Chapter 3
Chapter 3
haka ba zai hukunta shi, bayan sun dawo gida sai da yayi mata duka sosai kafin ya barta kuma ya tabbatar mata idan ta ƙara zuwa kai ƙarar sa wurin mai gari a bakin auren ta kuma zata bar mashi gida, ta zauna tayi kuka sosai har da nadamar zuwan ta duniya, tayi istigfari, ta sani bata da kowa a yanzu kuma babu inda zata je da yaran har guda uku, bata san dangin iyayen ta ba ta tashi ita kaɗai a gurin iyayen ta kuma ta same su suna gadin wani gidan attajiri a maiduguri, yanda mahaifinta ya haɗu da iyayen Audi ne bata sani ba har aka ƙulla auren, yau gata ɗauke da ciki na huɗu, mace ko namiji bata da masaniya akan me zata haifa ta dai san ko menene tana son abinta kuma ko da mace ɗin ce bazata taba bari ya cutar da ita ba zata cigaba da rainon ƴaƴanta tana addu'a watarana ya gane ya gyara halinsa. A yanzu safeenah tana da shekara 12, sai Meelah 10 sai hadiza 8, kullum adduarta Allah ya basu miji nagari kamar Alhajin maiduguri (gidan da iyayen ta suka yi gadi) su kula mata da ƴaƴanta mata ko kuma miji irin mahaifinta tasan irin kulawar da yake yiwa mahafiyarta bata taba ganin ya ɗagawa mahafiyarta murya ba balle har ya kai ga dukanta (wannan shine taƙaitaccen labarin su). Washe garin ranar duka yaran uku sun gama shirin tafiya boko, dama maƙocin su Malam Wadata ya saka su saboda baya son ganin yaran kullum gida a zaune, sai yayi magana da mai ɗakin sa Saratu yana son haɗawa da yaransa ya saka su boko da islamiya kuma ta yarda saboda suna matuƙar bata tausayi, Malam Audi kallon su yayi sanda suke shirin fita ya daka masu tsawa, " kai jajjayen buzaye ku dawo nan dan uwar ku" jiki na rawa su uku suka dawo, Ummi dake ɗaki a kwance tana ji ta fito da sauri kada ya illata mata yara, yace " gidan uwar wa zaku je da wannan kayan na jikin ku (uniform) Meelah tace " Makarantar boko zamu je Baba" yace " waye ya saka ku karatun, wane shegen ne marar hankali zai dubi ƴaƴa mata har guda uku masu kama da aljannun boye ya saka su boko, me bokon zai amfane ku dashi, dama ku maza ne sai inda ƙarfina ya ƙare akan karatun ku amma babu wani shege da ya isa ya taimake ku ina kallo wlhy, maza maza kuje ku cire kayan jikin ku kafin farar fatar nan taku ta mayu kamar uwar ku na maidata jawur yanxu" duk suka tsorata, Ummi ta ƙarasa gurinsa tare da tsugunnawa har ƙasa alamar roƙo tace " dan Allah mai gida ka barsu su nemi ilimin, duk wani hukunci na yarda ka sauke akaina amma ka barsu" yace " babu amfanin da ilimi zai masu waɗannan yaran naki mutane gudun su suke a gari idan baki sani ba, ni ba dan kar Allah ya hukuntani da laifi ba da nace ba nine na haifi waɗannan yaran ba, yara kamar su suka yi kansu dan kyau kuma kinga iyayena basu taba haihuwar ƴaƴa mata ba, mu uku suka haifa duka maza sauran sun mutu nine kaɗai nayi saura, ta ina nake da gadon haihuwar ƴaƴa mata, kinsan wanda yake maki cikin su". ta rumtse idanu zuciyarta na mata wani zafi yau fiye da duk tozarcin da yake mata, ta buɗe idanun a hankali tana kallon yaranta fuskarsu ta nuna damuwa sosai, murmushin yaƙe tayi irin na uwar da take son ganin ta cire yaranta daga cikin damuwa, tace " Safeenah ki riƙe hannun ƙannen ki kuje kada ku makara a dake ku kinji" yace " kada shegen da ya fita a gidannan, wallahi duk suka fita sai jikin ki ya gayamiki" cikin murmushin yaƙen take kallon su, tace " ai kuna son farinciki na ko? Suka gyaɗa kai da sauri, to idan baku je ba bazan ji daɗi ba, zuwan ku shi zai sakani farinciki, kuyi sauri kada ku makara" Meelah tace " innar mu yace zai dake ki fa" da ƙyar tace " idan kun je bazan ji zafin dukan ba saboda farincikin kun je neman ilimi" Safeenah ta riƙa hannunsu suka fice suna waiwayen ta, ransa yayi matuƙar baci ya riƙa ƙafafunta ya soma janta har cikin daƙi, bai yi la'akari da cikin jikinta ba yayi ta dukanta har sai da ya gaji dan kansa, ya je yasha ruwa ya dawo, wandon jikinsa ya zuge yana kallonta a galabaice, yace "buɗe min ƙafafun ki, wawiya kawai" ya faɗa a fusacce, ta ɗago idanunta jawur da ƙyar tana kallonsa, taƙi ta buɗe ƙafafun yasa hannu da ƙarfi ya buɗe da kansa ya aika mata, ta rumtse idanunta cikin baƙin ciki dama mutuwa tazo ta ɗauke ta a wannan yanayi, tana ji har ya qare abinda yake ya tashi bai ƙara waiwayenta ba ya fice, tayi kuka tayi kuka har Saratu ta shigo ta ganta a wannan yanayin, ko bata tambaya ba tasan dukan ta yayi kamar ko yaushe, tace " haɗa min ruwan wanka" Saratu cikin tausayi taje ta haɗa mata, taje tayi wankanta dawo ta zauna, Saratu tace " wai innar'su bazaki kai ƙarar Audi ga mai gari bane a ɗaukar mashi mataki saboda gudun watarana kada ya illataki ko ya kashe ki, ki bar yaran da bazai kula dasu ba tunda ba son su yake ba? Tace " Saratu Allah baya barci ya san halin da nake ciki kuma shine zai min magani, a kullum ina addu'a da sakawa ƴaƴana albarka tare da miji nagari, idan naje na kaishi ƙara yace a bakin aure na kuma zan bar masa gidan sa, waye nake dashi a duk duniya yanzu banda shi da yarana, bansan dangina ko ɗaya ba, idan ya sake ni ina zan je, ko wane bawa da irin jarabawar sa, xan cigaba da haƙuri da juriya saboda ƴaƴana". Saratu tayi shiru cikin ƙunar zuciya, sama sama suke taba hira saboda jikin nata ba daɗi duk yayi tsami akan duka, ganin barcin wahala ya kwashe ta suna tsaka da magana sai saratu ta girgiza kanta cike da tausayi tana kallonta, mace har mace kyakkyawar gaske sam bata dace da Malam Audi ba a tsarin halitta ballantana a wurin hankali da nutsuwa, Ummi da matan manya ta dace duba da kyawun da take dashi duk wahalar da take sha a gurinsa bai dishe kyau da hasken fatar ta ba, gashi duka ƴaƴan ta inda Allah ya taimake ta babu wanda ya ɗauko shi ko a farce duk ita suke biyowa, lallai nan gaba idan suka girma ta tabbata maza zasu so su kuma ta hanyar su kaɗai Ummi zata sami jin daɗi musamman idan su ka nemi ilimin nan, ta tashi cikin tausaya mata ta fice batare da tayi dogon motsin da zai tayar da ita ba. Ta jima tana barcin wahala da gajiya har bata san lokaci ya tafi sosai ba, buɗe idanuwanta tayi dai dai da shigowar su da gudu gidan suna kiran innar mu, suna ganin ta duk suka je suka rungumeta cikin farinciki kafin su soma duba jikin ta, Hadeeza tace " Innar mu sai da Baba ya dake ki ko, ni
Table of Contents