Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 7

Chapter 7

Farar Taska Book 1 Complete Hausa Novel 1,175 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

kai ni har yanzu bani da tabbas akan Ummy ba fita take wani guri tana haɗuwa da wani daban ba". Audi yayi jim kaɗan kafin yace " Ummy Salihar macece zan yi shaidar hakan akan ta, kuma duk inda zata je baya wuce aikatau da take zuwa sai nan gidan Wadata maƙocin mu, amma nima kaina idan na dubi yaran wani lokaci har ƙoƙonto nake idan jinina ne su kaf zuri'ata kasani bamu da farare kyawawa irin yaran nan, wani lokacin kyawun nasu ruɗani yake naji na tsane su nayi ta dukan su batare da laifin komai ba, ko kuma nayi ta dukan uwar tasu kamar yanda ka bani shawarar laifi kaɗan tayi min nayi mata duka kada ta raina ni, kuma fa duk kyawun nan nasu ai Uwar ta fisu kyau ko ka manta, kawai wahala ne da yanayi na cikin nan da take ɗauke dashi ya gusar da komai nata" cikin takaici Shamwilu ya ja tsaki yafi kowa sanin Ummy tana da kyau domin ya jima da son ta a zuciyarsa bashi da buri na ganin Audi ya rabu da ita shi kuma ya samu ya aure ta ko zata haifa masa kyawawan ƴaƴa masu kama da ita, ya muskuta kamar gaske yana kallon Audi, yace " Matar nan idan ta sake haifo maka wata macen wlhy kayi gaggawar rabuwa da ita domin babu ƙashin arziki a tare da ita kuma ita ɗin ba alheri bace a rayuwar ka, kowane gida yana buƙatar magaji yanzu da ace ta haifa maka ƴaƴa zaka dinga wahala a gona ne? Audi ya girgiza kansa, Shamwilu ya cigaba da faɗin " mutanen gari sai su fara maka kallon wani golobo kamar ba cikakken namiji ba, ka kasa haihuwar ɗa namiji raini ya zo ya shiga tsakanin ka da zawarawan garin nan su ɗauka baka da ƙarfin haifo ɗa namiji matarka ta fika ƙarfi". Audi yaji wani bacin rai sai gumi yake haɗawa saboda damuwa, Shamwilu ya cigaba da faɗin " sai kaje neman aure a hanaka akan wannan idan baka sani ba, saboda kowa kallon raggo yake ma kamar bazaka iya aikata komai a shimfiɗa ba sai matar ka, kai ni fa ko kaɗan bana sassauta wa yasira saboda kada ta raina ni, wlhy duka nake mata sosai ko gyaran murya nayi a ƙofar gida zaka ganta durqushe tana gaida ni cikin tsoro, balle kai mai mace irin ummy kace ba zaka kara aure ba" Audi ya dube sa cike da damuwa yace " gayamin menene abin yi yanzu ina cike da damuwa, ina buƙatar magaji, ba dan komai ba sai dan Allah ya saka min son haihuwar namiji a yanzu, mu'amalar ka da yaran ka tana burgeni musamman a gona" Shamwilu yayi wani shu''umin murmushi yana jan gemun sa, yace "abokina kasani nayi maka ƙoƙari wajen ara maka gonar nan tawa da kake juyawa, kasani baka da komai a duniyar nan banda wannan gidan da kuke zaune komai ka siyar kasha giya, sanda ka rasa iyayen naka babu shawarar da ban baka ba akan kada ka banzantar da kuɗin ka siye gona sai ka ƙi zance na gabaki ɗaya ka tare gidan giya inaji sau uku rak ka taba siya min giyar, sai da kuɗin suka ƙare ka neme ni, to magana ta gsky na kusa na karbi gonar bada jimawa ba domin siyar da ita zanyi na haɗa kuɗin da wanda ke hannuna na ba yaran zasu je can kudu neman sana'a". Audi ya dube sa jikinsa ya ɗauki karkarwa yace " Shamwilu idan ka karbe gonar ya kake so nayi da tawa rayuwar, a ina zan nemi abinci? Shamwilu ya ja gajeren tsaki cikin takaici yace " da kake neman abinci a gonar ina ce saidawa kake kana shan barasa da kuɗin, iyalinka kake ciyarwa da abincin ne da zaka damu? Ƴaƴana duka maza ne kasani kuma dole zan basu jari su je su nemi sana'a". Audi yayi shiru cikin tunanin mafita sosai yake ƙaruwa da gonar duk da ba wani abin kirki yake nomawa ba, Shamwilu yace " ko menene abin damuwa kai da kake da manyan jari a gaban ka" Audi ya dube shi da mamaki batare da yayi magana ba, Shamwilu yace " eh mana, kana da ƴaƴa mata irin wannan me kake jira, ai kawai ka bayar da su aure ka huta kowacce acikin su zaka sami alheri" cikin rashin fahimta yace " Shamwi bangane ba, waye zai yarda ya aure su kuma wane alheri zan samu a tattare da waɗannan fararen mata? Shamwilu yace " ai kawai muje can mashayar giyar tamu ka sami wani ka haɗa shi da wannan babbar, dama ƴaƴa mata ai jari ne saboda jarin ake haifarsu, ka bayar da ita akan kuɗi dubu ɗari uku zuwa sama, idan ka sami kuɗin ka siye wata gona ƙarama ka riƙe sauran canjin kasha barasa, nima ka bani wani abu na saka a aljihuna". Audi yayi shiru cikin tunani kafin yace " Allah ya shaida ya sani ina son ka shamwilu sosai saboda duk na shiga matsala kana da hanyar fitar dani, hakan zanyi tun da dama basu da wani amfani a gurina ga mahaifiyarsu sai wahala take wurin ciyar dasu, idan lokacin siyar da gonar taka yayi zan mata aure da duk wanda na samu zai bani kuɗin". Shamwilu ya tashi ya nufi cikin gidanshi ya bar shi gurin a zaune, da shigar shi ya ajiye kayan shi inda ya saba ajiyewa ya nufi ɗakin Yasira, " ranki shi daɗe na same ki lafiya". hararar sa tayi kafin taja tsaki tana faɗin " tun ɗazu ina ka tsaya har yaran nan suka dawo baka dawo ba? Yace " ai ina tare da Audi a waje tun ɗazu kiyi haƙuri masoyiya ta" tayi mashi banza, ya washe baki yana faɗin " ina abincin nawa? Cikin takaici tace " baka shigo da wuri ba na bawa yaran sun cinye". yayi shiru cikin bacin rai yaje gona yayi aiki ya dawo gidansa ace baa ajiye masa abinci ba bayan shine mai nemo wa, ta juyo tana kallon sa tace " kayi min tsaye akai ko akwai wani abu" ya haɗiye wasu yawu da ƙyar tare da girgiza kansa, ya juya har zai bar ɗakin sai ya dube ta yace " baki yi ajiyar ko ɗan wani abu ba na saka a bakina ko ruwan kunu ne, yunwa nake ji sosai Yasira" cikin bacin rai tace " to ko ni zaka ɗauka ka cinye ne? ya girgiza kansa yana faɗin " tuba nake ranki shi daɗe kiyi haƙuri" ya juya zai fice tace " ji mana" ya juyo da sauri yana kallon ta, tace " ni kaina ban samu naci abincin ba na bawa yaran sun dawo gona duk sun gaji ga yunwa sai nace su cinye duka, kaje kasuwa ka siyomin gasashen nama mai ruwa ruwa shi kaɗai nake son ci a yanzu kazo ga ruwan kunu na ajiye maka kasha", yace " kiyi haƙuri babu kuɗi hannuna a yanzu, amma nayi maki alƙawari anjima idan na fita zan zo maki dashi" tace " yanzu nake so kaje ko bashi ne ka nema ka siyomin yanzu kafin raina ya baci kasani kuma bazan maka da kyau ba, kuma kasani na saka yarannan sun samo

Table of Contents

Chapters

18 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});