Chapter 11
Chapter 11
cutar dake zan yi ba, nayi ne saboda Allah, na tabbata mahaifiyar ku ta hana ku karɓan abu a gurin maza saboda gudun kada su cutar daku and is good" Feenah ta girgiza kanta tare da boye duka hannuwanta a bayan ta "ni bazan karɓa ba" ya ajiye takalmin yana faɗin "waye mahaifin ki, ina so na ganshi" ta fiddo idanu cikin tsoro da fargaba, tace "kai ma kana so na ne? tambayar tayi matuƙar bashi mamaki, ya qara kallon ta qasa da sama kafin yace" so kuma? Ke kin san so ne? Gayamin menene so? Tace "malam kayi haƙuri wallahi bansan shi ba, amma duk wanda ya je ya gayawa Babana yana so na duka yake mana ni da ƙannena" yaji wani iri a ransa, yace "baya so a so ku ne? Tayi shiru cikin rashin sanin abin faɗa amma har ga Allah a tsorace take kada ya je inda Audi, ya sassauta murya kaɗan yace" ba son ki nake ba Safeenah ina so ne naje na roƙesa ya barki ki karbi takalmin nan domin kina buƙatar su, kince ba'a bari Kuna karɓan komai a hannun namiji amma a matsayin ki na mace sam bai dace kina fita babu takalmi a ƙafar ki ba, ki gayamin waye mahaifin naki. " taja numfashi kaɗan kafin tayi masa bayani nan take ya gane wannan babban mashayin giya ne mahaifin ta wanda duk garin jere babu kamar sa cos tun zuwan sa garin yana ganin yanda yara suke masa idan ya shawu, amma abin mamaki shi yake da wannan kyakkyawar yarinya kuma yake irin wannan rayuwar? Ganin yayi shiru yana tunani ya sakata ficewa da gudu ba tare da ta kara saurarar sa, a matsayin shekarunta goma sha biyu a duniya tana da tabbacin wannan so da maza ke yawan samun mahaifinta dashi akan ta ba alheri bane ganin yanda duk wanda ya tare sa da maganar a ranar sai yayi masu duka su uku tana son sanin ma'anar kamar ta taba tambayar Ummy a maimakon ta amsa tambayar sai faɗa tayi sosai akan kada ta kara jin kalmar a bakin ta. TWO WRITERS EMPIRE ✍️✍️ Ku garzayo kar ayi babu ku domin samun labaranmu guda biyu wadanda zasu nishadantar daku kuma su ɗebe muku kewa, FARAR TASKA (600) tare da alƙalamin FATYMA XARAH ZAMA DA MAƊAUKIN KANWA (600) daga alƙalamin UMMI A'ISHA Dukka wadannan Labaran guda biyu zaku samesu kan naira ɗari shidda shidda, ga mai bukatar biya sai ya tura kudinsa ta 7044644433 Aisha Ibrahim Moniepoint micro finance bank sai a tura evidence of payment ta wannan no 07044644433 ko kuma recharge card na mtn ta wannan no 08169334980 da shaidar biya. [8/2, 9:34 PM] J💕: https://chat.whatsapp.com/ER26gPFC7iT6v26Jyz8hCt?mode=ac_t *FARAR TASKA* Fertymerh Zarah 💕 8 Daren ranar sun gama cin abinci kenan Audi ya shigo da hanzari sa har tuntube yake kamar zai kife a ƙasa saboda tsabar sauri, "ke ɗiyar farar taska, Ina Ummy ne nake ta faman kira kika min banza" da ƙyar ta fito daga banɗaki saboda nauyin cikin ya soma damun ta, muryarsa kaɗai ta tabbatar da ba lafiya ba, yace "Ina yaran naki suka shiga" tace "suna ɗaki lafiya maigida? Yace" fito min dasu duka kafin na saka ƙafa na take cikin nan naki, daga yau ba zasu ƙara zuwa wani boko ba tunda soyayya take kai su ba karatu ba" taji hankalinta ya tashi, soyayya kuma yaushe yaran suka san wani abu soyayya? Yaran da basu da ƙawaye mata balle samari, yaran da bata bari suna zuwa ko ina daga makaranta sai idan aiken su tayi.....tayi firgigit saboda tsawar da ya daka mata, "Ina magana kin min shiru saboda kin raina ni ko" ta ɗaga murya kaɗan hankalinta a tashe tana kiran sunan yaran, ba bata lokaci duk suka fito a gaban sa suka tsaya cirko cirko, ya tofar da yawu gefe yana kallon su cikin bacin rai, "wace shegiyar ce acikin ku take bibiyar maza? Duk suka zaro ido suna kallon sa cikin rashin fahimtar maganar sa, da ƙyar Ummy tace" Mai gida me yayi zafi haka zaka shegantar da ƴaƴan cikin ka, kuma ma ta yaya waɗannan ƙananun yaran suka san s..... bata ƙarasa ba ya ɗauke ta da mari cikin bacin rai yace " ke har kin isa ina magana kina ƙaryatani? ƙarya nayi ba shegu bane ko ƙarya nake basa bibiyar maza, Meyasa ake yawan tare ni akan yarannan ko su kaɗai ne mata kaf a ƙauyen nan, wallahi ina magana kika sake sakamin baki sai na fasa shi, shegiya mayya, da maza ne kika haifamin da yanzu hankali na a kwance bani da wata damuwa" ya dubi yaran "mu je ya nuna min wacce yake magana acikin ku domin wannan karon bazan bar ku ba sai na maku mugun duka da ko sunan namiji aka ambata a gaban ku sai hankalin ku ya tashi" ba musu suka nufi hanyar waje a tsorace, yana biye dasu, ganin haka ya saka Ummy ta bi bayan su a sanyaye kada ya illa ta mata yara, cikin bacin rai ya dubi Huzaifa dake tsaye a gefe yace "nuna min wacce kake magana aciki". Shiru Huzaifa yayi yana kallon matan guda uku masu matuƙar kyau da kama da junan su, biyu ne tsawon su yazo ɗaya kuma suke matuƙar kama da juna kamar twins, Meelah da Deejah, ya dubi mahaifiyar su babu shakka a gurin ta suka sami wannan kyawun duk da jikin ta ya nuna tana cikin mawuyacin hali, Safeenah ta fashe da kuka tana faɗin "wallahi Baba Sai da na gaya mashi kada yace yana sona dukan mu zaka yi, kuma kayansa ma naki na karɓa...... Yace" au kece Kenan? Kai samari itace wannan? Yayi tambayar yana kallon Huzaifa, ganin tsoro sosai a idanun feenah da ƴan'uwanta ya saka shi nemo nutsuwar sa, yace "Baba babu wacce nake so acikin su, wannan ma sau ɗaya na taba ganin ta.... Ya katse sa cikin bacin rai " to me kake nema a guri na idan babu wacce kake so acikin su? Huzaifa yace "ni malamin makaranta ne kamar yanda na gayama sanda na zo, ɗaya daga cikin su ce naga bata da takalmi a ƙafa, a matsayina na malamin su na siya na bata taƙi ƙarba tace iyayen ta sun hana ta karɓan komai a gurin namiji, naji ta burgeni kuma hakan ya nuna ta fito gidan tarbiya da mutunci naji ina so nazo na haɗu da iyayen da suka tsaya akan tarbiyarta na kuma basu takalmin da kaina sai su ba ta " Audi ya washe baki jin ɗan boko mai gayu sai yabon su ya ke, ganin haka ya saka hankalin Huzaifa ya kwanta ganin dabara sa tayi aiki akan sa, yace" yauwa yaro an gode, bani takalmin ya faɗa yana fisgo ledar hannun Huzaifa, ya fito da takalmin yana juyawa kafin ya bashi yana faɗin "baza mu karbi wannan takalmin ba". Cikin mamaki Huzaifa yace "Meyasa Baba? Yace" saboda ƙa'ida ne duk wanda zai siyawa yarana ko menene nima sai anyi min tawa Leda, shine ribar haihuwar ai, dan haka kaje da takalmin duk sanda ka siyamin nawa sai ka kawo mana tare" Huzaifa yace "in dan wannan ne babu matsala nayi maka alƙawarin siya maka takalmi gobe zan kawo maka amma
Table of Contents