Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 16

Chapter 16

Farar Taska Book 1 Complete Hausa Novel 1,203 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

kika saka ni cin bashi har dubu biyar, ni ne zan maki zubin? Ta bata fuska tana masa wani kallon raini tace" me kake nufi, ko ban isa ka bani kuɗin ba ne? Yace "a'a yi haƙuri gimbiyar mata ki saki fuskar ki bakya kyau idan kika bata fuskar, wasa nake wallahi na haƙura" ta ja ƙaramin tsaki tana faɗin "ka da ka manta da mgnr da muka yi shekaranjiya, ka siyar da gona ɗaya ko ka karbe ta gurin Audi ka siyar ka bawa yaran nan jari za su je can kudu su yi sana'a ba aikin noma zasu zauna yi a gida ba". Yace "duk yanda kika ce haka zaa yi, ai dukiyar taku ce keda yaran ki Kinga bazan ji asarar siyarwa na biya buƙatun ku ba, zan duba naga wacce zaa siyar" batare da tayi magana ba ta nufi ɗakin ta da hanzari ya bi bayan ta da sauri yana waiwayen bayan sa idan babu yara a gida, kafin ya washe baki ya ƙarasa shiga ɗakin, ta juyo tana kallon sa "lafiya sai bibiyata kake? Ya sosa kansa yana dariya yace" haba yasira yanzu duk wannan hidimar da nayi na bada dubu biyar na adashe bai isa ya saka nima a ɗan bani na lasa ba, ki taimaka yau kusan wata takwas kenan ina bibiyar ki kina hanamin yau kaɗai sabida Allah ki bar ni nayi". Kallonsa tayi galala baki a buɗe kafin tayi wani shu'umin murmushi tana taba hannayen ta tace "Shamwilu ko na baka dubun ka biyar ne, naga sai mita kake a kansu zan iya fita naje na nema da kaina ka sani". Yace "aa babu inda zaki je neman kuɗi bayan gani, ba mitar kuɗin nake ba naga nayi abin a yaba min ne a saka min da wani abin? Tace" to ka fice min daga ɗaki kafin raina ya baci" yace "ki taimaka ko sau ɗaya ne, abin nan tana cikin yunwa idan ba wata kike so naje na nema a waje ba? wata irin dariya tayi mai cike da shaƙiyanci kafin ta juyo tana kallon sa ƙasa da sama a wulaƙance tace " shege ka fasa, ka je ka kwanta da wata mace a waje ka dawo ka same ni gidan nan " zai yi magana suka jiyo muryar Audi Yana sallama, da hanzari ya fita baya so ko kaɗan Audi yaji suna sa'in'sa da Yasira, a zauren gidan suka yi kicibis yace " Wai Kai da Sai ka faɗomin kawai a gida bazaka jira na fito ba, idan ka same ni akan matata fa? Audi yayi baya jiki a sanyaye yana faɗin "fito abokina fito ka ga babbar asarar da ta same ni a yau" wannan karon sai ga hawaye a fuskar sa wanda ya sanyaya jikin Shamwilu yabi bayansa ba kuzari, kallon abinda ke hannun sa yayi yana faɗin "Audi menene ka ƙunso haka a zani, kada dai ba abin wani kaje ka ɗauka aka ganka kazo kana min kuka ba, dan Allah kada ka saka ni a matsala". Audi ya sharce majina yana faɗin "kasani duk acikin hali na marar kyau giya ce kawai da nake sha, bana sata, bana caca da zina kuma ina sallah biyar a rana kullum ko da na buge, dana farfado nake ramakon sallah, meyasa kake bina da sharri a maimakon alheri? Shamwilu ya washe baki kaɗan yana dafa kafaɗarsa yace " yi haƙuri aminina kasani duk duniya babu wanda zai maka shaida irin wacce zan maka, a ruɗe nake da kai ne baka saba zomin kana hawaye ba dole na ruɗe, wai menene a zanin kake boyewa? Audi ya buɗe jinjirin yana nuna masa, "yaron da ummy ta haifa ne babu rai, ka duba ka ga irin magajin da na samu sak Irina, baƙi Mai kamanni kamar ni amma sun kashe mani shi Shamwilu" (ya cigaba da zubar da ƙwallah cikin ƙunci) Shamwilu ya karbi jinjirin yana kallo, yace "abokina tabbas ba dan ina cikin bacin rai na Yasira ba da na taya ka kukan wannan rashin da kayi, amma zuciyar tawa a bushe take yanzu saboda dukan ta na gama duk raina a bace yake, Kaga yaron sak Kai wannan zaa ce Kaine ka haife sa amma banda waɗancan matan, yanzu Ina ita Ummy? " Audi yace" tana asibiti na sake ta". Shamwilu ya zaro idanu yana kallon sa, yace "da gaske ka saki Ummy ko wasa kake min? Yace "baƙin cikin kashe wannan yaron ya saka na sake ta, babu wani amfanin zamana tare da ita tun da bata so na da khairi, amma wancan tsohon mai gari yana cewa babu sakin wai har yanzu matata ce ita, shine na kyautar da ita ga Wadata" Cikin ƙunar rai Shamwilu ya dube sa, yace "shi wadata ka bashi kyautar Ummy to ni menene amfani na, Ina abokin ka kaje ka baiwa wani banza gani meyasa ni baka bani ita ba sai wani shashasha". Audi yayi Jim kaɗan kafin yace "kasan kuɗin da ya kashe na nema mata lfy Sam bazan iya biyan sa ba shiyasa na bar masa ita, kana da mata irin Yasira ina zata bar ka kayi wani aure yanzu, ni bama wannan ba, wai yanzu Shamwilu babu ta yanda zaa yi yaron nan ya tashi? Cikin takaici shamwilu yace "ina ne ka taba jin an mutu an dawo, waye yake bayar da rayuwar idan ba Allah ba kuma ya karbe kayansa ko gurin boka kaje bazai tayar da wannan yaron ba" idanun Audi suka yi jawur ya karbi yaron yana ƙara kallon sa yana jin wani shauƙin son sa, da kyar aka rarrashe sa mutanen unguwar aka karbi yaron aka je aka masa wanka da sutura, kukan da yayi akan yaron bai yi akan rasa iyayen sa ba yanzu ne ya san zafin mutuwa, a wannan ranar yayi addu'a sosai ya saka iyayen sa tare da istighfari akan abinda ya aikata masu, yana tunanin ko haƙƙin su ne ya kama yaron, daren ranar ya nufi mashaya batare da ya ƙara waiwayar asibiti ba. TWO WRITERS EMPIRE ✍️✍️ Ku garzayo kar ayi babu ku domin samun labaranmu guda biyu wadanda zasu nishadantar daku kuma su ɗebe muku kewa, FARAR TASKA (600) tare da alƙalamin FATYMA XARAH ZAMA DA MAƊAUKIN KANWA (600) daga alƙalamin UMMI A'ISHA Dukka wadannan Labaran guda biyu zaku samesu kan naira ɗari shidda shidda, ga mai bukatar biya sai ya tura kudinsa ta 7044644433 Aisha Ibrahim Moniepoint micro finance bank sai a tura evidence of payment ta wannan no 07044644433 ko kuma recharge card na mtn ta wannan no 08169334980 da shaidar biya. [8/3, 9:11 PM] J💕: https://chat.whatsapp.com/ER26gPFC7iT6v26Jyz8hCt?mode=ac_t *FARAR TASKA* Fertymerh Zarah 12 Gwargwado Mutanen garin sai zuwa jajen rasa jinjirin suke masa sanin Audi wani gefe mutumin kirki ne, duk wani abu ya sami mutum na farinciki ko akasin sa idan har yaji lbr ya kan je wa mutum shiyasa rashin wannan jinjirin ya sami masu zuwa masa ta'aziyya sosai, bayan mutane sun lafa ya tashi daga ƙofar gida ya shiga cikin gida, kallon ko ina yayi duk a hargitse da kayan yaran dana mahaifiyar su, cikin takaici da bacin rai ya soma tattara su duka yana jefa su ta katangar wadata, duk wani tsumma nasu haka ya tattara ya fitar dasu daga gidan

Table of Contents

Chapters

18 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});