Chapter 15
Chapter 15
ta saboda ka cika babban mashayi, to wlhy ko ka sake ta sai ka bayar da kuɗin jinin da zaa saka mata domin kaine silla na shigar ta wannan halin" Audi yaja dogon tsaki yana ƙara rungume yaron tsam a ƙirjinsa kamar wanda zaa ƙwacewa shi ko zai mayar dashi a cikin sa, ya cunno bakin sa, da bakin sa ya nuna mata Wadata kafin yace "shi wannan ƙaton banza menene amfanin sa idan ya kasa biyawa ƙwartuwarsa jini, ke wallahi kika ƙara min magana anan zan fasa bakin ki babu ruwana da shekarun ki, duk uban da zaki saka ya dake ni anan gurin kin daɗe da baki saka ba, matata ce kuma nace na sake ta ko akwai shegen da ya isa ya saka na maidata, ku saurari kiran sammaci daga gurin mai gari" ya fice yana zage zage, Wadata ya girgiza kansa jikinsa a sanyaye ya juya zai bar gurin, Saratu ta dube sa tace "Mai gida ina kuma zaka je, dan Allah ka tsaya mu taimaki baiwar Allah, idan muka barta da yarannan baza su iya mata komai ba" ya juyo yana kallon ta, "duk abinda nake yi ina yi ne saboda Allah da haƙƙin maƙotaka ashe shi zargin yake ina tare da matar shi, kaico na kaicon wannan duniya da rayuwa irin ta Audi, Allah zai saka min, Nurse ɗin tace "kada kayi fushi ka bar ta wallahi zata iya rasa ranta, duba kaga yanda take numfashi bata hayyacinta dan Allah ku ceci rayuwar yarinyar nan". Su Safeenah suka fashe da kuka suna roƙon Wadata, babu yanda ya iya dole yaje aka auna jininsa baya yi mata, ya kira abokansa duka guda biyu aka duba jinin bai yi dai dai da nata ba, duk suka shiga damuwa sosai hankalin su ya tashi, Nurse ɗin ita ta bayar da shawara suje Birni su siyo jinin zata rubuta irin wanda ake buƙata ta basu da sun je asibiti su bayar da takardar, haka kuwa aka yi duk da Wadata ya wahala sosai kuma ya kashe kuɗi kafin ya samu jinin, a galabaice ya dawo yana kallon matar sa yace "Saratu duk kuɗin hannuna sun ƙare sai da nayi rancen dubu takwas, bansan ya zamu yi ba yanzu" tace "Malam kada ka damu Allah zai bamu wata mafitar tun da Alheri muka aikata da kuɗin, kuɗin da ake biya kuma idan mun koma gida lafiya zan duba abinda nake dashi na baka ka biya bashin, fatan mu kada ummy ta rasa rayuwarta ko dan ƙananan yaran nan da basu da wani gata a duniya yanzu". Suna zaune bayan an saka mata jinin sai ga kira daga mai gari duk wanda yake asibitin ana neman sa, babu bata lokaci kowa ya bar asibitin suka tafi (asibitin ƙauye kenan) , yaran kawai aka bari da Ummy wacce har lokacin barci take bata farfaɗo ba, acan suka sami Audi zaune rungume da gawar yaron duk tunanin su zuwa wannan lokacin an daɗe da masa sutura an kaishi makwancinsa ashe yana nan yana yawo dashi a ƙauye yana nunawa mutane ya sami magaji mai kama dashi sak amma an kashe masa shi saboda baƙin ciki. Duk suka sami guri suka zauna cikin girmamawa ga mai gari, yayi gyaran murya kaɗan kafin ya faɗi ƙorafin Audi akan yaron sa da aka kashe. TWO WRITERS EMPIRE ✍️✍️ Ku garzayo kar ayi babu ku domin samun labaranmu guda biyu wadanda zasu nishadantar daku kuma su ɗebe muku kewa, FARAR TASKA (600) tare da alƙalamin FATYMA XARAH ZAMA DA MAƊAUKIN KANWA (600) daga alƙalamin UMMI A'ISHA Dukka wadannan Labaran guda biyu zaku samesu kan naira ɗari shidda shidda, ga mai bukatar biya sai ya tura kudinsa ta 7044644433 Aisha Ibrahim Moniepoint micro finance bank sai a tura evidence of payment ta wannan no 07044644433 ko kuma recharge card na mtn ta wannan no 08169334980 da shaidar biya. [8/3, 8:45 PM] J💕: https://chat.whatsapp.com/ER26gPFC7iT6v26Jyz8hCt?mode=ac_t *FARAR TASKA* Fertymerh Zarah 11 Duk suka zubawa Malam Audi idanu kafin su dubi mai gari cikin mamaki, ɗaya daga cikin ma'aikaciyar asibiti ta muskuta tayi wa mai gari bayanin komai tun daga farko zuwan su har kawo yanzu, kana ta ƙara da cewa saboda yaron bai isa haihuwa ba da kuma an bar ta gida har kwana biyu tana naƙuda ya saka Allah bai yi mai numfashi bane" Mai gari yace "ina ita mai haihuwa? Saratu tace" tana can kwance bata san inda kanta yake ba saboda babu jini a tare da ita, an gayawa mijin ta yaƙi ya bayar da komai sai mijina ne yaje ya siye jini aka saka mata" mai gari ya dubi Audi dake ta rarraba idanu yace "ko da ka sake ta alhakin ciyar da ita da nema mata lafiya yana kanka saboda ta dalili ka ta haɗu da wannan jarabawar, ballantana babu saki irin wannan sai na bidi'a dan haka ka biya malam wadata kuɗin sa saboda har yanzu ita matar kace" Audi ya soma ƙoƙarin tashi da gawar yaron sa yana faɗin "wannan haɗin baki ne Sam babu adalci a wannan zaman, matar da nace na sake ta kuma zaa ce na kula da ita, ta yaya ciyar da ita da nema mata lfy yake ƙarƙashi na bayan na sake ta, kai da na zo mak da zancen an kashe min magaji ka bimin haqqi Sai ka buge da wata magan can, tukunna ma waye yace ba'a saki dan tana cikin jinin haihuwa? Mai gari ya dube sa cikin bacin rai yace" ka zauna Ina magana da kai ina zaka je, nace kuɗin da Wadata ya kashe ka maida masa domin bashi yake da alhakin kula da ita ba kai ne kuma Ummy har gobe matar ka ce babu wannan sakin" ran Audi ya baci, yayi jim kaɗan kafin ya dubi mai gari yace "ina cikin wani hali na alhini saboda rasa ɗana, a bar ni naji da mutuwar a yanzu idan anyi masa sutura zan biya shi" Wadata ya muskuta kaɗan yana kallon mai gari, yace "ranka shi daɗe maganar kuɗin saka jini a bar shi nayi saboda Allah, kawai ya bada kuɗin maganin da zaa siya mata" Audi ya dalla masa harara yana faɗin "duk zan biya ka ragin ko sisi bana so daga gurin ka, in har da gaske saboda Allah kayi matarka bazata zo nan bainar jama'a tana maimaita mijin tane ya siye jini aka saka mata ba, dan haka zan biya gudun gorin wata rana Kuma Ummin na bar maka ita bana so" ya tashi da gawar da sauri kafin mai gari yayi magana ya fice ransa matuƙar bace, Kai tsaye gida ya nufa inda Shamwilu. Yasira fitowar ta bayi kenan yayi dai dai da shigowar sa, ta ɗaure fuska tana faɗin "Sai yanzu kake dawowa gida? Yace " Afuwan abar ƙaunata kuɗin ne basu samu da wuri ba, gasu da ƙyar na samu" ta fisge kuɗin daga hannun sa tana dubawa, dubu biyar ne kana ta saki fuska ba yabo ba fallasa tace " karbi kaje da su inda Azumi ka bata kuɗin zubin adashe ne da nake yi, ka tunasar da ita kada ta aiko min cewa ban zuba a wannan watan ba" ya haɗiye wasu yawu da ƙyar yace "Wai dama yasira saboda ki zuba kuɗin adashe ne
Table of Contents