Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 6

Chapter 6

Farar Taska Book 1 Complete Hausa Novel 1,182 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

su, Deejah ma ta biyu tayi a ajin su kowa sai faɗa yake munyi ƙoƙari, kinga harda kuɗi wani malamin mu ya bamu a makaranta" taji wani farinciki a ranta, sai murmushi take tana duba jarabawar su duk da bata gane komai, amma farincikin da take gani a tare dasu yake saka ta wani nishaɗi a zuciya, tace " Allah ya nuna min watarana kun zo min haka kuna farincikin sanar dani kun zama wasu da Al'umma zata amfana daku tayi alfahari daku" Deejah tace " Innar mu ni kinsan dame zan amfani al'umma? Ummy ta girgiza kanta tana kallon ta da murmushi, tace " ni ina so na zama Malamar makaranta na riƙa koyar da yara irin yanda Anty Nabila take koyar damu, na riƙa saka kaya irin nata masu kyau ina yin kwalliyar kamar nata ko kuma na zama lecturer a babbar makaranta, Innar mu ance sai anyi karatu mai zurfi sosai ake kai wannan matakin" Ummy tace " babu laifi a wannan Hadeeza wasu su sami ilimi a ƙarƙashin ka domin kuma a ƙarƙashin wasu kuke nema a yanzu, Allah ya cika maki wannan burin naki har ki kai ga matakin riƙe makaranta gabaki ɗaya bama Malama kaɗai ba ". Safeenah tace " Innar mu ni kuma ina so na zama ƴar Jarida, bansan dalili ba amma abin yana burgeni idan naga ƙawaye na suna bayar da labari akan ƴan jaridu" Ummy tace " baki da ra'ayi sai na wasu kenan, nikam menene acikin aikin Jarida Safeenah? Tace " shikenan tunda bakya so, zan zama ƴar kasuwa zanyi karatu akan Business, na riƙa fita ƙasashe ina kasuwanci, malamin mu ya bamu labari masu kasuwanci har jirgi suke shiga suje wata ƙasa saboda kasuwanci, Innar mu idan na sami kuɗin zan gina maki ƙaton gida ki bar wannan, kuma bazaki ƙara yiwa kowa aikatau ba" Ummy tayi murmushi idanunta cike da ƙwallah ta shafa kan Safeenah tana faɗin " Allah ya tabbatar da hakan kasuwanci ma wani abu ne mai kyau shima dogara da kaine, amma shima karatun sa ake yi ne? Safeenah ta gyaɗa kai tana faɗin " Sosai kuwa Inna" Ummy tace " Allah ya cika maku wannan burin naku, ta dubi Meelah tana faɗin, saura ke baki ce komai ba". Ta yatsina fuska kaɗan kamar bazatayi magana ba kafin tace " ni Inna ina so na kasance tare da ke har ƙarshen rayuwata, idan na girma bazan ƙara bari Baba ya dake ki ba". Hawayen da take maƙalewa suka zubo, ta saka hannu da sauri tana goge su kafin tace " Jameelah suma ƴan uwanki zasu kasance dani har mutuwa ko da kunyi aure muna tare babu abinda zai raba mu, bana so ki kasance dani kawai batare da kin taimaki al'umma daga cikin ilimin da kike nema ba" ta tunzuro baki kaɗan tace " to zan zama ƴar sanda saboda kawai idan Baba ya dake ki na kama shi" Ummy tace " Mahaifi mahaifi ne komai lalacewar sa, ki daina tunani akwai ranar da zaki iya rama min duka a gurin wanda ya haife ki, ki ɗora hannun ki akan mahaifin ki kar na qara jin wannan banzan tunanin ki ko a mafarki, yanda kuke sona kuke son ganin farincikina haka nake so ku nunawa mahaifin ku, bana gayamaku duk abinda yake yi ba laifin sa bane kuma zai zo ya daina, ku daina ƙullatarsa ko tsanarsa ko da naman jikin ku yake yanka, kuma ko da ace mugun halin sa yafi na kowa a duniyar nan shi ɗin Mahaifin ku ne bazaku iya goge shi a rayuwar ku ba". Meelah ta ɗauke kanta tana tunzuro baki, Ummy tace " ki gayamin naji dame zaki taimaki al'umma? Tace " ki zaba min kome kike so nayi". Ummy tace " ina burin naga ɗaya daga cikin ku ta zamo unguzoma a ƙauyen nan ko dan mata irin mu da suke haihuwa a gida da waɗanda ake kai asibiti babu ma'aikaciya mace sai maza ne suke karban haihuwa suke duba kowacce mace da matsalarta, tunda su sun faɗi nasu ra'ayin ke kuma kin bani zabi wannan nake so kiyi Meelah" Meelah ta jinjina kanta tace " shikenan zan yi Innar mu" tayi murmushi tana kaallon su cikin farinciki, tace " Allah yayi wa rayuwar ku albarka ya raya min ku cikin aminci ya kuma baku mazaje nagari da zasu riƙe min ku hannu bibbiyu bisa amana da ku..ma....bakinta ya ɗauki rawa saboda wani baƙinciki daya zo ya tokare zuciyarta, tasa gefen zani tana goge wasu ƙwallah, Meelah tace " ni bazan yi aure ba innar mu kidaina saka ni a irin wannan addu'a, zan zauna na kula dake" Deejah ma tace " nima bazan yi aure ba ina tare dake innar mu" Feenah ma tace " nima bana son auren, bana so a dinga dukana kamar yanda Baba yake dukan ki" bata da ƙarfin magana a wannan lokacin saboda zuciyarta ba daɗi, sai tayi shiru tana sauraren su tana kallon su cikin shauƙi irin na uwa ga ƴaƴanta. [8/2, 8:40 PM] J💕: https://chat.whatsapp.com/ER26gPFC7iT6v26Jyz8hCt?mode=ac_t *FARAR TASKA* Fertymerh Zarah 💕 5 Tafe suke suna hira sama sama, zuciyarsa a jagule yau kamar ko yaushe, ganin yanda yaran shamwilu suka yi aikin gona sosai yau shi ko rabin rabi bai samu yayi ba kuma acikin su babu wani wanda yake taimaka masa, kallon shamwilu yayi yace " Shamwilu kai abokina ne na amana kasani, mun taso da kai tun muna yara kuma muka girma a tare har muka zo muna makwabtaka da juna saboda abotar mu, na ɗauka yaran ka yara na ne ko ban fito nayi magana da fatar baki ba zaka iya basu umarni da su taimaka min a tawa gonar, banda haka ma acikin su huɗu ko ɗaya ne ai zaka iya bani muyi aikin tare". Shamwilu ya kece da wata dariya kafin ya dubi Audi yace " ka manta yaran yanzu ka haifesu baka haifi halin su bane, ni kaina ba sai nayi da ƙyar ba kafin na samu su zo min gonar balle har kayi tunanin su taya ka taka gonar, ni bazan hana ba idan zasu taimake ka, gobe ka gwada yi masu magana kaji" Audi yayi jim kaɗan kafin yace " idan na haifi yaro dole yabi umarni na domin ni nake ciyar dashi na tufatar dashi kuma yake zaune a qarqashin inuwa ta, tabbas Shamwilu da nine nake da ƴaƴa maza kake da mata ko basa so dole sai sun taya ka aikin gona albarkacin ƙawancen mu" Shamwilu ya bata fuska kaɗan yace " Audi me kake nufi yanzu kana son gayamin nayi ma ba dai dai ba saboda basu taya ka aikin gona ba, nace ka barsu gobe idan mun fito zan masu mgn su taya ka, menene na fushi kuma" Audi yace "Allah ya kaimu goben" suka cigaba da tafiya har suka iso gida, ƙofar gida suka zauna suna mayar da numfashi cikin gajiya, basu jima da zama ba sai ga su Safeenah sun dawo daga ɗebo ruwa, suka gaida su kafin su shiga cikin gida, Shamwilu ya tabe baki yana jinjina kansa kafin yace " wallahi abokina waɗannan yaran guda uku da ace akwai wani bature a garin nan tabbas zaa ce ƴaƴan sa ne ba naka bane,

Table of Contents

Chapters

18 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});