Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 12

Chapter 12

Farar Taska Book 1 Complete Hausa Novel 1,207 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

kayi haƙuri ta ƙarbi wannan saboda kada ta sake fita babu takalmi a ƙafarta, ga wannan canjin ka riƙe kafin gobe" ya faɗa yana ƙoƙarin ciro kuɗin aljihunsa, dubu uku ne ya bashi, Audi ya karɓa yana washe baki sai godiya yake sosai wannan ne karo na farko da aka taba bashi kuɗi akan yaran, duk masu cewa suna son su ko kwandala basu taba bashi ba, Huzaifa ya juya ga Ummy itama ya bata dubu biyu yana faɗin "gashi ayi haƙuri da wannan". ta girgiza kai alamar bazata karɓa ba, ran Audi ya baci suna haɗa ido ya jefe ta da wata harara wanda ba shiri ta miƙa hannu ta ƙarbi kuɗin, ta tattara yaran suka juya suka bar gurin, Huzaifa yayi masa sallama har zai bar gurin ya tsaida shi, yace "yaro ya ya sunan ka kuma waye uban ka a garin nan? A wannan lokacin Huzaifa bai shirya sanar dashi ko waye mahaifin sa ba, saboda sananne ne a Maiduguri ɗan kasuwa ne, bautar ƙasa ta zo dashi garin, yace da Audi "mahaifina ba wani sananne bane ko na faɗa ba lallai bane ka san shi, ni sunana Huzaifa Kuma ni talaka ne, nazo yin bautar ƙasa a wannan garin" yace "shi mahaifin naka aikin me yake? Huzaifa yace" baya aikin komai a yanzu ni nake taimako sa da albashina " Audi ya jinjina kansa, yace" Naji a jikina Kai yaron kirki ne, idan hankali na ya gama kwanciya da nutsuwar ka zan baka auren Safeenah bada jimawa ba" murmushi Huzaifa yayi "Kamar yace shi bai shirya aure a yanzu ba domin akwai abinda yake jira ya kammala ya bar ƙasar gabaki ɗaya yaje yayi masters ɗinsa, Kuma ya tabbata mahaifin sa ma ba zai masa aure a yanzu ba amma yana tsoron hali irin na Audi, yana tsoron ya hana masa taimakon yarinyar, yace " nagode sosai da wannan karamci Baba" Audi ya nufi gida da sauri batare da ya qara magana ba, kai tsaye ɗakin su ya nufa, "ke bani kuɗin nan har kin manta ina da sauran canji a hannun ki da baki cika min kuɗin gida ba, naga har baƙin ciki kika so ki mana ki ƙi karɓan kuɗin wlhy da yau jikin ki ya gaya miki". Babu musu ta miƙa masa kuɗin ya karɓa zai fice, Meelah tace " Baba to me kake so mu ci da safe idan ka karbe duka kuɗin, ai ya raba ya baka naka itama ya bata nata" ya juyo Yana nuna ta da ɗan yatsa, "ke kin gan ki wlhy ki kiyaye ni, ina ɗaga maki ƙafa ne saboda ina jin ki a raina duk acikin su da tuni na daɗe da zubar da haƙoran bakin ki duka" Meelah tace "to ka bamu kuɗin mu mana idan dukan mu zaka yi ka dake mu amma kada ka hana mana kuɗin mu zauna da yunwa, idan ba haka ba gobe idan ya dawo kawo maka takalmin zan gaya masa ka karbe kuɗin innar'mu.... bata ƙarasa ba ya saka hannu ya bige bakin nan take ya fashe da jini, "shegiya farar mayya dama kece yace yana so a goben zan aura masa ke ya tafi dake na huta" ya jefa masu dubu ɗaya ya fice yana balbalin faɗa, kicibis suka ci karo da Shamwilu a ƙofar gida, yace "Audi Kai da waye kake faɗa a wannan daren, ko farar taskar kace? Tsaki Audi yayi kafin yace" baƙar taskar dai ai idan ka ganni cikin bacin rai ka sani babu mai ƙuntata min kamar Ummy da yaranta, gabaki ɗaya sun gama raina ni kuma duka babu irin wanda bana yi masu". Shamwilu ya ja hannun sa suka zauna nan dakkali yace "Wai har sai yaushe Ummy zata daina saka ka a ƙunci ne? haka zaka ƙare rayuwar kullum da bacin rai abokina, gashi shekarun ka kaɗan amma fitinar matar nan da yaranta sai tsofar da kai suke, wai baza ka ɗauki mataki bane? Yace" wallahi Shamwilu babu wani mataki da ya rage wanda ban yi ba nayi dukan nayi dukan har na gaji amma duk a banza daga ita har yaran". Shamwilu yace "Ai yanzu mafita ɗaya ce kawai ka yarda ka sake aure, ka auro mafaɗaciya Kuma hatsabibiya ka haɗa su zama a gida wlhy zata gyara maka Ummy, idan zama ya gagare ta zata tattara ita da yaran su bar maka gidan ka" Audi yayi shiru cikin tunani kafin ya girgiza kansa, Shamwilu ya buga kirjinsa kaɗan yace ka sami lokaci kayi tunani Audi ni mai son ka ne shiyasa duk abinda zai saka ka farin ciki nake kokarin nemo maka shi, yanzu sanar dani me Ummy tayi maka a wannan daren ya fusata ka haka? Audi yace "yaron kirki ne yazo yana son Safeenah ya bamu kuɗi taqi ƙarba Sai da na zare mata ido, bayan ya tafi naje na same ta na kwace kuɗin shine Jameelah ke gayamin magana....Shamwilu ya buga wani uban ashar, yace "amma duk duniyar nan babu munafuka irin Ummy a gaban ka zata nuna bata karɓan kuɗi a hannun maza, bayan a idon ka zuwa take tana roƙona kuɗi? Audi ya zare idanu yana kallon sa cikin mamaki, yace "me kake son cewa shamwilu, wai kana nufin ita ummy tawa dai take zuwa roƙar ka kuɗi? Shamwilu yaja ƙaramin tsaki yana gyara zaman sa, yace "ko jiya ta tare ni a hanya na bata dubu biyu, ta zage ka sosai akan rashin ciyar dasu da baka yi kake barin su da yunwa, ta tsinewa giyar da kake sha, ta kira ka mashayin banza, Ummy da bakin ta take sanar dani ta jima tana sona saboda yanda nake kula da iyalina nake ciyar dasu da basu farinciki, kuma kudin da na bata ne kazo kake nuna min kyale ka kawai nayi a jiya, nan da bakin ka kake cewa ka yarda da ummy bata neman maza amma a jiyan tace idan zan jure bata kuɗin da zata ciyar da yaranta babu abinda zan nema a jikinta ta hanani k.....bai ƙarasa jin zancen shamwilu ba ya tashi a fusacce ya shiga gidan, kansa har wani sarawa yake ga duhu dake mamaye idanun sa. TWO WRITERS EMPIRE ✍️✍️ Ku garzayo kar ayi babu ku domin samun labaranmu guda biyu wadanda zasu nishadantar daku kuma su ɗebe muku kewa, FARAR TASKA (600) tare da alƙalamin FATYMA XARAH ZAMA DA MAƊAUKIN KANWA (600) daga alƙalamin UMMI A'ISHA Dukka wadannan Labaran guda biyu zaku samesu kan naira ɗari shidda shidda, ga mai bukatar biya sai ya tura kudinsa ta 7044644433 Aisha Ibrahim Moniepoint micro finance bank sai a tura evidence of payment ta wannan no 07044644433 ko kuma recharge card na mtn ta wannan no 08169334980 da shaidar biya. [8/3, 6:33 AM] J💕: https://chat.whatsapp.com/ER26gPFC7iT6v26Jyz8hCt?mode=ac_t *FARAR TASKA* Fertymerh Zarah 9 Murmushi Shamwilu yayi yana addu'a a ransa Allah yasa karshen auren yau, tana haihuwa idan ta gama idda ya aure ta koda karshen zaman sa da yasira zai zo karshe, akan soyayyar Ummy babu abinda ba zai iya ba. Yaran Suna zaune tana tsaye tana yiwa meelah faɗa akan abinda tayi wa mahaifinta, yaran suna maida mata magana akan rashin kyautawar mahaifin nasu babu zato taji ya haɗa kanta da nashi, tayi tangal tangal zata faɗi tayi saurin

Table of Contents

Chapters

18 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});