dole yaje ya siyawa yarinya rago ayi mata suna idan ba

Table of Contents

Chapters

18 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});